← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 86

Sashe 72

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na dakatar dake har na tsawon sati biyu!" "Don Allah Hamma kayi hakuri!" "Get out of my sign!" Da sauri ta fito, ni kuwa bawan Allah nan haka ya kira Taj ya kara jibga min kaya, haka har karshe shida ina wurin ga ciwon ciki, shima don bakin mugunta yana office din yaki fita, fitowa yayi lokacin ina amsa wayar Ya Ado.

"Ya ina hanya ne hau aikin ya min yawa ne, kayi hakuri gani nan zuwa." Na kashe wayar ina mai binsa da harara "mugu kawai!" Na fada ina jin marana yana ciwo.

Taj ne ya shigo yana fa
in.

"Muje a sauke ki a gida!" A hankali na tashi na nufi wurin da Abayana yake na saka, zuwa yanzu na san na bata jikina, shi yasa na saka pad din a inda na zauna, lokacin da da muka sauko ina ta Addu'a Allah yasa na zauna a baya, cikin ikon Allah kuwa bayan na zauna kafin na shiga haka na bude sabon pad na saka a inda xan zauna, kamar nayi kuka, bawan Allah nan mugu ne ko saka abin ban yi a jikina ba.

Haka na shiga na zauna, ina jin kamar nayi kuka.

Har muka isa gida, na dan haska wayata na dauki pad din da jakata na, musu godiya sannan na shiga cikin gidan da sauri, ban tsaya ba ban dakin yara na wuce na wanke jikina na tura Ummu ta dauko min pant da wasu kayan na gyara jikina, ina sauke ajiyar zuciya.

Laptop dina gida na dauko nayi login din na kamfanin ba fara aiki. ......
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 50
Da yake ke yana gaba ne shi da Taj har suka isa Taj ya dauki jakarshi ya shiga da shi cikin shi kuma ya wuce masallaci.

Taj na isowa ya bi shi suka tafi.

Koda aka yi sallah isha taj ya wuce gida shi kuma ya nufi inda motar yake zai duba abu, yana budewa ya kunna wutar motar ya saka hannu ya dauki file din da yake bayan motar, idanunsa ne ya kai kan jinin da yake manne a jikin kujeran.

Mamaki ne ya kama shi.

A hankali yayi lissafi yau ya zo mata, shi yasa take kome sanyi-sanyi.

Kiran Taj yayi ya ce mishi.

"Kace yarinyar nan ta zauna sai Monday!" Ya kashe wayar, sannan ya koma cikin gidan ya dauko kayan wankin ya zo ya wanke sit din ya jingina da motar yana nazarin har yau bata daina fama da ciwon cikin ba ne?

Shiru yayi yana nazarin lamarinta, duk da yana jin zafinta amma a duk lokacin da ya kalleta sai ya ga kamar tana boye wani abu fuskarta, idanunta yana fadar abinda fuskanta yake fa
a daban.

Wayarshi ce tayi
ara ya saka a kunne.

"Oga ban samu numbeta ba, domin bani da shi." "Ok"
Haka ya wuce gidan Ubaid ganin Nihla suka yi ta wasa da Yarinyar amma zuciyarshi tana wani irin yanayi.

Bude wayar yayi ya kara bincike ko ya dauki number wayarta yasan gobe zata zo da mood din.

Amma bai samu ba abinci ya ci ya nufi gidan Uncle Auta, nan ma fura ya sha yana dawowa gidan ya wuce Gym ya motsa jikinsa.

Rabin daren yayi shi akan aiki ne amma baki
aya Lubnah ce a ransa.
----
Kusan har gari yayi tsit ina aiki, tashi nayi na dauko faten da wanke na sha.

Sannan na zo na kwanta saboda hajijiyar da nake ji, haka nayi barci a wahale ban farka ba sai karfe shida na safe.

Na shiga nayi wanka na wanke jikina duk na b'ata zanin gadon haka na hada na wanke da kayan jiya, sannan na shafa mai da body spray.

Na saka kaya irinta hausawa saboda yau juma'a ce, pad dina guda goma na zuba a jakar, domin kada a kara samun matsala.

Doguwar riga ce ta atamfa, sai hijab da na saka yadi biyu da rabi da na saka, na fito Ya Ado ya ce min.

"Allah yasa kada a koro ki, kin makara." Murmushi nayi na shiga muka fita, a inda ya saba ajiye ni ya ajiye ni, na dauki jakata na wuce na jira motar kamr kullum muka wuce, ina isa na biya tare da fita na nufi hanyar kamfanin, a hankali nake tafiya kaina a sunkuye.

Har na kusan kamfanin na ji muryan Khamis, gabana ne ya fadi.

Na kalle shi dauke kai nayi na cigaba da tafiya, karar horn da aka yi fa karfi yasa ni juyawa.

Yau shine da kanshi ba Taj ba.

Daina bina Khamis yayi, ya tsaya matsawa nayi a gefen hanyar yayi kan Khamis da motar ya matsa yana ihu da dariya kamar mahaukaci.

Da yazo kusa da ni,sai ya rage gudun motar yadda nake tafiya a hankali, bar na shiga kamfanin haka yake bin bayana, ajiyar zuciya na sauke ashe bashi daya ba ne a motar shi kan ma yana baya, daya mutumin nan ne.

Fita yayi a motar ya nufi hanyar waje.

Mai tuka motar ya ce mishi.

"Kaga ka daina zubawa rauni gishiri." Zuciya ce take cinsa, bai saurare shi ba haka ya fita can ihun Khamis muka ji, baki
aya muka fito wajen.

Aka yi juyin duniyar nan ya sake Khamis amma fir yaki, sai da nace mishi.

"Don Allah ka kyale shi mana!" Ture shi yayi ya juya tare da damkar hannuna.

Har office dinsa ya kai ni, tare da cewa.

"Daga yau ki tsaya a inda ake sauke ki na gaya miki!" Ya daka min tsawa, shiru nayi tare da rufe idanuna, haka ya fita ya bar ni kamar mayya a office
insa, shigowa mutumin da suka tawo tare yayi ya zuba min harara ya daka min tsawa.

"Wacece ke?

Me yasa saboda ke yake abinda bai ta
a yi ba!?" Kuka ne ya zo min dai-dai lokacin da ya shigo office, "Tambayar ki nake ba kuka nace ki min ba!" Ya daka min tsawa, "Malam ya isheka haka, ya ishe ka nace!" Ya fada a masifance.

"Bai isa ba Turaki nima zaka dake ni ne kamar yadda ka dake shi, wace ce ita da kake fada akanta?" Ture mutumin yayi har waje.

"Kada na kara ganinka a inda nake!" Daga haka ya rufe kofar.

Ai kuwa nima ya juya ya fara min fada tare da cewa na zo ina juya jikina har maza na kai min yadda yake fadar kamar ya rufe ni da duka, sannan ya koro ni waje tare da kiran Taj ya zo ya kawo min aikin, nasha kuka kamar an yi min mutuwa sannan na cigaba da aikin kamar jaka, na jiya ban gama ba, yau aka kara kawo min wani aikin, jikina har ciwo yake abinci kuwa taj ya kawo min faten wake da soyayyar agada, naci sai ruwan tea, wurin karfe biyu ya fito cikin fararen kaya, da hular da ya karya, sau daya na kalle shi na cigaba da abinda nake yi.

Shigowar wasu yan mata na family
insu, ya sani mikewa nace musu.

"Sannunku da zuwa, da mai za a taimaka muku?" "Mun zo miki kashedi ne ki fita harkan hamma Turaki!" Kallonsu nake kafin na ce musu." Ayi hakuri ba zan kara shiga harkansa ba!" " Aiki kika zo nan, ba shige mishi ba!" Yadda suka yi ta min maganar banza ni dai ban ce musu kome ba, sai can na ce musu.

" Mr Turaki ya saka cctv idan kuka matsa dayawa zai dauki mataki!

" Na nuna musu, wurin da camera din yake, sai suka fara baya Baya.

Bar suka fita, bayan ya dawo na tattara takardun na kai mishi, ya duba sannan ya watsa min a fuska ya ce min.

" Ki gyara basu yi min yadda nake so ba!" " Tow" na kwashe, haka na dawo na zauna karfin hali nake amma ni daya nasan yadda nake ji da ciwon ciki amma mutumin nan ya kara dawo min da aiki ba.

Hawaye ne ya zubo min, haka na kara zama na fara sabon aiki karshe ya fita abinsa, shigowa Taj yazo ya amshi aikin yana taya ni, ni kuma na zauna ina hutawa, muka yi ta hira da Taj har ya gama min aikin ya ce min.

"Aikin na da wahala amma a madadin sai kin sake type kawai copy and paste zaki yi." " K
amar ya?

" Na tambaye shi, ina sani.

Mikewa nayi kafin ya bani amsa na wuce ban dakin da aka nuna min, na gyara jikina.

Ina dawowa na samu baya nan, sai Masifaffen nan ne a tsaye, " aiki kika zo ko yawo?" Kasa magana nayi ina kasa domin kwarjini ne da shi, baka iya tsayawa ka kare mishi kallo.

Kamar nayi kuka haka na wuce bakina yana rawa nace mishi." Toilet!

Banza ya bawa ajiyata yayi gaba abinsa, takaici ne ya kama na cigaba aiki har karfe biyar da rabi, na mike zan hada kayan fitowa yayi fuskarshi a ha
e yayi tare da kafe ni da idanu, diriricewa nayi na fara niman inda zan tsaya kawai sai na koma na zauna, ba magana ba zagi amma wannan idanunsa masu kama da na dodanni, sun iya hukunta mutum.

Haka na cigaba da aiki har karfe shida ya wuce.

Ina wajen, ban san lokacin da hawaye ya fara zuba min ba.

Haka na cigaba da aikin ina kuka.

" Lubnah!

" Naji muryan Jasminah, d'ago kai nayi ina kallonta na fashe da kuka.

" Taso muje!" Haka na taso ina kuka, " ina zaki kaita?" " Bro lokacin tashi ya wuce fa, idan aikin ya mata yawa." " Koma ki cigaba da aikinki" haka na koma na zauna tare da cigaba da aiki ina shashekar kuka, ya juya ya banko mana kofar.

Ya cigaba da aikinsa, ina ta kallon wayata ko Ya Ado zai kira ni, amma bai kira itama Jasminah Yaranta suna ta kiranta, haka ta mike tana gaya musu.

"Gani nan zuwa!" Kallona tayi ta ce min.

"Hankalin Yaran ya tashi." Cikin dauriya nace mata.
Chapter 72 · 0% Book details