Sashe 42
Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata rana mun fito sallah wurin alola ya kira ni, yadda na dauka na kasa magana dama kuma ba maganar nake ba, haka na ajiye wayar a wurin sanadin da aka sace wayar, koda na tafi masallaci nayi sallah na dawo na duba ban ga wayar ba, a hankali na koma aji, koda na koma gida da kaina, Ya Ado ya kira Aunty Zakiyah ta gaya mishi gani nan wayata ce ta fadi ne, da zai dawo sai ya zo min da sabon.
Akan washi gari zai kai ni a yi min welcome back, kai tsaye na ce mishi.
"A'a bana so, ka barshi kawai idan aka tashi zan dawo da kaina." Na fa
a mishi.
"Tow idan ana son magana da ke fa?" Shiru nayi ban kara magana ba, haka ya kyale ni tunda raina baya son wayar, kuma Alhamdulillahi kin wayar ya kawo min kwanciyar hankali.
Don nasan Hafiz yana can yana niman wayata.
Bai samu ba,
Yau asabar babu aiki, Hakazalika kowa yana hutun karshen mako.
Hajiya Daddah tana dakinta tana tattara Alqur'ani dinta mai falle falle.
Badr ta shigo dakin.
Zama tayi tana kallon Daddah da tunda ta shigo bata d'ago kai ta kalle ta ba, shiru Badr tayi tana mamakin kakarsu a saninsu Yaran mace ake so da kauna, musamman yadda Mamanta take kula da Daddah, duk ana yin haka ne don a samu kyakkyawar alaka mai karfi, amma Daddah ko kallo basu ishe ta ba, a hankali ta ce mata.
"Ina kwana Daddah!" Yadda kasan da dutse take magana Daddah bata d'ago kai ta mata magana, haka kuma bata amsa mata ba.
Hannu ta kai tsabar reni irin nata zata tab'a jakar Alqur'anin Daddah ta daka mata tsawa.
"Kul na ka taba min kayana, bana son reni da rashin kunya irin naka ni ba abokin wasanka ba ne." A hankali ta janye hannunta.
"Amma Daddah tun dazun nazo." "Assalamualaikum." Mimih ta rangad'a sallama da muryanta mai sanyi, "Amin waalaikumunsalam." "Daddah ina kwana?" "Lafiya lau, takwara ka tashi lafiya?" "Lafiya lau Daddah, cika Badr tayi tana kallon yadda Daddah take amsawa Mimi.
" Daddah jiya na turawa Hamma Turaki sakonki." Bata wani damu ba, don tasan waye Turaki tunda kusan saboda ita ya ki zuwa kasar ya yi fushi sosai. ,yadda bata amsa mata ba ta cigaba da cewa.
"Ya bude yace yana kewarki!
" Anan ne ta ce mata, "Takwara shi karya bai da kyau, ka daina karya Turaki bata amsa wayar kowa daga Ubaid da Auta bayan nan sai kiran Alhaji.
" Tayi haka ne don yadda Badr take ta cika tana batsewa, gyaran murya Alhaji ELYakub yayi yana rike da sandar shi ya ce mata.
" Fadime ga turaki akan waya!" Ba tare da ta ji nauyi ba, ta mike da sauri ta isa zuwa gare shi, ta amshi wayar tana fa
in.
" Alhamdulillahi Turaki kina lafiya?
" Daga can ya ce mata.
" Hmm!
" " Turaki yaushe zaki dawo gida, ko dai na mutu zaki dawo?" Kome ya gaya mata ta sake murmushi tana fa
in.
" Tow Allah ya baki hakuri, tunda bakya son dawowa ki cigaba da zamanki har Allah ya baki damar dawowa."
Kusan ita ce take mishi hiran domin bata yi shiru ba sai magana take tana bashi labari, yadda zaka fahimci how she miss him, wani irin kewarshi take daga karshe da aka gama wayar sai da ta fashe da kuka, fita tayi ta kai mishi wayar Badr ta watsawa Mimih harara ta ce mata.
"Munafuka waye ya gaya miki bamu san cewa baya kiran kowa kuma ba ya daukar kiran kowa na gidan nan sai mutane uku, ki bar wawantar da kanki.
Mun san kome da kike wannan iyayin kin manta idan da kunya ai babu aure a tsakaninku?" Murmushi tayi Mimih tayi na wani lokaci kafin ta ce mata.
"Eh kin san ni kawai ana iya kallona ne, amma wani abu ai a bude ya
e muna raye cikin haske amma a inuwarmu akwai duhu me
matukar hatsari." Daga haka ta wuce ta barta ita
aya a dakin Daddah, ranta yayi masifar b'aci, haka ta gama cika ta batse.
Itama barin dakin Daddah tayi tana jin wani daci daci a ranta, a haka suna son juna amma a zahirin gaskiya tsanar juna suke akan Turaki.
Tana fita dama da motarta ta zo, shiga tayi ta fisge ta da gudu.
Tana ji kamar zata tashi sama, haka ta wuce gidansu tana isa ko parking Mai kyau bata yi ba, ta bar motar a bude ta shiga cikin gidan da gudu, Hajiya Khaulatu da Alhaji Abbas suna lissafi ta shigo a guje.
"QueenB ya dai?" Da gudu ta haura sama, tana kuka.
Hankalin uwar ya tashi ta bita sama, ta samu tana ta razga kuka.
"Me aka miki?" "Daddah ce ta ki kula ni, amma Mimih tana zuwa ta kulata." "Ba na hana ki zuwa gidan Daddah ba?" "But Mom taya xan yi ina son Hamma Turaki." "Bana ce ki bar kome a hannuna ba." Nan ta zauna tayi ta mata fada da cewa ta nisanta kanta da Daddah ita zata mata fight samun Turaki, amma ita bata isa ba.
Haka ta gama Uban yana bakin kofar yana kallonsu cikin murmushi ya ce musu..
"indai turaki ne zan yi wani abu guda daya da zai saka kowa ya amince." "Ko?" "Eh kai, ranar Litinin zamu yi azumi kamar yadda Baffa yake yi.
Ba zan manta Harisu ya ce idan yana raye zamu hada auratayya a tsakanin Yaranmu.
Kuma akan idanun Baffa aka yi Allah ya jikan Harisu.
" Ya fada yana kallon yarshi, domin yanzu ya fahimci duk abinda zai faru, Yayanshi suna sama da kome, shi yasa yake ta kokuwar bawa Khamis MD na kamfanin domin a karba a hannun Jasminah tunda ba wani abu take tsinanawa a kamfanin.
Haka suka gama kitsa mata kome.
-------
Baki
aya wancan satin nayi shi a zirga-zirga, amma yau da muke weekend.
Ya Ado ya hana ni barci.
Wai sai mu shirya mu tafi beach.
A kasale na fito na isa parlourn ina sanye da riga da skirt English wear, duk da na ragu sosai amma yanayin fuskata idan ka kalla zaka
auka fulawa ce ta ji yis.
Haka muka fito baki
aya muka shiga motar, ina baya da su Adil.
Sai hira suke min ina amsawa, koda muka isa bakin ruwan yaran wasa suke Adil ya hau doki, mai sunan Mama tana wasa da ruwa idan ya zo da gudu ta dawo wurinmu idan ya tafi ta bishi da gudu, sai dariya muke mata, Allah sarki Princes tsoro ya hanata zuwa inda muke sai tsoro take tana cewa ruwa zai dauke ta, wani irin nishadi da nutsuwa ya shige ni.
Wayar Aunty Zakiyah Mama ta kira na
auka, da yake wayar tana kusa da ni.
"Mama bata kusa ne!" Da yake ta saka Mamanmu, mamanta kuwa ta saka Maman Dass.
"Ina wayarki nake kira kullum baya shiga?" "Hmm ya fadi ne, kuma nace bana son wani." "Me yasa tow?" "Ya zan yi Mama Ya Hafiz ya samu numbeta sai d'aga min hankali yake Mama kamar zan mutu idan ban dauki wayarsa ba, idan na dauka kuma na ji gara na mutu na huta, shi yasa da wayar ya fa
i naji na samu sukuni." "Wato Yaron nan don kutumar ubansa bai kyale ki ba?
Waye ya bashi number ki?
" " Ina zan sani Mama!" Haka muka gama wayar sannan na mikawa Aunty Zakiyah da take jin mu sai kwafa take, tana amsa suka daura tsinewa Ya Hafiz, sai naji wani irin yadda suka tsane shi.
Wurin karfe biyar muka bar Beach zuwa gida, daga nan muka baje domin abinci ma oda Ya ado yayi mana.
Daren ranar bayan yara sun yi barci Ya Ado ya tsare ni da fada kamar zai dake, bayan ya gama ya kira Baban Jama'are, ya ce ya shiga tsakanina da Ya Hafiz ya daina shiga harkokina, sai dai maganar da Baban Jama'are ya fada ya saka Ya Ado harzuka, wai ai shi aure rai ne da shi idan akwai yiwuwar kara zama sai Allah ya nufa.
Wannan abin ya daki ya Ado, tun daga lokacin na ji na shiga tashin hankali mara misaltuwa domin ji nake kamar zan mutu, kusan sai da na samu tsaiko s karatuna, ai kuwa Ya Ado ya zo Bauchi na tsawon kwanaki uku, zan iya cewa koda ya dawo bai ce mana kome ba, amma na ga kwanciyar hankali a tare da shi.
Ya Hafiz bai san waye yake rigima da shi ba, bai kuma fahimci yadda ake rigima ba, sai dai wannan karon daga shi har yan gidansu sai da suka yi danasanin shiga harkata a gaban jama'a Hajiyarsu take cewa.
"Idan har kai dan sunnah ne ba shege ba, na maka iyaka da Lubabatu idan kuwa na ji ko a mafarki ka sake shiga Rayuwarta sai na maka baki ka lalace." Shima Abba ya ce ya zare ni cikin Yaranshi kada na tab'a kiran shi a matsayin Mahaifi, idan kuwa na sake na zo kan gawarshi sai Allah ya tsayar da shi yayi mana hisabi.
Babu wnada ya gaya min sai Aunty Innah.
Mama kuwa ta yi tsalle ta ce ai dama sai da ya mutu a haka amma har Abada an rabu kenan.
A bangaren Ya Hafiz, abinda yake damunsa gani yake duk abinda yake da samun da yake yayi baya, duk da yadda yake gina Karimah da kanshi amma fa baya ganin haske, duk yadda yaso yayi gaba abun ya ci tura.
Haka Hajiya Asiya ta dauke shi zuwa wurin Malaminta, ya zana ya goge, ya kuma buga kasa sannan ya ce mishi.
"Yarinyar nan itace daukakarka, ita ce arzikinka, ita ce kome naka.
Amma ba zata tab'a dawowa gare ka ba matukar Yayunta da Mahaifiyarsu suna tare da ita.