← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 86

Sashe 41

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka na saka abaya mai sauki.

Sallah da kwana biyar muka dawo gida, haka na cigaba da jinya satin mu daya da zuwa dai ga Aunty Hindatu da Aunty Innah, Aunty Munah da Aunty Raliyah, wato wani abu da na kara fahimta shine yadda suke yiwa Aunty Zakiyah shatara na arziki, ban yi mamaki ba domin basu isa biyanta Alkhairin da take min, bamu isa biyanta biyan ba, Dr Dijah Bala da Baby sun zo min ya jiki, haka Aunty Zakiyah ta cire musu tsaraban da ta musu.

Tace musu nice nayi musu sai nayi ta mamaki, wani ikon Allah satinsu Aunty Hindatu daya suka koma.

Wata na biyu goshin layya ina jin duk wanda ya ganni sai ya ji na burge shi, domin jikina ya ragu, a lokacin da Ya Ado yake basu labarin jinyar da nake fama da shi, Aunty Munah sai da tayi ta Bala'i ita sai ta shigar da Hafiz kotu, aka ce a kyale shi tunda na samu sauki yanzu ai da sauki sosai sai a tafi gaba.

Haka yasa suka tsayar da shawarar ko zan koma makaranta, nima zaman gidan ya dame ni.

Don haka na ce tow, na amince da shawararsu na koma jami'a a karo na biyu.

Zanyi MBA wato Master Business Administration and specialization, a tsarin tallace-tallace, Ya Ado.

Kullum tambayata yake.

"Lulu zaki iya kuwa?

Idan kin san har yanzu akwai abinda yake damunki a hakura da shi, kin ga saboda result
inki yayi kyau sun baki shekara biyu da wata shida, idan kina ganin akwai matsala a hakura." Yadda Ya Ado ya saka hope a kaina sai naji kamar idan nace mishi ban warke ba ban yi mishi adalci ba.

Haka na ce zan iya amma har yau ina tsoron shiga Mutane, ya zanyi tow?

Zan tabbata ina zaman gida ne, haka na daure sabon shekara na shiga cikin daliban da aka diba, na kwantar da hankalina, a yanayin acadamy calendar dinmu ba zan wuce shekara daya da wata tara zan gama.

Haka yasa na nutswa, daga yanayin shigar da nake yasa an Makarantar suka fahimci na fito daga arewa ce, sannan yanayin fuskata, kuwa face mask nake sakawa saboda har yanzu fuskata kamar an buga donut, haka nayi ta rayuwa da tare da mai da hankali kamar ina yi da wani.

Yadda an ajin mu suke mamakin domin kusan nice karama amma yadda nake mukekiya sai ka dauka na shekara arba'in, a hankali na fara fuskantar body a shame, haka yasa na fara tsargu.

Wani lokaci a tsorace nake shiga ajin.

Sai ta min dariya ko tsokanata wani lokaci sai naji ana fa
in luxury, ko naji ana fa
in super Mama, haka yasa na fara jin wani irin yanayi ya fara shigata.

Ban san me yasa nake jin wani irin damuwa ba, duk yadda naso na kauda kai amma na kasa sai tsoron da nake binnewa ya fara tasowa.

Haka muka yi huta First semester din mu,
Haka muka yi hutun sati sati biyu da kwana hudu, zai kama Monday mai kamawa.

Yau ya kasance Lahad, ana gobe zamu koma makaranta.

Ina ta
an hada kayan makaranta na nutsu naji wayata tai kara, dauka nayi a hankali.

Na saka a kunnena.

"Ru
iyar tsutsa mara haihuwa!" Ji nayi gabana yayi mugun bugawa a ina Ya Hafiz ya samu numberta yadda yayi ta gaza min magana har sai da naji kaina ya fara sarawa, hawaye ya fara zuba min kamar zan mutu kuma ya rantse min idan na sake na kashe wayata abinda zai min sai na rasa inda zan cusa kaina.

Haka ya gama cin mutuncina sannan ya gaya min ko mutuwa nayi a gidansa za a min sutura, kafin ya kashe wayar, wurgi nayi da wayar yadda ya tsorata ni na ji wani irin tsoro ya kama ni.

Dakyar nayi barci cike da tsoro wanda ya haifar min da mugun mafarki da rashin hankali.

Daidai buguwar agogon bangon dakin wanda ya ja burki da wani "ki...ki" cikin barci nake amma sai da naji gabana yayi mugun faduwa, bude idanu nayi ina kallon hasken waje tare da bishiyar da take kad'awa, hadari ne ya gangamo amma sai naji kome ya tsaya min, barcin ma na nime shi na rasa, Innalillahi wainnalihir rajoun, yau ya xan yi ni da ya dace na farko tun 4am.

Da sauri na sauka a gadon na shiga ban daki nayi wanka da brush, sannan na ha
a da alwala, na fito ina jin kamar zuciyata zata fado, saboda tashin hankalin.

Ina shafa mai na saka kayana, sannan na gabatar da sallah asuba, lokacin ruwa ake tsugawa kamar da bakin
warya.

Ji nayi kome na kaina ya sake kuncewa wai ma yau ba Monday ba ne koda yake abinda ya faru jiya ne ya d'aga min hankali Ya Hafiz me yake nufi da Ni ne,? na dauki jakata na rataya zuciyata tana wani irin bugawa,, sannan na fito parlourn na samu Ya Ado wanda shima cikin shirinsa na zuwa aiki.

"Ina kwana Ya Ado?" "Lafiya lau Lulu kin tashi lafiya!" Gyada kai nayi na nufi kitchen inda Aunty Zakiyah take aiki na ce mata.

"Good Morning Aunty Doctor!" "Morning My love, kin tashi lafiya" "Alhamdulillahi!" Ta mika min abincina.

Tsayawa nayi ina kallon abincin, ina son na yi mata magana amma kuma ban san yadda zance ba.

"My lovely ya dai?" "Wai dama abincin!" "Idan ba zaki koshi ba kawo a kara meye amfanin niman da muke?" Sai naji hawaye yana shirin zubo min, na kalleta a hankali na ce mata.

"Na gode!" "Kada ki yi min godiya kuma ki dauke hawayenki domin Barista sai ya kusan cinye nama na danye!" Murmushi nayi da ya kara fitar da kumatuna waje."na gode!" "Sai ki yi!" Ta fada tana barin kitchen din, kasa fitowa nayi na zauna a saman kujera tamu ta hausa yar tsugunne, na shiga tura abincin.

A hankali nake turawa baki
aya sai naji taste din abincin ya fita min a kai.

A yayinda
walwata da zuciyata suka hasaso min wani lokaci can irin wannan zaman nayi ina cikin abincin.

Hawaye ne ya shiga zubo min ban san me yasa a duk lokacin da zan tuna wani bangare na rayuwata nake jin ciwo da zafi ba, kuka ne ya kwace min,.na ajiye abincin ina mai toshe bakina, na nufi pampo ina shan ruwa.

Kalaman da aka fada a can baya yau jin shi nake kamar yanzu ake fada min. *Rubabbiyayyar tsutsa mara amfani, ke ba haihuwa ba sai kayan tsoka kamar tsutsa.

Aikin kenan ga baki ga ci darling kama take da irin tsutsan da suke cikin kashi!* Amai ne ya zo min sakamakon kwarewa da nayi da ruwa, nayi ta tari wanda yayi sanadin shigowarsu dakin.

"Lubnah lafiya?" Kasancewar idanuna yayi jajjur sai kukan da nayi ya tafi a kan kwarewa nayi.

"Sannu kin kware ko?

Kin ma ci abincin kuwa?" Gyada kai nayi nace mata.

"Na ci!" "Tow muje parlourn ina ga haka zamu tafi fa!" "Abban Naylah bata ci abincin ba wallahi!

Bari na mata park dinsa a cikin lunching box ta tafi da shi." Kallona yayi yaga ina sunkuyar da kai tare da kare fuskana, kaina a kasa ina sunsukuyarwa.

Hannunsa ya kai zai tab'a ni, nayi maza na kare kaina daga shi har Aunty Zakiyah suka zuba min idanu.

"Ba dukanki zai yi ba!" Ya fada tana kallona, shi da yake namiji ya kasa jurewa fita yayi yana zaga parlourn.

Hannunta itama ta kai na koma jikin bangon kitchen din na makale.

"Ba dukanki zamu yi, Lubnah me yasa kike dawo da abinda ya wuce?" Wurga-wurga idanuna na fara kamar wacce nayi karya ko sata na ce mata.

"Ba haka ba ne,.na zata zai dake ni ne don ban ci abincin ba."
"Lubnah wani yana threating dinki a makarants ne?" "A'a Aunty don Allah kada ki yi da karfi ya dauka ko wani abu ake min." Na fada ina kallonta tare da rike hannunta alamar roko!

"Na ji amma me yasa?" "Ba kome!" Sai ta yi ta kallona da dukkanin zuciyarta take tausayi na.

"Kina da kyau!" Ta fada shafa kumatuna nayi da suka kasance kamar donout ya sha bugu.

Sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa, don nasan hala itama zolayata take.

"Ina jiranku fa!" Ina ga bai rufe baki ba na rigata fitowa waje, kallona yayi ya ce min.

"Idan kin gama muje.

Gyada kai nayi tare da
aukar jakata, na amshi lunching box din na fito ya bude min mota na shiga.

Ina kallon kayan wasan Yaran da ruwa yake sauka akansu.

Haka muka bar Estate din, ya kunna karatun Alqur'ani a muryan Sheikh Afif, muna tafiya yana bin karatun.

Nima a hankali nake bi, suratul lukman....
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 25
"Akwai wani abu ne?" Ya Ado ya tambaye ni, girgiza kai nayi ina danne damuwar da take fuskata.

Tuki yake har ya iso makarantarmu, sannan ya juya bayan motar ya dauko lema guda biyu ya mika min daya shi kuma ya dauki daya muka fito tare, har cikin makarantar ya raka ni wurin department dinmu, daga nan ya wuce office din HOD, ban san me ya faru ba, sai dai bayan tafiyarshi, HOD dinmu ya shigo yayi magana sosai sannan ya kara da cewa.

"Cin mutunci ko cin zarafi abu ne da ba a yarda da shi, idan kana ganin zaka yi tow kayi a wajen makarantar nan, daya daga cikin manyan lauyoyin jahar nan yayi dokaciya akan kanwarsa, idan ka sake ko kika sake wani abu ya faru na cin zarafi ku sani abin yana da doka a kundin tsarin mulkin kasar nan, kuma za a hukuntaka daidai da laifinka ko a yanke maka hukuncin zaman gidan kaso!" Jin hakan na sha jinin jikina, tabbas Ya ado ne, wannan dokaciyar sai ta sama min yanci duk da naki yarda na saba da kowa domin gani nake zasu cutar da ni, s gefe guda barazanarshi ya kara d'aga min hankali, ko barci nake ya kira ni ban isa d'agawa ba, Ya Hafiz ya hana ni sakat, saboda tsananin tashin hankali sai na fara jin kamar anya na cancanci farin ciki?

Domin ya Hafiz bai da burin ganin nayi rayuwa cikin sallama.
Chapter 41 · 0% Book details