← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 86

Sashe 12

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai na mai da hankali kan aikina, buga gidan aka yi na mike na je na bude makotanmu ne, na bude suka shigo suna ta fara'a.

"Sannun da zuwa, sannu mu shiga daga cikin." "A" a waje ma ya isa wannan zafin ai kuna shan fama musamman wacce take wannan dakin zata fi kowa shan zafi ita da jin sauki sai ko damina ko hunturu." Murmushi nayi bayan ma shiga daki na dauko musu kafet na shimfida musu.

Sannan na shiga na dauko musu pure water na ajiye musu ina kara gaishe su.

Sun amsa sannan na ce musu ." Bari na kira muku abokiyar zamana!

" Na tashi na buga kofar Karimah dakyar ta fito tana wani hade rai, suka gaisa sama sama, sannan ta koma wata yar yarinya ce ta bani sha'awa, na dauke tana ina fa
in.

"Ina Mamanta!" Murmushi Mamar tayi tana fa
in.

"Sunanta Suleimin" gashi yarinyar tasha wanka an gyarata.

"Allah sarki sunana Lubabatu amma ana kirana da Lubnah!" Fitowar Yusrah ta ce min..

"Lulu zan sha tea!" "Tow ina zuwa!" Na shiga dakin da kananun kofina uku na hada har da na yarinyar na fito waje na mika musu itama yarinyar na mika mata.

"Har da dawainiyya!" Murmushi nayi ina kallon yarinyar, don ta shiga raina duk inda zan ga Yaro kamar na dauke shi nake ji, haka muka yi ta hira ina leka kitchen din, dab Magariba suka min sallama, sannan suka min bayanin gidansu ne a bayan na mu, ita babbar cikinsu sunan ta Maman Abidah ta aurar da ita ma, sai yan mata biyu Na'ilah da Na'ima, sai ta gefenta ita kuma Maman Boy da alamu ita kamar yare ce, Yaronta daya Boy tana sayar da kayan miya da sauransu, sai Maman Suleimin, sai wata kamar Amarya ta ce min.

"Ni amarya ce!

Akwai Maman Salim da Maman Yaya basu gama aiki bane amma zasu shigo gobe!" Na musu godiya na rako su waje, suka tafi.

Na dawo na karasa aikina tare da jollop din macaroni.

Wurin karfe bakwai ya shigo shi da likitan ya kara duba ni ya saka min ruwan karshe sannan ya bani shawara yadda xan kula da kaina, sannan ya tafi Ya Hafiz ya ajiye min leda bag din da ya kawo min, ya shiga bu
ewa, yana fa
in.

"Gashi nan ki ci, amma ki sani kudin wannan abin da nake miki shima dai rantowa nayi!" Gyada kai nayi nace mishi.

"Na gode!" "Ba fa batun godiya biya zaki yi ai kin sani biya zaki yi a tow!" Daga nan ya mike ya bar dakin.

Sauran kwanakin da suka biyo baya, na ji sauki makotana sun shigo, bayan kwana biyu nima na shiga musu muka gaisa sannan na dawo, nayi haka ne don fita hakkinsu, sannan a gefe guda Karimah tana d'aga min hankali rigimar yau daban na gobe daban, haka yasa kullum ya dawo sai ya ji kamar ya rufe ni da duka, haka xan ta bashi hakuri.

Kusan wata mun
aya a zango, Ya Hafiz bai tab'a cewa na kira gida na gaya musu mun tashi ba, sai da ya ji a ransa.

Ya kalle ni da zai tafi kasuwa ya ce min.

"Yau ina ga zaki yi baki me nene babu a gidan?" Shiru nayi kafin na ce mishi.

"Kayan miya, shinkafa ma ya kare" nayi ta mishi lissafin abinda babu, koda ya fita wurin karfe goma sai gashi da kayan abinci niki -niki, ya kawo dakina ya ajiye su kwalin madara da milo duk ya kawo dakina ya zuba, sannan ya sakar min murmushi.

Tunda na ga haka na fahimci akwai wani abu a kasa, sai dai kamar kullum ina mishi fatan shirya sannan ina da yakinin zai daina abinda yake yi.

Haka na
dawo dakina na kara kintsa dakin na fito na daura abincin rana.

Ina waje wayata da babu chaji yayi kara na shiga dakin.

Ya Umar na gani kamar nayi kuka na
auka.

"Yanzu Lubnah kin kyauta baki gaya mana kun tashi ba?

Har shi Hafiz din ya iya gaya mana?"
asa magana nayi ina jin shi.

Yayi ta fada sannan ya kashe wayar, Aunty Hindatu ta kira ni.

"Auta me ya faru?" Murmushi nayi mata nace mata.

"Ba kome Aunty!" "Lubnah idan kika cigaba da shiru taya zamu taya ki wannan yakin, wannan ba hujja ba ne, Lubnah ki bude baki kiyi magana ki gaya min me ya faru?" "Ba kome!" Na kara fada mata, "Lubnah ina takardun gidan can?" "Don Allah kada ki tambaye ni, don Allah kada ki saka min magana!

" Na fada kamar zan yi kuka, murmushi tayi ta ce min.

"Shi kenan idan kina bukatar kudi zan turo miki da dubu dari!" Ban ce mata kome ba, ta kashe wayar.

Zuwa yammacin ranar sai ga Aunty Innah ta shigo ita da Aunty Jamilah matar Ya Umar, ganin gidan yasa duk suka yi shiru.

Ni dai ban ce musu kome ba, shine dai yayi ta fada yana fa
in.

"Ai ban san me ye matsalar Lulu ba, ace bana gari domin Allah ya gani nayi tafiya kusan wata guda nayi tare da Karimah kuma na bar mata yaran jiya da muka dawo nake tambayarta ashe bata gaya muku, ai har nayiwa Baban Bauchi bayanin dalilin tashinmu, amma in sha Allah kafin nan da wata shida zamu koma wani hatsari ne ya faru amma an shawo kansa.

" "Allah ya kyauta ya kiyayye na gaba!"
"Amin Ya Allah, Luluna idan zasu tafi ki diba musu tsaraba nan, akwai wasu a dakin Karimah bari na kawo sai ki hada musu." Ya tashi ya fita, can sai gashi dauke da jaka cike da fruit, ya kawo musu da Naira dubu goma a ciki wai su yi kudin abin hawa, Aunty Innah ce ta kawo su a motarta, bayan fitarsa da ya ce musu bari ya tafi muda lawan akwai kayan da aka kawo zai je ya duba, ya fita Aunty Innah ta kalle ni yadda nayi shiru.

"Tunanin me kike yi?" Ta ciro ku
in da yake cikin jakar ta ajiye min a gefena.

"Mu yan uwanki muna jiranki duk lokacin da kika shirya ba zamu kashe miki aurenki ba!" Tana gama fadar haka suka mike tare da barin kayan ma baki
aya basu dauka ba, domin tun kafin su fita Karimah ta fita da Yaranta, aka bar ni a gidan ni daya tal.
*08130269641*
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: *ALA
AR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu
BAKWAI
Zama nayi ina nazarin makomar rayuwata, me nayi na kuskure?

Duk da ina son Ya Hafiz amma ban san me yasa yake jin dadin daura min laifi ba, shi ya hana ni gayawa mutane, yanzu yazo yana fa
in ni ce me yasa yake min haka ne?

Me yasa tow?

Dama soyayya tana zama kiyayya ne?

Ina cikin wannan tunanin Baban Bauchi ya kira ni, wato Abbanmu yayi ta min fada yana fa
in nayi haka ne don ba lalata zumuncin da yake tsakaninsa da
an dan uwansa, wallahi ban isa ba.

Haka ya gama fadar shi nace mishi yayi hakuri.

A hankali kuka ya zo min can kuma na fara dariya kamar mahaukaciya, domin haka ne kawai zai saka ni jin dadi.

Tunda na fahimci dariyata tafi kuka saka ni nishadi, na saka a raina na daina kuka akan Ya Hafiz, zan yi dariya.

Aunty Hindatu ta zo ita da Ya Sani suka ga gidan, babu wanda yayi magana har suka fita.

A ranar Aunty Hindatu ta kira Ya Ado ta gaya masa.

Murmushi yayi yana fa
in.

"Hindatu dadina dake baki da hakuri, mutane biyar suke da iko akan wannan lamarin Baban Bauchi, Baban Jama'are, baba malam, sai ita Lubnah idan ta ce bata yi duk inda nake zan kwana a Bauchi, amma fa sai ita da kanta ta ji a ranta bata yi duk abinda zamu yi ba yadda muka iya.".

"Amma kasan ya sayar mata da gidanta na Tambari?" "Tow ya za ayi tsakanin mata da miji sai Allah idan ita ta bashi fa!" "Ado kasan sai Lulu bata da hankalin da zata bashi gida ya sayar ko?

" " Tow waye ya sani kin ga idan tana bukatar wani abu ayi magana batun gida dama ai an saya mata ne domin su huta da Yawon gidan haya tunda ya sayar ya sayi wani." " Amma ai a getto area ne!

" " Ba gashi ta zauna har na wata guda ba ta gaya miki ne?" Shiru tayi ya cigaba da magana.

" Baba da Mama sune suka involved din rayuwar Lubnah, idan da zasu tsaya mata Lubna zata samu yanci amma fa sai taso idan bata so ba, kuwa koda su zasu shiga ba zata matukar bata bada hadin kai ba.

Babu yadda zamu karshe sai dai shara'a tayi aiki kanmu haka magatakarda kin manta da dokar ce.

" " Ba dokar na manta ba, na hango tashin hankali da bukatar taimako, bata bukatar kome amma kuma idanunta yana kukan tsoron da niman taimako, wallahi Lulu da ka sani ba ita ba ce a gabanmu"
Dakyar ya shawo kanta Ya Sani ya ce mata, "Ni dai na rasa me shegen Yaron nan yayiwa Abba ne da baya kaunar laifinsa, ki ga yadda Lulu ta koma don Allah?

Ko ni da nake zukar wiwi wallahi ban ga dalilin dariyar da take ba, ki ga yadda take abu kamar wacce take cikin tashin hankali."
Kwafa yayi suka cigaba da tafiya,
Ko Ya Hafiz ya ji abinda yake faruwa ne, yadda Yayuna suka fusata, sai gashi ya tafi har Jama'are wurin Kakanmu, suka tawo tare yadda mutumin nan yake da mugun hali na tsane na bude idanun na ganshi, domin shima ya taka rawar lalata min duk lissafina, haka yayi ta fada da nuna kada ya ji kada ya gani domin yaji labarin ana son a kashe auren Lubnah da Hafiz, idan suka kashe auren waye zai aure ni?

Sannan ga misali a gabansu Jalilah tunda aurenta ya mutu waye ya zo da sunan zai aure ta, kada ya ji kada ya gani.
Chapter 12 · 0% Book details