← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 86

Sashe 64

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gamawa ya turawa Uncle Auta cewa ya gama s tura mishi wanda suka diba, ba dadewa kuwa ya turo mishi mutane talatin a bangarenshi, haka yayiwa Ubaid magana ko minti goma ba ayi ba ya turo mishi mutane sha tara, da ta dauka baki
aya mutane dari da yan kai, daga nan ya tura musu yadda zasu raba mutane ranar interviews din.

Sannan da kuma yadda zasu duba su.

Sannan ya ce musu a tura musu sakon yau yadda zasu shirya akan lokaci.

Haka ya tura musu yadda ya tsara, kowane su zai dauki ya 27 har da Jasminah.

A ranar suka gama tsara kome.

Yadda yake basu hit yasa Uncle Auta ya kira shi yana cewa.

"Kai don ubanka yaushe ka shigo?" "Ni kuma?" Ya rena mishi hankali, sanin cewa bai gaya musu zai shigo ba, sai kuma ya saka a ransa cewa.

"Kawai ina zargin kamar ka shigo ne." Murmushi yayi ya ce mishi.

"Na zata ka shigo ne!" Murmushi yayi ya ce mishi.

"Ka cika zargi!" Daga haka ya shashatar da zancen, suka cigaba da abinda ya tara su.

Domin daga karshe conference call suka yi.

Kusan wunin ranar aikin da suka yi kenan, tunda aka kawo mishi abinci mai gadinsa ya amsa ya kawo mishi, ya ci ya bar sauran.

Can ya kara odar na dare.

Kusan sallah yake d'aga shi a wurin bayan ya gama ya wuce ya tafi unguwa.

Bai dauki mota ba, sai dai taxi d ya dauka haya, ya tafi kamfanin lokacin an tashi ya shiga dakyar suka bari ya shiga shima sai da ya bada cin hanci, bai nuna musu waye shi ba ya shiga yana kallon yadda ma'aikatan yake, daga nan ya wuce tsohon side, daga can ya hango office din MD Khamis ya bude asalima kamar akwai wani a cikinsa, haka yasa shi isa har kofar office din abinda ake zargi ya gani da idanunsa, daya daga cikin ma'aikatan ce take kuka, da rokon ya barta da mutuncinta sannan ya duba tana da ciki dakyar suka samu cikin kada wani abu ya same cikin rayuwarsu zata shiga garari, amma Khamis ya shafawa idanunsa toka ya daka mata tsawa, tura office din yayi yana fa
in.

"Taso ki tafi!" Ta cire hular kanshi na face cap din da ya saka ya ri
e.

Kunya ne ya kama shi, "thank you sir!" Murmushi yayi ya ce mata.

"Ki dauki maternity leave mana idan cikin yayi kwari sai ki dawo, yana da kyau hakan!" Cikin wani irin girmama ta ce mishi.

"Zan dauka sir!" Bata san waye shi ba, amma a yadda ya bata umarni, kuma Oga Khamis bai magana ba, haka ya tabbatar mata da shi wani ne, juyawa yayi ya rakata har bakin gate din, sannan ya nufi new side dinsu, ya gama kallon wurin da kyau, kafin ya wuce ya fita.

Koda ya isa gidan da abinci ya isa, ya haura parlourn sama ya baje.

Next day ya kar shiryawa ya tafi ma'aikatan, ya samu suka bar shi ya shiga yasan Khamis ba zai tab'a bada labarin ya dawo ba ko don a tambaye shi yaushe?

A ina ya ganshi?

Haka ya gama zaga kamfanin har ya hadu da masu sata a kamfanin, haka ya dawo gidan ya rubuta, kome zuwa uku yayiwa kamfanin.

Khamis kuwa tattarawa yayi ya gudu Abuja, don yasan idan har suka sake ido hudu da shaidani Turaki tow sai dai ya bar kamfanin.

Shi yasa ya gudu kafin su sake haduwa.

Yau kwanaki hudu kenan da aka ce mu je interviews, Ya Ado ya kira Mama ya gaya mata har da su Aunty Hindatu, aka yi ta murna a Bauchi Mama kan har da sadaka tayi, domin gani take kamar na amshi kaddarata ne, amma har yau na kasa nutsuwa zuciyata tana wani irin tsalle a duk lokacin da na tuna da Ya Hafiz yana nan sai na ji baki
aya kome ya rikice min, Ya Ado ya ha
a ni da Dr Dijah Bala, ta min yan tambayoyi na bata amsa, ta ce mishi yayi hakuri abin yana barin mutum ne a hankali, amma da zaran wani abu da ya shafi past dina ya dawo tow zai cigaba da hunt
ina, Haka Aunty Nuratu Kafaya ta gaya masa, kusan sati aka saka a zuwa interview din, haka yasa Ya Ado ne ya kai ni kasuwa muka sayi kayan da zanyi amfani da shi, kuma yana da yakinin Allah zai bani sa'a, ranar ashirin da watan June aka saka zamu.

Yau sha bakwai ina kwance da yamma a parlour kasance Asabar ne, Rufa'i ya shigo da sallama, tashi nayi na zauna ina kallonshi yayi dariya yana fa
in..

"Manya Lubnah ki amince na kawo dubu goma a daura mana aure, ni bani da matsala xan amince ki ta juya ni kamar masa." Murmushi nayi na ce mishi.

"Kai dan Yaro da kai ne zan amince na aure amma ka mugun rena min hankali." "Samun kyakkyawar saurayi irina sai an cika form, Gara na miki talla kafin mata su kwace miki ni." Haushi ya kama ni na kalle shi na yi kwafa, Aunty Zakiyah ta fito tana mana dariya sai zoyalat suke karshe na biye musu aka wuce wurin, haka ya zauna har Ya ado ya dawo ya amshi abinda ya zo amsa ya koma, ranar Lahadi kuwa jin wani irin tsoro ya kama ni nake, ban taba zuwa irin wuri haka ba, nayi su goge karamin fashion hijab din da zan daura akan kayan, sai takalmana da na kara goge shi, sannan na koma na zauna ina ta azkar, domin zuciyata ta gama razana, lokacin da na ga kamfanin da Ya ado ya nuna min, da kuma aikinsu, sannan ya gaya min wani abu.." kada ki rena kanki, idan kika yi haka ma'aikata zasu yi bullied dinki, please ki tsaya akanki kada ki bada fuskar da za a wulakanta mana ke, ki yarda da kanki."
Daga haka na ji a raina zan yi kome don na wanke Ya ado, ruwan sama aka fara kamar da bakin
warya, bayan na ci abinci na kwanta sannan na kara nazarin takardun da zan tafi da su, kafin na hada kome a wani jaka.

Washi gari tun asuba Ya Ado ya buga min kofar dakin ya bani wayarshi.

Addu'a mama take min kamar ta aro kafa ta biyo wayar, tayi min Addu'ar nasara da sa'a tare da dace, haka na amsa da Amin, bayan mun gama wayar na shiga wanka na hada da Alwala, sannan na yi sallah na shirya tsaf, karfe bakwai saura muka bar gidan tare da Ya Ado da Aunty Zakiyah, ita ta sauka a can asibiti ni kuma Ya Ado ya kawo ni inda ma'aikatan take.

Ikorodu Local Government.

Anan kamfanin yake, kafin mu wuce ya ce min..

"idan kika fito daga kamfanin idan kin samu abin hawa zasu kawo ki can inda mutane suka tsaya sunan wurin Garaj kenan, daga nan zaki samu mota zuwa gida kin ji ko?" Gyada mishi kai nayi ya dunkule hannunshi yace Goodluck!

Murmushi nayi ya kawo ni har kofar kamfanin ya ajiye ni, ya fito zuwa bayan motar ya mika min lema da rigar ruwa nace mishi.

" Ya Ado wannan ma ya isa." Ciro dubu goma yayi ya ce min.

" Ki rike wannan!

" Murmushi nayi na ce mishi.

" Allah ya kara budi.

" Har ya juya zai tafi ya dawo ya
an janyo ni jikinshi.." ki kula kada ki bari a rena min ke kin ji ko?

" Gyada kai nayi, yayi murmushi sannan ya wuce ya shiga motarshi sai da ya tafi na shiga kamfanin, ana ta taruwa, ina shiga na ga matasa ire-irena, ina zuwa wurin na musu sallama babu wanda ya amsa min, kame kaina nayi na koma gefe, domin daga dukkan alamu duk masu zuwa interview ne, har wurin karfe takwas motocin alfarma suka fara shigowa kamfani, gabana ne ya fadi sosai, haka wasu fararen mutane suka fito, ni dai ban tab'a ganin irinsu ba, haka suke fitowa tare da tafiya cikin kamfanin kamar zasu tashi sama, kowa ka gani sanye yake da coat irin na aikin nan black kusan shigar mu ce da su, wurin karfe goma saura wata mota ta shigo kamfanin wanda yayi daidai da fara kiran sunayen mutane, Yara ne guda biyu suka fito, daya tana cin abu a cikin kwali, tana ta zaga wurin.

Kiran wasu mutanen aka yi a lokacin na lura bamu wuce ashirin da wani abu ba, haka muka cigaba da zama, har karfe sha biyu ba rana sai ga wata mota ta shigo, a lokacin Yaran nan sun zo kusa da ni suna wasa, masu kula da Yaran suna ta tare tare da su, ban san ya aka yi ba sai ganin daya daga cikin yara biyun ta tsaya........
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 44
Cak idanunta kawai yake motsawa, a daidai lokacin da aka kira sunana kenan, yadda yarinyar ta tsaya zaka zata ko wasa take tana kallon mutane amma ni nasan ba haka ba ne, saboda ya tab'a faruwa da Yasir ya saka abu a bakinsa sai da na rungume shi ta baya na matse mishi cikinsa abin ya fado da amai.

Da gudu nayi watsi da takarduna, na nufi yarinyar da kowa ya kama gabanshi tana niman faduwa, na rungume ta ta baya na shiga matse cikinta tare da buga bayan da kaina sau biyu nayi mata na ukun sai ga amai da kwallon abin ya fado, zubewa muka yi dukkan mu, domin ta suma ne, da sauri na kara gyara mata kwanciya a jikina masu kula da su, suka shiga ihu, "ban ruwa!" Ka fada musu, mika min suka yi na kunsa a bakina na watsa mata sau uku sai gashi ta fara ajiyar zuciya.

Nima ajiyar zuciyar nake saukewa, na tashi duk kayana yayi kura, ashe labarin abinda ya faru har an isar ciki, tallafo yarinyar nayi na zauna da ita a kujeran da na tashi.
Chapter 64 · 0% Book details