← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 86

Sashe 83

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tow ba makawa sai yadda karfinsa ya
are, shi wannan da gaske yake sonki ba cutar dake zai yi ba.

"
" Yan uwansa basu sona!" Na fada ina kuka," akan me zasu su so ki?"
"Mama ya fi karfina, Mama danginsa wasu irin dangine, na masifa Mama ba zan iya bude mishi zuciyata ba, Mama ban tab'a sonshi ba tun farko a yau ma ina kara fada kamar farko bana sonshi." Murmushi Mama tayi ta ce min.

"Nasan ai zuciyarki a rufe take shi yasa kika ki yarda ko kalli kowani mutum da sunan soyayya, amma ba zan boye miki ba, kina son Bilal Koda baki fada ba." Kuka na saka mata ina ta rantsuwa wallahi bana sonshi.

Weekend a gida nayi shi, ranar lahadi sai gashi da Yaran kanwarsa a lokacin na tambaye su basu Islamiyya ne,.

Suka ce eh basu zuwa.

Turawa Uwarsu sako nayi na kama hannunsu na kai su makarantar su Adil na musu registration na Islamiyya, aka basu uniform suka zauna, ko da na dawo na samu yana bada hakuri ne, murmushi kawai Mama take ta ce mishi.

"Ai ni ba ruwana kai da abokiyar aikinka, ni ba ruwana ku yi duk yadda zaku yi amma ka sani Lubnah tana bukatar hutu saboda tayi fama da mentally healthy ill, shi yasa bana son damuwa ya dame ta domin ta kai har matakin GENERALIZED ANXIETY DISORDER, idan har zamanku babu alkhairi kowa ya kama gabansa." Kasa magana yayi zuciyarsa tayi sanyi ya ce mata.

"Taya ta hadu da wannan laluran?" Murmushi Mama tayi ta ce mishi.

"Rayuwa ya ha
a ta da wannan laluran idan da ranka ai ka sha kallo." Idanunsa yayi mugun ja, haka yayi ta wasa da kafet din parlourn.

Mama ta fahimci yana son ya tambaye ta, Abubuwa dayawa amma kuma yadda yake da zurfin cikin.

Tana mamaki ma da yake dogon hira da ita domin irinsu basu cika hira har da kowa ba.

A hankali ya ce mata.

"Allah ya kyauta, xan tafi an jima zan zo daukar Yaran ." "Allah ya kai." Abinda na fahimta ya zama
an gida kowa ji da shi yake da yamma bayan isha da yaso ya samu yaran sun ci abinci sai da ya ci tuwon alkama miyar kuka, sannan ya dauki yaran zuwa gida bayan na biyo shi waje na ce mishi.

"Ka yi hakuri da abinda nayi naga rayuwar mata ne, shine na ce bari na biya musu kudin Islamiyya, amma don Allah ku yi hakuri." Murmushi yayi ya ce min.

"Kin kyauta ai!" Daga haka ya shiga motar ya bar gidan.

Mama take gaya min mutane irinsu, suna son mace amma aikace suke nuna mata so, basu damu da su gaya mata ba domin ya zama old fashioned a wurinsu.

Kuma dabi'ar masu irin halinsu ne, suna da zurfin ciki domin kamar basu yarda da kowa ba, sannan basu cika yarda su yi hira da kowa ba sai wanda ya fahimci halinsu, idan baka fahimce su ba zaka yi ta ganin suna wani abu kamar basu ba, ta ce haka suke kuma dai da tayi magana na fahimci yadda yake masifa kamar nayi mishi laifi musamman idan aka yi baki maza ina musu bayani yayi ta wani fushi da fisga karshe korani yake waje ya ce musu zan bada abinda suke so ba,ya kira Taj, idan da taj muke hira yayi ta fushi ranar daga ni har Taj kamar zai rataye mu, don masifa.

Ni kuma tausayi yake bani domin idan haka ita ce soyayya gaskiya am not ready, zuciyata a rufe take.

Washi gari kuwa da safe suka zo da Taj, Ashe Ya Ado yasan da zuwansa.

Don fushi nayi naki zuwa aikin haka kawai zasu daura min hawan jini, a gidan suka karya tunda na fahimci yazo fir naki fitowa ba ayi, kuma ai kakanshi ya ce kada na gaya mishi haka ya share zamanshi har yayiwa Mama kyautar ku
i, wanda ya damu da ku
insa shi ya ji wurin.

Ni bayan gabana balle ya ce don ku
insa nake, ni magana da Ubaid ya gaya min ma ya ishe ni.

KUMO FAMILY
Fada Alhaji ELYakub Kumo yake kamar ya mari Uncle Auta, ya ce mishi."kasan tana tare da Yaron nan ne saboda kai, amma ka gaya mishi wacece Yarinyar bayan ba kaunarshi yake da gaske ba, ina sane da cewa Turaki yana bin ra'ayinka ne yake kula Yaron nan, kada ka kara bawa wani labarin rayuwar Turaki.

Da shi da aka hada baki aka kore shi a shekarar karshen shi a secondry School, kasan sharrin da ya so a kulla mishi?

Kasan yadda ya lalata mishi rayuwa?

Ban da Allah yana tare da shi da rayuwarsa tafi haka lalacewar don Allah kada ka kara gaya mishi kome akan Bilal wanda ya mishi a baya ma, ya isa yanzu meye ribar shiga rayuwarsa?" Yadda yake shiga ba nan yake fita ba, fada kamar zai mari Uncle Auta.

Yayi fada sosai domin kuwa yana jin zafin abinda Ubaid yayiwa Turaki a lokacin.

Abu guda biyu da suka lalata alakar Turaki da Ubaid na wani abu ne, duk da kowani mutane yana da hali me kyau ko mara kyau, idan har Turaki yayi kuskure tow ya dace ya samu mutumin da zai tsaya a tare shi, tow har ana niman haka tow Ubaid ya kai wannan matsayin, sai dai tun suna Yara Ubaid baya kaunar Turaki yayi sabon aboki ko kuma ya taimakawa wani, yayi ta fushi da kuncin rai kenan.

Duk yadda za'a gaya maka matukar ba faruwa yayi da kai ba, ba zaka gane ba.

Ubaid ya bawa Bilal wahala akan wannan lamarin domin Ubaid yana ganin Turaki da sabon aboki yayi ta fushi kenan har sai ya raba shi da abokin, sai da Ubaid ya kai ko me turaki zai yi to bai iya ba shi
aya ya iya........(Sometimes silent pain yana kashe mutane dayawa, lokaci yayi da zaka fadi ra'ayinka lokaci yayi da zaka rusa wancan bond din da kake gani kamar sasari ne let move together)
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 59
Abinda ya fara faruwa shine kama yara da aka yi suna lalacewa a cikin Makarantar, wnada a lokacin iyayensu suka raye maza sun zo akan case
in, wanda yayi sanadiyar da Turaki ya bar makarantar domin Ubaid ya bada shaidar yana lalacewa irin ta mazan da aka tsinewa, kasancewar akwai kyakkyawar alaka tsakanin kakaninshi na Rasha da kasar Saudiya musamman ta harkan kasuwanci suka kashe zancen ya koma Rasha wurin kakarshi sai da ya dauki wata goma ya koma Saudiya yayi jarabawar barin makaranta.

Daga nan ya koma can yayi jami'arsa a lokacin Ubaid azo suka yi karatun tare, duk da wannan abinda yayi mishi yayi hakuri sai ya kasance duk wani abin asha kiri-kiri Ubaid yake danganta shi da Turaki, amma bai ta
a kawowa a ransa yana haka ne don ya cutar da shi ba,
A hankali yayi ta amfani da wannan damar yana raba Turaki da duk wanda ya zo gare shi, ana haka iyayensu suka rasu mazan sai da Hajiya Amina mahaifiyar Ubaid zata koma gida Alhaji ELYakub ya amshi rikon Ubaid yace idan ya tafi Turaki zai shiga kadaici, a wannan lokacin kowa ya amshi haka amma kuma a ransu basu son Ubaid din da Turaki domin kowa so yake ya rabu Turaki ya cutar da shi, amma an rasa yadda za ayi, ba a san me ya faru ba.

Amma lokacin amma wani satar da aka yi a cikin gidan ElYakub kumo wanda ya girgiza ilahirin family ana cikin binciken baa tambaye shi ba, kawai ya ce ai Turaki ne yayi satan wani abin takaici aka nime kudin ba a samu a wurin Turaki, a lokacin fushin da Turaki yayi dakyar aka shawo kanshi yake kula shi, babban rigimarsu shine akan Mimih wanda aka ce zai aikata, a lokacin ya ce zai aikata ya ci-gaba daga maza ya koma kan mata, tun daga wannan lokacin Turaki ya watsar da shi, amma yana kyautatawa Iyalinsa da duk wani dangin mahaifinsa da na Mahaifiyarshi.

Amma ya yanke duk wani abu da yake tsakaninsu, ko rike office din Turaki da yayi ai Alhaji ELYakub ya bashi domin kusan shima bai da mutunci akan gaskiya zai iya aikata kome.

Yadda alakarsu ya lalace musamman yadda yake zargin Turaki yafi kome bashi haushi.

"Ke bana son rashin hankali, ya zaa yi ace mutum ya zo baki sauko kun gaisa ba." Tura baki nayi nace mata.

"Wurinki dai ya zo!" "Amma kanki daya kuwa!" Mirgina mata kaina nayi nace mata.

"Kin ga shi
aya ne babu kari!" Make ni tayi, haka ta fita, na tura baki ina ruwana da shi.

Ba dai ga shi bayan isha ba, muna parlour muna kallon super story, da yake Alhamis ne, zare idanun nayi kaina yana cinyar Mama tana zaune a kasa nima na kwantar da kaina akan cinyarta.

Lumshe idanuna nayi kamar me barci, ai kuwa cikin ikon Allah barci yayi gaba da ni, nan suka shiga hira har tara tayi, na musu sallama ya tafi yana fita daga parlourn Mama ta zuba min mari a kafada.

"Tashi ja'ira yau kin kunyata ni!" Sosa wurin nake ina tura baki.

"Allah ya shirya ki!" Tashi nayi na wuce sama, washi gari ba naki zuwa aiki ba, sai ga Taj da aika tulin aiki kamar nayi hauka Mama kuma taki bani goyan baya, haka nayi ta aiki kamar jaka kwana biyu nayi ina aiki.

Dole ranar Monday na koma aiki domin aikin kamar zai hallaka ni.

Tun da na dawo sai na ga yayi sanyi ba masifar nan, nima kuma wannan karon sai na kama kaina.

Baki
aya satin Mama biyu ta bar Lagos, bamu gaya mishi ba.
Chapter 83 · 0% Book details