← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 86

Sashe 52

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Daidai isowar Tahir da Umar hankali a tashe.

Har ta juya ta ce mishi.

" Usman Jama'are!

Na rantse da Ubangiji Adamu da Muhammad, sai na tsayawa Lubnah, sai na bata kariya sai na hanata kuka akanka da shi wancan Tsinannen yaron, Usman Jama'are idan ka isa da Tsinannen Yaron nan kace ya fita harkan zuriarta ba Lubnah ba wani cikin Yarana wancan shegen.

Ya kara mu'amala da su sai na yi Shari'a da kai da su.

" Har ta cigaba da tafiya ta juya cike da takaici ta ce mishi.

" Wallahi billahi azim na kara ganinka tare da Yarana sai na ga uban da ya tsaya maka a Bauchi, ku ai ba mutane ba ne dabbobi ne a cikin shigar mutane.

" Huci tayi kafin ta juya a hankali Umar da Tahir suna take mata baya ta juya tana kallon Baban Bauchi dariya tayi ta ce mishi.." kamar yadda ka yarda min Y'a a cikin makaranta ka saka kowa ke mata kallon tausayi da hauka yau kai ma ka ji yadda take ji!

Feel it I said it how lubnah she survived, ka ji kunyar da taji a duk lokacin da ta fita hayacinta,.

" Ya kara takawa har habansa " how you feel it?

Da kunya ko?

Haka take kallon kowa yana jin tausayinta, kun mai da min yarinya wata iri ta koma kamar ba bil adam ba.

" Aunty Innah da suka iso kasuwar da Hindatu ta rufe mata baki, fisge bakinta tayi.

"Na rantse ba zan gushe ba sai na saka kowa yasan waye kai, kai ko ban ce maka Allah ya sakawa Lubabatu ba Allah sai ya saka mata, amma ba kome In sha Allah sai kayi danasani sai ka ji tsoron duniya da mutanen cikinta, sai ka ji kunyar kallon Lubabatuna, In sha Allah sai ta zame maka inuwar gajimare, shi kuma wanda ka daukaka kanta in sha Allah sai ya nuna maka iyakarka." Daga haka Yaranta suka ja ta, amma yadda zuciyarta yake tafasa ba zata iya tafiya ba sai ta gumawa Abba takaici ta juya ta ce mishi.

" Ka ji kunya duniya da lahira, ta duniya mai gushewa ce ta lahira ita ce wacce zaka kasa kallon har Ubangijinka." Yasan halinta amma bai ta
a kawowa idan wani abu ya faru zata iya mishi tijara har haka ba, bai taba kowowa ko a mafarki haka zai faru ba, amma yau ta kunyata shi a gaban jama'a ta saka kowa yana shi da abinda ya aikata.

Shi akan daidai yake kuma bai ga dalilin da zai saka ya sauka akan ra'ayinsa ba.

Dayawan dattawan da suke wurin hakuri suka yi ta bashi haka ya bar shagon babu wani abin annashuwa, ranshi idan yayi dubu ya b'aci.

Karshe shima Hafiz sulalewa yayi ya gudu, domin yadda kowa yasan me ya faru, dama an ji aurensu ya mutu amma babu wanda yasan dalilin mutuwar sai yau kuma abin mamaki sai gashi an yi yadda yayi ta azabtar da yar uban rikonsa, a take wasu suka ce su ba zasu iya ba, abokansa da suke zuga shi da daura shi akan mugun hanya basu ce kome ba, amma an samu wasu kananan magana ya fara fita ai kuwa da gaske ne abinda ya faru.

Dayawa sun tabbatar da haka, sai gashi mutanen da suke kallon Hafiz da wani mutunci sun daina, wasu ma har daina mishi magana suke domin gani suke ya koma shaidanin da ya raba zaman lafiya ga uban rikonshi, da yayi mishi gata wasu ai gani suke zai aikata domin kawai a ganshi a wurin amma abinda yake aikatawa ya wuce tunanin me hankali.
...........

Mama kuwa a motar Ya Umar aka kaita gida bata yi kuka ba, sai da suka isa gidan Yaran suka zagaye ta, ta fara kuka tana fa
in.

"Ku kira Adamu ku ji halin da take ciki hankalina yana kanta!" Lokacin da suka kira Ya Ado suka gaya mishi abinda ya faru, kiri-kiri ya ado ya goyi bayan Maman sannan ya gaya musu tana gida ya koma wurin aiki amma kamar barci take.

Haka Tahir ya kashe wayar ya gwada kiran Lubnah da wayar Mama, a hankali ta dauka.

"Ya Tahir ina Mama?

Ina lafiyarta lau?" "Gata nan tana ta damuwa ne ne halin da kike ciki?" Daga can ta sakar mishi murmushin karfin halin ta ce mishi.

"Alhamdulillahi, ina Maman take?" Ta tambaye shi, mikawa Mama yayi mikewa Mama tayi tana fa
in..

"Jinjira kina lafiya dai ko?" Murmushi tayi tana fa
in da sauki kaina ne kawai ke ciwo amma da sauki kin ga gobe xan tafi na amso abincin da zan fara ci na rage kiba, sannan zan fara motsa jiki." Sai abin ya sakata jin yadda ta shanye kome ta shiga bata labarin abinda ya faru, murmushi tayi ta ce mata.

"Mamana kada ki kara fada da Abba a kaina, ki kyale shi fushi yake da ni zai sauko wata rana, nima kewarshi nake shi yasa amma ba zan kara kiranshi ba, ki yi hakuri kin ji na ki bin umarni ki don Allah ki yafe min!" " Waye ya gaya miki kin yi min laifi, Allah ya miki albarka, ke da yan uwanki don ki nutsu ki yi karatu har Allah ya baki lafiya." Karshe sai ga Mama da ta gama kukan takaici ta koma hira da Autarta ta manta da wasu yaran a wurin, baki
aya tattara kauna da tausayin ta daura akan Lubnah, sai da suka yiwa wayar fyade ta hanyar cinye katin tass, sannan ta ajiye wayar sannan ta tuna da wasu bayin Allah, nan suka yi ta bata hakuri da kada ta kara biyewa Abbansu shi yanzu kunyar zaman kasuwa ma ya ishe, haka suka bar zancen aka shiga maganar bikin Sani,
Ranar dai Baban Bauchi a asibitin kainuwa da yake nan dutsen tanshi ya kwana saboda yadda jininsa ya haura, bayan ya dawo ya tara Yaransa baki
aya ya gaya musu ya sallamawa Adamu Lubnah sannan ya cire Adamu da Lubabatu a cikin Yaranshi ya barwa Salamatu su, kamar yadda suka kashewa Lubabatu aurenta in sha Allah haka duniya zata musu alawadai da abin kunyar da Lubabatu zata kawo musu.

Duk parlourn suka yi shiru Sani da yasan idan yayi shiru yayi munafunci ya ce mishi.

"Abba ba ayiwa Ubangiji kutse zanen
addara da yasa alkalamin ya rubuta, ko kai aka hada da Hafiz sai ka yi kara amma lokaci ne kawai zai bayyana haka, Allah ya kyauta." Shi ya fara fita daga parlourn domin idan ya cigaba da zama maganar da zai fita bakin shi ba kyau kuma mahaifa ne ba ayi musu magana ta rashin
a'a.

Bayan fitar sani yace duk wanda ya kara kula Mama da su Lubnah bai yafe ba, Yadiko da take waje tace mishi.

"Wannan dai ita ce ake kira karya domin ba zaka raba su da uwarsu da yan uwansa, kai kar ku sake ku dauki wannan maganar, hakkinku ku kula da Uwarku da Yar kanwarku, kune gatanta." Yadda Yadiko ta nuna musu nasu kada su dauki maganar shi ya kara kwantar musu da hankali, yayi ta fada karshe a daren sai da ya koma asibiti, take Hafiz ya kira Jama'are ya gaya musu cewa ai ga abin da ya faru, sai ga yan Jama'are mota guda, a nan kowa ya nuna Mama bata kyauta ba, jinin halin da Abba yake ciki da kuma ganin yadda yake kwance bai da lafiya, Hafiz ne kanshi ko asibitin yasa aka yi ta zagin Yaranshi da nuna Hafiz ya zama gatanshi tunda gashi ya haife su amma Uwarsu tafi shi moransu, tunda gashi kowa ya juya mishi har Yaran Yadiko, suna tsaka da maganar Yadiko ta iso wayyo ai Mama ita nata karamar yaki ne, Yadiko da ta ji abinda suke fada da ta fara bala'i da cira kamar zata tashi sama.............
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 34
Shi yasa Allah ya tsinewa mai tadda fitina, domin kuwa rigima sosai aka yi kamar za a daku, wai duk akan Hafiz da Lubnah.

Ai kuwa lamarin har Jama'are, abinda ya dawo kunnen Mama aka yi ta cewa suna son kashe Baban Bauchi ne saboda dukiyarsa, domin su ci gado musamman Mama da yake ita ce Uwar Yara dayawa, wato ita fitina idan tana barci mafi alkhairi a barta ta cigaba da barcinta kada a tashe ta, amma wannan karon sun tashi lukutar masifa, domin Mama har Jama'are ta cimma Goggo Uwani da Talatuwa da suka haddasa rikicin, ta ce sai sun shiga kotu domin wanke mata suna, da suka ce tana son kashe musu dan uwa.

Nan fa hankalin kowa ya tashi rigima ake yi tun karfe bakwai na safe har karfe biyar na yamma sallah yake tashin su dakyar da su
in goshi Mama ta hakura bayan manya daya daga Fada sun shiga lamarin, ta kuma ce a shata mata layi a tsakaninsu, idan wani magana ya fito ba zata yarda ba sai gaban kuliya manta sabo.

Jin wannan abinda take shirin yi yasa kowa ya shiga hankalinsa aka fita harkanta da Yaranta.

A cikin kwanaki biyu ko waje bana lekawa, zai yau da Aunty Nuratu ta zo da kanta.

Sai na ji kunya ya kama ni, a hankali na sauko muka shiga mata hidima.

Sai da ta
an sha ruwa sannan take kallona.

"Ina ta jiranki ina lafiya?" Murmushi nayi duk da rashin sabo a tsakaninmu, amma yadda take damuwa da lamarina yasa zuciyata sakewa da ita nace mata.

"Ciwon kai da habbo ya hanani fita!" "Kina yawan tunani ko?" Kallon Aunty Zakiyah da ta kawo mata snacks nayi domin ta amsa mata da cewa.

"Ai kullum muna magana akan tunanin nan." Kallona tayi can ta ce min.

"Duk abinda zai faru ba zai tab'a kai na baya ba, you need to move on.

Kin tab'a tsammanin zaki samu freedom haka?" Murmushi tayi tana kallon yadda na rike hannuna da juna.

"Ba laifinki ba ne,
addara ce ta zo miki a haka.
Chapter 52 · 0% Book details