← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 86

Sashe 22

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda Abba ya gaya min Ya hafiz ba zai tab'a cutar da ni ba, kuma na yarda da wannan magana, haka Kakanmu Baba Malam wanda shi yayi ruwa yayi tsaki akan lamarin ya gaya min haka, ashe kiransu yake yayi ta gaya musu yadda yake kaunata, shi baya fatan na mutu na barshi gara shi ya fara mutuwa.

Haka nayi ta karatu ina kuma shan magani ban tab'a fadawa kowa ba.

Nayi imani da Allah nice sanadin matsalata.

Duk abinda Ya Hafiz zai aikata ban tab'a ganin laifi ko kuskure ba.

Shekararmu daya na fara tsintar wasu abubuwan a jikin wandonsa ko rigarshi wato condom, ban tab'a magana ba, na zama makauniya akanshi bana fadar aibunsa, bai sauya min ba sai da na fara wani irin kiba, wai ashe maganin da nake sha ne.

Idan da xan gaya muku yadda Ya Hafiz yake min a lokacin kwanciyar aurenmu ni har mamaki nake, domin kamar wata yar iska haka zai ta min, ni kuma bana son ya ji ba dad'i sai na hakura na barshi yayi yadda yake so, kibar da na fara sai ya sa na kasa tabuka abin arziki.

Lokacin ina aji hudu na jami'a, an tura ni IT, wani bank na samu horo.

Ranar ya kasance Juma'a haka yasa na dawo da wuri kuma mun yi zan tsaya gidan Ya Umar Aunty Azizat ta haihu.

Na manta kayan barkan a kan gadona.

Na koma gidan dauka, yadda na shiga na ga motarshi jikina yayi bala'in sanyi, domin kuwa ya ce min zai yi tafiya ne zuwa Kano.

A kofar shiga cikin gidan na ga takalmin mace, haka na shiga cikin gidan domin ina ga ko Kannensa ne da yake suna zuwa.

Koda na shiga ban kawo kome a raina ba, haka na shige can dakina ina d'aga labulen mace na samu akan Ya Hafiz suna masha'a, bugawar da zuciyata yayi yasa na juya parlourn da sauri na zauna, jin karar takuna yasa suka fito, lokacin da suka fito suka same ni ina kallon, murmushi nayi mishi nace mishi.

"Dama baka tafi ba ne?" A dan razane, ya ce min.

"Eh!" Yana kallon yadda nake kallon tv, haka yarinyar ta fito tana kallonshi.

Shi kuma ni yake kallo.

Tana fita na koma dakin na dauki abinda xan dauka na fito.

" Ina zaki?

" "Ka manta dai sunan Aunty Azizat ne?

" "Muje na ajiye ki!

" Ya kai hannu zai tab'a ni nayi maza na matsa, ina murmushi na ce mishi.

" Huta kawai!

"
Haka na bar gidan, a can na wuni anan ake gaya min umarar bana ma za a tafi damu, sannan Abba ya cire zakkar da yake cirewa duk shekara an bawa Ya Ado kudin ya ha
a da na wanda yake hannunsa an saya min gida Tambari housing estate, ina jin haka na ce musu kawai zamu koma can, ganin haka kuwa suka mara min baya domin yadda kowa yake sonshi saboda ina sonshi ne, laifin da yayi min sai na barshi a matsayin ajizanci.

Muka cigaba da rayuwar har muka taso daga unguwar da muke muka koma sabo bayan sallah.. shekararmu biyar cib wanda yayi da yin bautar kasana, Ya Hafiz ya fara kulafunci Yara, a lokacin hankalina ya tashi nayi ta zaryan asibiti amma babu labari.

Bani mantawa wata rana ina kwance wurin karfe tara na dare ya shigo da wata mata, don zata girme ni.

Ya ce bata daki ta kwana.

Haka nayi kuwa na bata daki da na ware shi don bakinmu, kwana
aya sai ya zama kwana biyu kai a takaice dai sai gashi ta share kwanaki a gidan.

A cikin wannan yanayin na kama shi da ita, a lokacin na saka a raina gara ya aure ta, yaki har da gaya min wai karuwa ce, na ce haka zai yi hakuri, a cikin lokaci kalilan na shawo kanshi, ya kai sadakin karima, kowa a dangina yaji maganar aurenshi, hmm mutum sai Allah sai ga magana ya fito ta Jama'are cewa ai dalilin aurensa don ni na kashe mahaifina da shan kwayar hana daukar ciki, a lokacin dangi kowa ya juna min baya nima kuwa na tashi da rikici na ce ba gidana ba, Abba da Baba Malam suka zo har gidan suka ci mutuncina tunda ni bana kaunar Hafiz shi yasa na sha maganin hana daukar ciki ban isa ba a gidan zai zauna da Matarshi.

Haka nayi hakuri na dauke kai, aka yi auren.

Suka yi ta min iskanci da renin hankali.

Wallahi tun bana iya dauka har na fara, abin da ban sani ba akan shi kai kara, abu ka
an ya kai
arata, ayi ta zagina ana ganin laifina.

Kwatsam sai ga Matarshi da ciki aka yi ta murna ana farin ciki.

Nima dai nayi murna, nayi farin ciki.

Sai dai watanin cikin da auren bakwai, da safe muka samu hatsaniya da ita, kuma Ya Hafiz din Yana nan shi ya raba rigimar, bayan ya fita kasuwa kawai jini ya
alle mata, haka aka kwashe ta zuwa asibiti.

Haka muka je ko awa daya na ayi ba ta haifi Yarta mace, aka fito aka gaya mana, muka yi ta murna haka na koma gida na gyara inda jini ya bata na wanke gidan, wurin karfe biyar na yamma aka sallame ta, suka dawo gida washi gari Ya Umar ya zo ya min shegen duka, wanda ya fusata Aunty Hindatu a lokacin tayi ta fada tun daga nan ta tsaya min, wai ashe labarin abinda ya faru Ya Hafiz ya gayawa Baba Malam shi kuma ya kira Abba yake ce mishi ga can Lubabatu zata kashe mata da ciki jini ya
alle mata.. shine Abba ya ce ko a samu wani ya min duka.

Ko kuma ya sake Mama.

Wannan abin ya fusata Ya Umar..

Danginta da kowa yana jin haka, har shi ya Hafiz din, sai da nayi zazza
i, yan uwanta don gulma sai sun zo duba ni.

Haka na daure na yi ta hidima dasu har aka gama suna abu daya na musu fintinkau, iyayenta talakawa ne na fitar hankali hatta abubuwan da aka yi na suna daga gidan Iyayena ne, ranar sunan da yamma na shiga naji suna min dad'i.

Ni ban kula su ba sai Aunty Raliya da ta wanke su tas ta ce musu.

"Ai ku san tarbiyya irinta gidan yasa aka zane ta kada ta kara aikata shirme, gidan da Yarku take abincin da Yarku take ci daga arzikinmu ne, shi kanshi mijin dai bai da nashi na kanshi sai na matarshi don haka mu yar mu tana da tarbiyya domin bamu sake ta tayi ta bin titi kwaro-kwaro ba.

Ga sittin ga degree.

Haihuwa kuwa ba akanta aka fara rashinsa ba, Allah ya karawa Nana A'ishah yarda itama har tayi wafati Allah bai bata haihuwa ba.

Mun san islamiyya domin mun zauna gaban Malamai " daga haka suka yi shiru.

Tun daga nan ta koma bayana, Yan uwan ya Hafiz suka koma jikinta hatta Hajiya komawa tayi jikinta.

Haka aka watse wani renin hankali, sai su bawa yarinyar maganin barci su kawo min ita haka zasu ta iskanci wani lokaci kuma haka zasu kawota ko za mutu tana kuka ba zasu amshe ta ba, haka na ci wahalar yarinyar nan.

Gashi da na gama bautar
asa result dina yana fitowa aka so niman min aiki Amma da yake mugunta na ransa ya hana..

Haka nayi ta rayuwa da kunci da wahala, gashi ya hana ni cigaba Umaran da muke zuwa ya dauke min damuwa, idan ya Hafiz yana son wani abu a guna tow wallahi a lokacin zai ta kashe ni da soyayya har sai na fara jin anya ba rashin fahimta bane, amma ina haka dai muka cigaba.

Akwai shekarar da Abba ya biya musu Umara shi da Karimah kanta yayi ta rawa haka suka tafi watan Mauludi.

Bayan sun dawo takuma daukar ciki, a lokacin Firdausi ta zo ta zauna a gidan, na ga iskanci ganin idanuna.

Na gama secondry School ina sha shekaru goma sha bakwai, na gama jami'a ina da shekaru ashirin da biyu, a duniya.

Haka kafin ta haihu ya ado ya zo ta sauya min kayan gidan ashe ya samu karin mukami ne, a lokacin na ji labarin tun dukana da Ya Umar yayi suka daina magana, dama shi ne mai tsaya mishi akan kayansa da yake shigo da su ya cire hannunsa.

Kai abin fa sai da aka yi zama sosai domin a ganan Abba Ya Ado ya ce mishi..

"wallahi billahi azmin, duk wnada ya kara ta
a Lubabatu sai kotu ta raba ni da shi, saboda me aka sauke Suratu hujara?" Akan wannan rigimar Ya Umar
in ya shirya min birthday da na cika 23, ina zaune aka zo aka dauke ni, sai gidan Ya Umar a can aka yi birthday party din ya bani motar da kowa sai da yayi mamaki ya ce min na kira Ya Ado na gaya mishi, na kira na gaya mishi na tura mishi motar ya gani shine dalilin shirinsu, tun daga lokacin Yayuna suka dauki nauyin tura min kudi, Amma ya Hafiz ya shiga kwacewa, duk shekara idan muka je Umara sai na sayi yan kunne gwal kamar yadda su aunty Hindatu suke yi domin dukkanmu Yaran Abba mata yake biya mana, har su Aunty Munah aunti Raliya.

Karimah ta haihu ana saura kwanaki uku ba dawo haka na saya mata kayan Baby, lokacin da na dawo na samu an gyara min parlourn, ai kuwa na dawo da kwana biyu aka yi suna yan'uwana a parlour, ga girkin da aka yi musamman ni da muke shiri da yan unguwar suka yi ta shigowa saboda ni, bayan suna shima suka tattaro min yaran baki
aya, haka nayi ta hidima da su har tsawon shekaru biyar cif.

Duk wani abinda nake da shi Ya Hafiz ya ga na cigaba ne dai ya raba ni da shi hankalinsa yake kwanciya.

Kiran sallah farko ne ya sani share hawayen da ya zuba min yanzu na fahimci dalilin da yasa min haka.

Na ga tashin hankali a rayuwata na ga abinda zuciya ba zata iya karba ba, amma na amshe shi hannu bibbiyu, danginmu kowa ya juya min baya.
Chapter 22 · 0% Book details