← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 86

Sashe 45

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karba takardun Alhaji Mudansir yayi jikinsa yana rawa, bai ta
a tunanin kari da ragi da yake yi a office
insa zai iya fita a takarda tar haka ba, dole ya dauki mataki akan kowani dan iska ya rasa wannan rashin wayon Khamis gashi nan dai kamar me wayo amma baki
aya daga Turaki har Ubaid suna iya kifar da shi, duk yadda yaso Abbas ya dauke idanunsa akan Khamis din amma a bayan fage sai sun nuna son zuciyarsu.

Cizon lips dinsa Alhaji Mudansir yake har Alhaji ELYakub ya fita daga office din Ubaid, kanshi kamar zai bindiga, ya juya ya kalli Ubaid.

"Ka kula da kanka!" "Ka kula da Mimih domin ba san me gobe zai haifar ba, kasancewar ita
aya ce maka." Hadiye yawun bakinsa yayi yana kallon Ubaid , ko kiftawa bai yi ba, mamaki yadda ya iya mishi barazana da yarsa.

A hankali ya fita daga office din, ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin sauki da nutsuwa a ransa.

Daga nan ya tattara takardun ya kira Number Lauyar da Alhaji ELYakub ya ha
a su, ya gaya mishi inda zai kai mishi, koda ya kai mishi sama sama suka gaida juna sannan kowa ya kama gabansa.

Lubnah
Yau tunda na dawo nake daki, abinci ma yau dakin aka kawo min, ina ci ina kallon handout, ina nazari har kusan karfe tara na dare.

Ban fito ba wayar da Ya Ado ya saya min kwanan tayi haske kiranshi na dauka ina fa
in.

"Ya Ado?" "Auta ina lafiya dai ban ganki ba ne?" "Bari na fito mu gaisa!" Ka tattara kome na sauko kasa, na samu suna ta hira zama nayi ina kallon Aunty Zakiyah.

"SAN yarinyar nan bata tsoron Allah!" Murmushi yayi yana fa
in, "Auta da gaske ne kin shanya Doctor Ahmad?" Idanuna ne suka cika da kwalla, ina kallon kasa ya cigaba da cewa.

"Tunda nace kin fara karatu hankalin Mama yake kanki tace tana son ki yi aure Hafiz sai ya rabu da ke?" Ni dai ban ce kome ba, har ya gama maganarshi, na ce mishi.

"Zan koma na kwanta." Na mike zan tafi ya ce min..

"Ahmad mutumin kirki ne, ki yi nazari yasan matsalarki kuma zai tsaya miki!" Da gudu na haura sama, ina jin kuka yana zuwa min, ni tsoron maza nake ji bana son abinda zai hana ni dasu, haka yasa na ki kula Ahmad.

Kwana nayi ina kuka domin har yau ban manta abinda Ya Hafiz ya min ba.

Washi gari tun kafin ya fito na bar gidan, domin bana son Magana ya kuma hada ni da shi, a makaranta na karya shima naci ne gudun kada na wahalar da kaina.

Wunin ranar har aka tashi bani da walwala, ina hanyar komawa gida Baby ta kirani.

"Yan mata gani a gidanku!" A shake na amsa mata, sannan na ce.

"Ina hanya!" Haka na isa gidan a hankali nake takawa, har gidan, motar Doctor Ahmad na hango a harabar gidan, ba don mun yi ido hudu da shi ba da na juya.

Haka na daure na shiga na gaishe shi sannan na wuce cikin gidan, na samu Aunty Zakiyah tana gida.

Gaishe ta nayi na wuce sama.

Baby ta biyo ni.

"Yan mata wai meye ya faru ne?" "Babu!" Na fada mata, murmushi tayi ta ce min.

"Wancan hot guy din fa?

Da me shi ko na
auka?" Da sauri na juya ina kallonta.

Baby irin mutanen nan masu open mind bata iya boye what she want kome ta gani tana so baya bata wahala ta mallaka.

D'aga gira daya tayi tana fa
in.

"Ko dai naki ne?" "Yayi miki da gaske?" Na tambaye ta domin ina jin kamar zata raba ni da matsalata ce, idan har ta ce yayi mata tow ba makawa zan samu hanyar rabuwa da shi.

"Idan kina son shi zan baku number wayarshi," na fada ina kallon yadda take murmushi, "wallahi yayi min!" "Ok ko bari na fito wanka sai na baki number shi." Na fada ina wucewa toilet, sai da nayi wanka nayi Alwala sannan ka fito na samu tana zaman jirana, abu take zuka na ce mata.

"Yaushe zaki daina shan wannan abin ba?" mai da shi jakar mata tayi tana fa
in.

"Ina kokarin bari in sha Allah." Ina son gaya mata gaskiya amma kuma san yadda zata dauki maganata ba, kada ya ga kamar don zan hadata da Doctor Ahmad ne, sai na ja bakina nayi shiru na kyale ta har nayi sallah, ina idarwa Adil da Mama suka kawo mana abinci, muka fara ci a hankali, ina lura da yadda bata son abinci, na ce mata.

"Ki daina shan drugs, ki fuskanci rayuwa ki ci abinci domin wallahi zai iya haifar miki da wata matsala daga baya ayi ta kuka da juna." Murmushi tayi ta ce min.

" In sha Allah zan bari!

" Daga haka ta cigaba da tsakuran abincin tana wasa da shi, har muka gama Princess ta shigo ta ce min.

"
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 28
"Aunty kizo Mama tana kiranki!

" Nasan batun Doctor Ahmad ne, ji nayi gabana yana faduwa, kamar zan yi kuka haka na mike na shiga ban daki na wanke hannuna, sannan na saka mayafi akan riga da zanin jikina, na sauko kasa na same ta tana duba books din Yaran na makaranta.

" Lulu kin manta da Doctor Ahmad ne a waje?" Shiru nayi ban bata amsa ba, can dai ta kara magana sannan na d'ago kai ina kallonta kafin na ce mata."to!

" So nake na ce mata, ta sallame shi amma na kasa saboda yadda bakina yayi nauyi, hawaye ne ya cika min idanun.

Komawa sama nayi na dauki Hijab na saka sannan na sauko kasa, na samu tana waya da Ya Ado, kusan tare muka sauko da Baby ta mata sallama zata tafi, muka hada hanya a waje na samu Doctor Ahmad zaune.

Jan plastic chair nayi na zauna ina dan matsawa can nesa da shi, Baby ta tsaya a bayana tana gaishe shi, sannan ta min sallama ta fita a gidan.

Har ta bar gidan yana bin ta da idanu.

"Ki fita harkan yarinyar nan, bata dace da ke ba." Ni dai ban ce masa kome ba, yadda ya gama surutunsa haka na tashi muka yi sallama.

Ban san ya suka kare ba, sai dai kwana biyu da zuwan shi ya kira ni a waya yana tambayata me yasa na bawa Baby numbersa, shiru nayi bani da ta cewa.

Ganin naki magana yasa shi katse kiran, washi gari sai gashi ya zo, shiru duk muka yi yana kallon yadda nake wasa da yatsu hannuna na kasa magana tunda na gaishe shi ban kara magana ba.

"Kin san yarinyar nan bata kyauta ba?

Sannan ta gaya min cewa kece kika bata number ta?

Akan me zata na kirana any how?

Har matata sai da ta fahimci akwai wani abu a kasa." Sai a lokacin na d'ago kai ina kallonshi.

Wato shima dai irin Ya Hafiz ne na shiga gidansa ya gana min azaba da Matarshi, to idan ba mai mata ba, waye zai aure Ni?

Ni dai ba samun saurayi xan kara yi ba a karo na biyu, duk tsiya idan ban auri mai mace daya ba zan auri me mata uku na shiga ta hu
u.

Wannan abin ya saka min wani irin tsoron shi Ahmad din kansa.

Duk mutumin da bai da ikon kasan a gidansa har abada ba mijin aure ba ne.

Don haka na tashi na bar shi a wurin haka ya kira Ya Ado ya gaya mishi, lokacin da Ya Ado ya dawo gida ina daki ya shigo dakin, jan stool yayi ya zauna yana kallon yadda nake takure wuri guda.

"Lubnah me yasa ba zaki bawa Ahmad dama ba?" Yadda yayi magana yasa na d'ago ina kallonshi, idanuna cike da kwalla har ya gama magana ban ce mishi kome sai kukan da na fara ganin yadda nake kuka da gasken gaske yasa shi zuba min idanu cike da mamaki, har washi gari ban fito ba don bamu da class, ina daki a kwance gashi garin an tashi da ruwan sama, haka yasa nayi luff a dakina suka tafi aiki sannan na fito na karya na wanke kayan na koma na kwanta.

Karfe uku na fito saboda hayaniyar Yaran na fito na tsaya suka shiga kafin motar islamiyya ya zo ya dauke su na koma na kwanta.

Karfe biyar duk suna gidan ban kara lekowa waje ba, na cigaba da kwanciyata.

Wurin karfe goma na dare sai gasu nan su biyu yaran sun kwanta ina kwance, kunan wutar dakin tasa nayi kamar ina barci, zama a bakin gadon Aunty Zakiyah tayi tana kallon yadda na sake jikina.

"Ko tayi barci ne?" Inji Aunty Zakiyah, "idonta biyu!" Shima ya ja stool ya zauna yana kallon yadda nake kwance.

"Tashi mun zo magana ne akan Ahmad!" Tashi zaune nayi ina kallon gefe guda.

Tunda kuka fara kawon farillah da musta'abin halin Ahmad, kasancewar shi mutumin kirki ban san lokacin da na fara kuka me karfi ba, sai suka zuba min idanu.

"Me aka miki to?" "Kawai ku mai da ni Bauchi na je can ko kashe ni ne gara su yi!

" Shiru Ya Ado yayi yana kallon yadda nake kuka.

" Me yasa tow?

" " Tsoro suke bani tsoro yake bani, duk wanda zai zo gare ni tsoronshi nake, ku gane ni tsoron maza nake, wallahi cutar da ni zai yi don Allah idan kuna son farin cikina ku kyale ni!"
Ganin yadda nake kuka abin dai yayi ta basu mamaki, har suka fara ganin kamar basu so kansu ba, don haka Ya Ado da kanshi ya rarrashe ni, na bar kuka suka hada min abinci na sha tea, sannan suka tafi na kwanta kusan raba dare nayi ina gayawa Allah kukana, tsoro nake ji shima Ahmad din akwai abinda ya gano yasa yake bina, ban san yadda Ya ado ya fahimta da shi ba, amma kuwa na ga ya daina turo min sako ko wani abu sai dai duk ranar juma'a yana turo min da sakon barka da juma'a wato ba zai tab'a give up ba.
Chapter 45 · 0% Book details