Sashe 81
Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Eh Bauchi zamu koma, mu je ki zauna har Allah ya kawo miki mijin aure." "Alhamdulillahi Ubangiji ya amince!" Na fada mata, domin kuwa babu amfanin zan yi musu da Mama domin duk abinda zata yi tana yi ne domin ni.
Can ina tura abincin ta cewa Ya Ado.
"Jiya Yaron Rufa'i ya kawo min hoton abinda yake faruwa , Adamu ka min adalci!" Girgixa kai yayi cikin ladabi ya ce mata.
"Ni ba zan ce ni adali ba ne, amma nasan ke Adalar uwa ce wacce take tsaye domin Yaranta akan me zan musanta abinda kike da hujja a kai, nayi kuskure babba na sakaci da tarbiyyar da kika bani, amma ki yi hakuri haka ba zai kara faruwa ba." Akwai wata duniya da Allah da kanshi ya ginawa Uwa domin Yayanta, wannan duniyar iya uwa da
anta suke ninkaya a cikinsa.
Murmushi tayi ta ce mishi." Ban ga gazawarka, amma Lubnah ba zata koma aikin nan ba, idan har shi shugabanta mutumin kirki ne, da kanshi zai zo nimanta, idan kuwa mutumin banza ne ba zai tab'a zuwa ba sai dai ta je mishi.
Nan da sati ba zata aikin ba." A hankali na saukr ajiyar zuciya, mother like no other.
Duk wannan abinda take don mutuncina da kimata take.
Haka na kwashe kayan abincin na kai kitchen suka yi ta hira, haka suka tafi aiki suka barmu, nima ina gamawa na ce ta shirya muje gidan Aunty Nuratu Kafaya, haka kuwa muka tafi a can muka wuni sai yamma likis muka dawo a gajiye, har ga Allah mutane sun mana mummunar fahimta, amma yadda na fahimci Mama bata Zafaffa ba, amma kuma ta zuba idanun tana kallonmu ni da Ya ado, maganar gaskiya Ya Ado shi ya ma manta da batun, a daren ta amshi wayata ta kashe, ban wani damu ba na bar mata dama Ya ado ya gaya min na dauke kaina akan kome.
Ranar da Mama ta cika kwanaki biyar da zuwa, bayan sallah isha ina sama ina gyara kayana, Princess ta shigo tana fa
in.
"Aunty ki zo inji Kakar Bauchi." "Ok!" "Ok ina zuwa." Na fada ina tattara kayan, can na fito sanye da riga da wando palazzo sai rigar iya gwiwata kaina sanye da hula, tun kafin na isa parlourn mayyen kamshin turarensa mai mugun kama wuri ya min maraba, da hanzari na sauko ina son gani da gaske ne shi din ne.
Da gudu Yaran kanwarsa suka rungume ni.
"Mom ita ce mana kin daina zuwa aiki, waye ya miki laifi?" Jan kumatunsu nayi na ce musu.
"Break na
auka." "Yaushe zaki dawo?" "Mama ta ce zan tafi Bauchi!" Na fada ina satar kallonshi, ya fada kamar bai da lafiya.
"Eh zata koma Bauchi da zama!" "Kakar Bauchi, ki barta kin ji Mom tace tana da kirki, kuma nima ai ta min kirki." Murmushi Mama tayi tana fa
in.
"Tow kishiya amma ba zan bari ki aure min Alhaji ba, domin nima ina da gashi yala-yala irin naki." Dariya Ilham yayi tana fa
in.
"Kaka ai naki yayi fari, ba irin na Aunty Lulu ba ne, ita nata fa ranar donut na ga tayi da shi ko Mom bata donut.
Uncle kace kai ma Mom
inka tafi Aunty Lulu gashi, amma tana kama da Mom
inka." "Da gaske Bro haka ka fada musu." Bai ce kome ba, ni ce ma nayi maza na toshe bakinta, na mata rad'a a kunne.
"Bakyau fadar sirrin da kuka yi da wani ko?" Na fada ina kallon Mama da take kallona.
"Aunty Jasmin ya kwana biyu?" "Alhamdulillahi, kin ajiye aiki ko?
Brother ma jiya aka sallame shi bai da lafiya!" Da sauri na d'ago ina kallonshi, ya tara Kaduna, sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa na ce mata.
"Allah ya bashi lafiya!" "Amin Ya Allah, yaushe zaki koma aikinki?"
Gyara zama Mama tayi sannan ta ce mata.
"Ta gama aiki da ku ai, zata koma Bauchi ta cigaba da aikin a can anan ana bibiyar rayuwarta.
Sannan su wa
anda hotunan ban san ma'anarsu ba, na ji ance kai ne mai gidanta." Shiru yayi yana kallon hotunan daya na wurin abinci ne, na biyu na Eko hotel ne, na uku dawowarmu daga Japan.
Tasowa yayi ya durkusa a gaban ta.
Cikin sanyin murya ya dauki hotunan ya ce mata.
"Kasancewarta sakatarinya, ina bukatarta a kusa da ni.
Wannan wani kasuwanci muka yi shine sanadin da ta bi ni hotel, wannan gidan abinci ne bata ma ci ba sai tawowa tayi da shi, na uku tafiya ce na kasuwanci.
Na rantse miki da wannan rayuwa da mutuwa take hannunsa, sai da tace min ba zata ba, har wata ta ce zata nace a'a.
Mama!
" Ya kira sunanta a hankali, cikin rarrashi da niman afwa ya ce mata.
" Ko bayan ranki, Yarki ba zata zubar da mutuncinta ba, ba zata wulakanta tarbiyyar da kika mata ba.
Mama da ace Yarki zata yi wani abu da tayi.
" Kallona yayi kafin ya sunkuyar da kai kasa, ya cigaba da cewa." Allah ya sani ita din Mutuniyar kirki ce, kamila ce, Saliha , mijinta ya dace da mace ta gari.
Yaranta zasu yi Alfahari da ita a matsayin Uwa ta gari.
Don Allah ki barta anan wallahi ni da kaina zan tayaku kare mutuncinta, kamar yadda xan kare uwar Yaran nan da su Yaran Lubnah ma zan kare mutuncinta." Ceo yana da hikima,.
A yadda yake iya kasuwanci da mu'amala da mutane haka duk wanda ya zauna da shi sai ya fahimci haka.
Kaina a sunkuye ina wasa da yatsuna ina jin tsigar jikina yana mikewa, ina
ara jin wani abu yana tab'a ruhina da zuciyata, d'ago kai nayi ban san yadda aka yi na ji yana bani tausayi ba, a yau na ga yadda damuwa take cike da idanunsa, zuciyata tayi rauni ainun.
Kasa jure yadda yake rokon Mama nayi, na riko hannun Yaran muka wuce sama, kafin nayi nisa na tsinci wasu kalmomi da suka fito daga bakinsa.
"Ni maraya ne, amma ina da gata.
Na fuskanci cin amana tun ina yaro har zuwa yau da nake gabanki, duk cikin mutanen da suke zagaye da ni daga Kanin Mahaifina, sai Jasminah kanwata sune basu tab'a cutar da ni ba, sai Yar autarki.
Ita ce bana gabanta.
Tun fil azal haka." Shiru yayi juyowa nayi ina kallon yadda ya sunkuyar da kai kasa.
"Bana zo nan akan ta koma aiki bane, na zo ne na bata hakuri akan abinda aka fada a kanta.
Idan ma ina son lalata ai ba zan yi da ita ba domin ta fito daga gidan da yake da babban zaure, ita din fata ce da yakini." Murmushi yayi sannan ya ci-gaba da cewa.
"Zata iya rubuta takardan barin aikin na gode da bani aronta." Yadda Mama ta fahince shi kaf duniya babu wanda ya mishi irin wannan fahimtar.
Amma tayi murmushi kafin ta ce mishi." Zan barta na wani lokaci, na ga kamar kana da bukatar haka, amma ka ji tsoron Allah kada ka kara daukarta zuwa wata duniya, yanxu an daina kiwon dabba mutane ake kiwo, idan har na ga wani abu ba haka ba raina zai b'aci.
Duk da ban san sunanka ba, amma kayi wani abu da na kasa fahimta, Auta ta kasa zama ta ga kana rokona.
" D'ago kai yayi yana kallon Mama jinjina kai tayi.
Ta ce mishi." Ban san wacce alaka ce a tdakaninku ba, amma kuma naga ta kasa zama ta wuce sama da Yara, da kace kai Maraya ne ta tsaya cak, nasan wace ce ita.
" Murmushi tayi ta cigaba da cewa." Allah ya dafa mana!
" Tayi shiru, tana kallon Ya Ado, gyada mishi kai tayi tana kallon Turaki da yake gabanta, tabbas idan har abinda Ado ya fada mata gaskiya ne, Yaron ya cancanci zama da Lubnah.
"Amma ya batun iyali!" Shafa kai yayi yana murmushi, kafi ya ce.
"Na so wata yar Bauchi tace bata sona na mata kama da gardawa tun daga lokacin Daddah take karbo maganin aljanu sun aure ni." Ai kuwa parlourn aka yi ta dariya, Mama ta ce mishi.
"Kuma yanzu baka da wacce tace tana sonka ai kai ba dai budurwa ko?" Shafa kai yayi ya ce..
"Mama na baki wuka da Nama ki nimo min wacce zata iya da tsufa." Rike baki tayi tana fa
in, "ai kuwa zan iya cewa babu wata Y'a a gabana da na baka ita!" Sosa kai yayi yana fa
in.
"Ikon Allah, babu ko kanwar Lubnah ce." "Gaskiya bani da ita, Allah ya baka ta gari." Ta yanke hiran, duk yadda ya so Mama ta yi mishi barin zance akan Lubnah amma fir taki, don shi har yau kallon matar aure yake mata, sai yayi shiru wurin karfe goma suka bar gidan, duk sun fita ina bakin kofar, ina kallonshi.
D'ago kai yayi ya kalle ni na dauke kaina, ina jin Jasminah tana cewa.
"Mama gobe ta zo aiki don Allah." "Ubangiji ya kai mu gobe lafiya!"
Bayan tafiyarsu na riga su wucewa dakin Mama na kwanta da tazo dakin sai da tayi sallah shafa'i da wutir, bayan ya idar ne ta cigaba da addu'a.
Har na fara barci ta ce min.
"Kina son Mai gidanki ne?" Da wani sauri na tashi zaune ina zare idanu.
Kirjina yana bugawa da karfi.
Murmushi tayi ta ce min.
"Eh kina son shi Lubnah." "A'a wallahi Mama, ni ba wannan a tsakaninmu idan ma ya gaya miki wallahi karya ce." Hannu ta kai bakina ta rufe.
"Bai gaya min haka ba, amma ni naga haka a tattare da ke, ni Uwa ce kuma dole na fahimci haka amma tunda kin ce bakya sonshi ai shi kenan amma ki sani kafin Azumin ba
i ina son ganin mijin aurenki don Allah na baki wannan lokacin ne domin ki samu wanda ya dace da ke, amma ni idan har zaki dauki shawarata wannan mutumin yana bu
atarki sosai.
Yana sonki yana kuma girmamaki!" Murmushi tayi.
Sannan ta kwanta kamar nayi kuka haka na ji maganarta taya zata ce yana sona bayan kuwa ba wani mutumci muke ba, haka na kwanta sai na kada barci nayi ta juyi.