← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 86

Sashe 31

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baby sai yanzu ka dawo, Auta barka da zuwa welcome to home!" Murmushi nayi ina kallonta.

"Muje na nuna miki dakinki a sama!" Kallon stair din nayi na kalle su a hankali na ce musu.

"Na gode!" "Never mind!" Muka haura saman, dakin farko aka bude min.

Juyawa nayi na kalle su a hankali na furta da cewa.

"Tsarki ya tabbata ga Allah gwanin da babu irinsa!" Ba don kome ba sai don yadda aka tsara min dakin sai nake gani kamar ban cancanci zama a dakin ba.

"Shigo dakinki ne, bamu gama gyara dakin ba amma ki yi maneji kafin a gama!" Gyada kai nayi ina fa
in.

"Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi." Ban daki ta bude tana fa
in.

" Look at the toilet yayi miki?

" Gyada kai nayi ina kallon ban dakin.

" Shi kenan bari na karasa abinci, sai ki yi wanka da sallah muna jiranki.

" Gyada kai nayi, na zauna bayan fitarta na cire kayan da zan saka na shiga nayi wanka da Alwala na fito, nayi ta kallon inda zan fahimci gabas ne, turo kofar Ya Ado yayi yana fa
in." Jikina ya bani kina niman alkibla!" Karamin murmushi nayi ya nuna min gaban gadon." Shimfida abin sallah nayi na gabatar da sallah asar sannan na zauna a wurin ina addu'a.

Bayan na idar ne na sauya kaya riga da zani na daura, sannan na cigaba da zama a wurin na tsunduma cikin tunani, wanda ni kaina ban san me nake tunawa ba, ni dai na b'ata shiru.

Turo kofar dakin aka yi ta zuba min idanu.

Juyawa tayi ta sauko kasa, ta ce mishi.

"SAN kazo don Allah!" "Wani abu ne?" Ya tambaye ta yana mikewa da sauri, "just come!" Ta fada tana haurawa.

Haka suka nufo dakin ya shiga ya ja stool ya zauna a gabana har lokacin ban san sun shigo ba.

Itama zuwa tayi ta zauna a gefena.

"Lubnah!" Ya kira sunana, ban amsa ba, ya kara kiran sunana a karo na biyu, shima shiru dafa ni yayi, na wani irin zabura tare da fasa ihu.

Rungume ni Aunty Zakiya tayi tana fa
in.

"Sorry Baby girl we're here!" Ta fada tana shafa bayana, kuka na fashe da shi, tayi ta shafa bayana tana fa
in.

"Ya isa haka, muna nan babu me cutar da ke!" "Tsoro nake ji, ina jin tsoro!

Don Allah ku boye ni!" Har lokacin shafa bayana take tana fa
in.

"Wanda zai cutar ke, you in safe place.

Daga ni har SAN ba zaku bari wani ya tab'a ki ba!" Mikewa Ya Ado yayi ya ce mata.

"Doctor ina son ki mana booking ganin neurologist please!" "In sha Allah, SAN!" Haka tayi ta bubuga bayana, har nayi shiru karshe dai barci ne yayi gaba da ni, ta kwantar da ni.

Sai da ta gyara min kwanciya lokacin Yaran gidan sun dawo daga makaranta, har sun fara ihu ta ja su zuwa daki ta zaunar dasu.

"Aunty Lubnah tazo, and please bata son ihu ko hayaniya, yana iya dakata faint ko tayi loser control, please ku zama good children, kunji ban da fada Ummu Salma, Adil kai ne Babba kada ka yarda su saka ka magana.

Prince kada ki yi ihu
ko kukan banza kin ji!

" " Mommy me ya same ta?

" " Bata da lafiya ne idan kuka yi sallah ku saka ta cikin addu'arku ko?!"
Gyada mata kai suka yi, suka fito bayan sun sauya kaya.

Yaransu uku ne Adil sunansa Usman sunan Abba, sai Ummu Salma me sunan Mama.

Sai Princess me sunan Maman Aunty Zakiya wato Hauwa'u.

Aunty Zakiya da Ya Ado sun hadu a BUK ne, kusan shekarar shi biyu da fara karatu ta shiga a lokacin ta samu medicine ne, wani abun da nake son a sani Aunty Zakiya Bajara ce daga Dass, iyayenta yan boko ne, sosai sannan tana da yayu maza da mata, a lokacin da suka hadu har magana tayi nisa Abba yaki auren, Baban Jama'are ne ya tsaya aka yi kome, domin a lokacin shi Abba Aunty Nana Asma'u yaso Ya Ado ya aura, amma yaki aka yi ta rigima, Baban Jama'are ne ya kashe maganar bayan ya gaya mishi ai Nana Asma'u tana da wanda take so da wannan aka kashe rigimar, itama Aunty Zakiya kamar tasan an yi wannan rikicin, ita da danginta da aka fara zancen auren sun tsaya sosai kuma sun yi abinda ya dace duk wasu iyayen zasu yi akan Yarsu.

Sun nuna mata fada da gaya mata gaskiya.

Ta rike su a matsayin nata, tayi kuma hakuri da kome.

Haka kuwa aka yi ta zo gidan a matsayin wacce bamu amshe ta ba, saboda Abba ya nuna bata mishi ba.

Amma wani ikon Allah ba a shekara ba sai gashi da kanmu muke sonta.

Tana da wani irin kyawawan halayen da sai ka ji kana matu
ar kaunarta, a lokacin da aka yi aurensu Ya Ado saro kaya yake yana turowa shagon Abba, a lokacin duk yan makarantasu gani suke kamar ya cika zakewa akan niman kudi, idan aka ce musu dan Bauchi ne.

Sai su ce dama yan Bauchi suna kasuwanci haka, domin da kanshi yake shiga kwari yayi sayayya ya cika manyan motoci a turo Bauchi, dayawa idan aka ce musu dan Bauchi ne sai su ce a'a ba dai yan Bauchi ba, domin basu damu da kasuwanci haka ba.

A lokacin Ya Tahir yana da shagon provision haka dai shiga singa ya mishi sayayya ya turo mishi.

Koda ya gama karatunsa, sai da suka tura shi school of law Lagos, ya shekara daya.

Bayan ya dawo ya tafi service na wata tara, sannan ya dawo BUK a lokacin itama tana gab da gama karatu, a shekarar aka haifi Adil, wanda yadiko da kanta ta zo Kano ta zauna da ita, da har Iyayenta suna damuwa da maganar tazo wanka gida, sai suka ji labarin Yadiko tana nan, abin da yasa Abba ya sauko ya bar Yadiko tazo, don jin Haihuwar da namiji aka yi kuma Ya Ado ya gaya mishi sunansa yayi masa huduba da shi, itama kuma ta tabbatar da haka.

Tare da mishi Alkunya da adil.

Sai take ta tara mishi nauyi da kunyarta, musamman yadda yake share ta, idan ta zo gaishe shi yayi kamar bai ji ba, wannan soyayyar da ya wayi gari da shi akan Jikansa na farko ya matu
ar amfani iyayen, domin a Bauchi ma har walima aka yi na sunan Usman Adil Adam Usman.

Yadiko bata bar Kano ba sai da suka yi kwanaki Hamsin haka Abba ya ce tayi, sannan da zata dawo Ya Ado da ita Aunty Zakiya suka mata shatara na arziki kasancewar tana da jarabawa, yasa bata zo ba sai da Yaron ya cika wata biyu da rabi, sannan suka zo ganin gida.

Tunda suka iso dutsen tanshi, Abba ya dauki Yaron ya lullube a wurinsa sai nono da wanka kawai ke sakawa ya bada yaron ko idan zai tafi central.

Wannan kaunar yasa ita uwar Yaron bata wani saka yaron a ranta ba, haka da ta tafi gida da Yaron Abba kullum sai saka Mama ta kira ta, a saka mishi muryan Yaron, dan wata biyu iyayenta da dangin sun fi kowa farin ciki, da tayi kwanaki zata koma suka hada mata kaya har da na su Mama da Abba aka hada mishi zuma da zabi aka kawo musu anan fa ta kara daraja da kima.

Adil na shekara daya a duniya ta fara service inda aka tura ta Niger minna, ai kuwa ta kai Adil wurinsu Mama ta tafi service dinta inda zata yi sati uku ta dawo Kano ta karasa domin mijinta yana ta shige da fice akan haka.

Yaro kan da ya saba da ganin Abba don haka kawai zai bushi iska ya zo kano ganin Adil kada ku manta yana da wasu jikokin na Yara mata amma shi wannan gani yake kamar na shine baki
aya, yaron ma ya saba da shi.

Ai kuwa shekarar da aka kawo shi Abba ya tafi da shi Umara, saboda gata da soyayya.

Iyayen Yaron hakura suka yi suka barwa Abba Yaron.

Har suka gama karatunsu.

Kwatsam Ya ado ya samu aiki a Abuja yana can ita tana aiki a Bauchi, Allah ya kara mishi wani nasibi a lokacin tana goyon Ummu Salmah, a shekarar suka koma Lagos domin wani Shari'a yayi kuma yayi nasara, sai gashi cikin ikon Allah suna ta gaba a Lagos itama tayi master dinta, wnada ya kara d'aga darajarsu.

Abba ya basu dansu domin zai fi dacewa su daura shi yadda suke so.

Shekararsu daya a lagos ta haifi Princess, yanzu shekarar su biyar kenan.

Bayan sun ci abinci, suka yi sallah Magariba, sai a lokacin Ya Ado ya zo ta tashe ni.

Bayan na farka na bude idanuna addu'a nayi sannan na tashi na shiga ban daki, nayi alwala nazo na gabatar da sallah Magariba, ina idarwa Aunty Zakiya ta shigo tana waya.

"Gata nan Hindatu kada ki fasa min dodon kunnena." Ta fada tana murmushi.

Mika min wayar tayi tana fa
in.

"Gashi idan kin gama muna jiranki a kasa zamu ci abinci." Karban wayar nayi ina kallon kasa.

" Auta kin isa lafiya?

Na kira dazun wai kina barci.

" Inji Aunty Hindatu, " Eh ban jima da farkawa ba!" Na fada a sanyayye.

" Ya kika ga garin?

Yayi miki ko?

" Ko bai min ba dole na amsa da dai na cigaba da zama a Bauchi Ya Hafiz yana min barazanar zai sace ni.

" Yayi min!

" Na furta a hankali, ina wasa da bakin hijab din jikina.

" Auta ki saki jikinki kin ji ko." " Ehmm!

" Nace mata bayan nan shiru nayi, , Ya Ado yace zaki fara ganin likita ko?" Shima sai da nayi shiru kafin nace mata.

" Amma ai lafiyata lau." "Eh lafiyarki lau kai, amma ana son ki ga likita da kyau." Shiru nayi ina jin yadda take ta bayani da ta fahimci ba zan iya cewa kome ba, sai ta kyale ni.
Chapter 31 · 0% Book details