← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 86

Sashe 57

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan nima na samu nutsuwa irin taki haka Uwar mijina zata min hidima?" Juyawa tayi tana kallona cike da mamaki ta ce min.

"Kina da saurayin ne?" Girgixa mata kai nayi da sauri ina rike bakina.

"Da gaske kina da interest akan aure?" Ajiyar zuciya na sauke na ce mata.

"A'a ni fa kawai yazo bakina ne, bawai don ina da ra'ayin yin auren ba ne, sannan wa nake da shi?" "Doctor Ahmad!" Kallonta nayi nace mata, "don Allah mu bar maganar nan Allah ya gani bana son shi, kuma ban tab'a daukar shi a matsayin wanda zan zauna da shi ba, asalima yaya na dauke shi, don Allah kada wani ya ji ya dauka ko na ajiyewa wani ne!" "Lubnah zo ki bani document dinki ga wani opportunity ya samu Allah yasa a dace!" Fitowa nayi na samu Ya Ado ya nutsu akan computer dinsa, ya d'ago kai yana fa
in.

"Oya dauko min takardunki zan rubuta miku VC letter ana niman ma'aikata har da masu irin matakin karatunki." Haurawa sama nayi da gudu na gaji da zaman gida kusan for good 3 yrs, a yanzu fa ina ina gudu ni kaina sai naga ina burge kaina, ba da kamar wata bukka ba, amma a yanzu jikina a tsantsame.

Wargaza wardrobe dina nayi na kwaso takardun na sauko da gudu na kawo mishi, sannan na tsaya a bayanshi ina ganin yadda ake cike vc din.

"Wacce ma'aikata ce a ma'aikatan sufurin kudi ne?" (Wato ministry of financial) " Kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY ne!" Wani yatsina fuska nayi ina fa
in.

" Wannan ba zai wani abun arziki ba idan ba zaman shan shayi ba!

Amma ai kudi yana aikin gwamnati!" " Ki cigaba da jiran aikin gwamnati idan a kasan nan ne kafin ki samu aiki da takardarki, babbar Yarki ta gama jami'a har da yara uku gare ta.

Sai dai ko idan kina son koyarwa?" " Haba Ya Ado, aikin gwamnati bai da wuya kai da kake lauya fa!

" Na fada ina tura baki.

" Ai suma organization ce ta bude firm
insu, ba gwamnati ba sannan baki ga su ma da kansu suna shara'a da gwamnatin ba, kudin da suke samu ana bayansu daga kudin da clients dinsu suke biya ne idan za ayi Shari'a, so su ba gwamnati ba ne, su masu zaman kansu ne!" Inji Aunty Zakiyah, ta kare Mijinta.

"Ikon Allah, a gidan nan ne zaka yi magana da mata miji ya shigar mata kayi da miji matar ta shigar mishi.

Ke ba aikin gwamnati kike ba?" Na tambaye ta ina tura baki.

" Nima da farko wata kungiya ce ta dauke ni aikin wucin gadi daga baya kuma sai asibitin suka ga ana bukatar gurbina.

Idan kuma zaki yi aikin goge goge da share share ai duk aikin gwamnati ne sai ki zo mu baki!" Tura baki nayi Princess ta kwashe da dariya wai.

" Aunty Lulu idan kika yi haka sai ki yi kama da Moana, ki ga yadda kika yi da face
inki, ko Ummu?"
Kallon iyayen nayi da suke ta min dariya, "Allah dai na gayawa Mama abinda kuke min!" Wayar Ya Ado ne yayi kara ya dauka yana magana a hankali, " ok bari na shirya booking Allah ya kawo ku lafiya!"
" Lafiya Ya Ado!??

" " SAN lafiya?

" " Daddy lafiya?" Duk lokaci guda muka mishi tambayar.

Katse kiran yayi ya ce mana." Jikin Abba yaki za a kawo shi nan ne." Ya fada yana kallon laptop din, ai kuwa hankalina ya tashi take na nime walwalar da nake na rasa.

" Shi da waye zasu zo?" Aunty Zakiyah ta jefa mishi tambayar.

Tana kallona.

"Shi da Tahir da Mama ta yadiko zata zauna, matar Sani bata da lafiya tayi bari." Ajiyar zuciya na sauke murmushi tayi ta ce min.

"Zai tab'a samun damar zuwa inda kike ba har abada!" Hawaye ne ya cika min idanun.

Na zauna jikina a mace, "je ki motsa jikinki, yar lukuta." Ba musu na wuce don tasan kuka zan yi, haka ya Ado ya ajiye aikin da yake ya koma nima musu jirgin Jos to lagos, bayan nan ya saka Aunty Zakiyah ta nima musu likita anan kuwa cikin ikon Allah wani abokin aikinta Dr Abraham Abati, shi ta samu ta gaya mishi ya ce mata ba damuwa Allah ka kawo su lafiya.

Bayan sun gama waya sai ga kiran Aunty Hindatu ta ke ce mata..

"Maman Abbana, zamu zo muma amma sai zuwa weekend ki gayawa Mijinki na kira yana busy." "Wayyo Allah Ubangiji ya kawo ku lafiya, don Allah a zo mana da doya." " Amma matar nan baki da kirki a jirgi zamu zo fa!

" " Ku saka a mota ya rigaku zuwa." "Ai kuwa kin kawo shawara me kyau bari na gayawa Raliyah a saka ta jos."
Ai kuwa kamar yadda ta fada a group aunty Munah ta ce musu.

" Ku tura mata dankalin turawa tunda mun fi kusa zan saka a mota idan zan zo!"
Haka suka tsayar da magana, dakin da yake gefena na kara gyara musu, da inda Mama zata zauna a kasa don tace Allah ya kashe ta ba zata kara yarda da yaudareta ta zauna a sama ba, A lokacin muka mai da hankali a gyaran gidan, washi gari Ya Ado da safe yake gaya min cewa.

"Na
tura takardanki!" "Na gode!" "Naga kin fison aikin gwamnati ko?" "Eh mana ga fansho da garatuti, wannan fa idan haukarsu ta motsa zasu kore ka aiki!" "Daga nan sai mu ce miki korariya!" Inji Aunty Zakiyah"Ai duk abinda kike min sai na gayawa Mama ita
aya ta damu da lamirina!" " Gaskiya kan yar lukuta autar mu, SAN baka lura da wani abu ba, su fa yan auta kiba ce da su." Tura baki nayi nace mata.

" Maganarki ba zai yi aiki akan wannan kyakkyawar matashiyar ba!" Na fada ina barin parlourn, ai sun san ba kibar sai dai idan suna son takura min sai su ce min yar lukuta.

Shiga daki nayi na kalli kaina a madubi, wanda yake tsaye zalla.

Ka juya ina kallon bayana, sannan na kalli gabana, ni dai kamar ba mace ba babu ya'yan gwaiba da za a gani ya ja hankalin kowa, wai tsaya me yasa nake tunanin jan hankalin wani ne?

Na ga yan tsakanin nan sai batun wani ko aure, rintsa idanuna nayi sharrin makiya ko?

Zasu sako ni a gaba, na kalli kaina a madubi na ce.

" Ke Lubnah ki nutsu, idan baki manta ba kin sha wuta a hannun Hafiz!!" Daga haka na cigaba da shirmena a madubi, wayata ce tayi
ara na
auka.

" Ashe za a kawo Alhaji ba lafiya?" " Sorry Aunty Nuratu, mantawa nayi ban gaya miki ba, za a kawo shi gobe in sha Allah." " Allah ya kai mu, Allah ya bashi lafiya." " Amin Ya Allah!" Ta lashe wayar kuma fa naje Gym din ni na ma manta da wani kawo Abba sai da na dawo aka tashi zancen, kasancewar yau Laraba.

Da dare muna parlourn Ya Ado ya ce min.

" Ke bani e-mail
inki don na lura yadda kika tsani aikin nan ko an turo miki ba zaki fada ba!" Lubabatushehuusmanjamare'[email protected] daga haka na cigaba da shan fruit dina.

"Shima password din sai na roke ki?" Nifa aikin kamfanin nan sam bai min ba," ni wallahi aikin nan haushi yake bani!

Lulu@19" na fada ina hura hanci, " don Allah dube ta yadda take hura hanci kamar wata sauro ke yanzu baki ji dad'i kin samu aiki a Lagos ba, kin zama big girl!" Kalaman Abba ne ya dawo min........
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 38
" Idan karuwanci ne dubunki sun yi babu riba." Hadiye yawun bakina nayi da yayi min kauri yanzu haka Abba zai zo ba halin na je na ganshi ko na ji muryansa sai na ji lokaci guda tsoronsu ya kama ni daga shi har Ya Hafiz, wani irin masifaffen tsoronsu ya kama ni.

"Lubnah!" Kallonsu nayi na mike a hankali zan wuce sama Ya Ado ya ce min.

"Kina tsoro ko?" Tsayawa nayi ina mai da kwallar da ya cika min idanu ciki na ce mishi.

"A'a kawai im wondering yadda zamu zan ga Abba ne!" "Kada ki damu zaki ganshi." Da sauri na koma sama, ranar dai saboda na saka tsoro da damuwa sai da nayi mafarkin, wai gashi nan Ya Hafiz zai tura shi a rami, amma na kasa zuwa cetonshi, karshe ina ji ina gani ya fada.

Da wannan mummunar mafarkin na farka around 3am, ban daki na shiga nayi alwala na zo na gabatar da sallah Nafilla, ina zaune a wurin har aka kira sallah farko nayi raka'atu fijir, ina idarwa na cigaba da addu'a domin wannan lokacin yana da muhimmanci, karfe biyar da wani abu aka yi sallah asuba nima nayi, da na idar sai na ji na kasa fita motsa jiki, haka na kwanta saboda barcin da ya cika min idanu.

Ban farka ba sai karfe daya na rana, ashe tun karfe goma su Mama suka iso, ganin kayanta nayi a kusa da ni ga kamshin turarenta na Touch me, da sauri na shiga ban daki nayi wanka na saka wata riga irin bubu din nan na sauko kasa, ba kowa a gidan, wayata na koma na dauko na shiga kitchen na hada abincin da zanci wanda ganye yafi yawa na zauna na fara ci a hankali, ina shan tea, a hankali ina kallon tv.

Wayata na kunna, sannan na cigaba da kallon tv ina jin kamar wani abu yana damuna.

Can na duba wayar na kira Mama.

"Mama shi ne ko ki tashe ni?!" Murmushi tayi tana fa
in, "tow sannu ban tashe ki ba jinjiirata na ga kina barci ne kamar mage." Murmushi nayi na ce mata.

"Kun iso lafiya ya Abba da jikin?" Bana gabanta amma yadda ta amsa min kamar irin she does care ta ce min.

"Gashi can ana ta fama da shi." "Kamar ya?" "Tow ai yaki ya tsaya a duba shi dai fama ake yana tirjewa!" Idanuna ne suka cika da kwalla.
Chapter 57 · 0% Book details