← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 86

Sashe 46

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bangaren Mama kuwa har zuwa tayi akan matsalar sai dai tana zuwa lagos, ganin yadda ta saka ni a gaba da maganar aure, ban ce mata kome na tafi makatanta na dawo, na same ra bata daina maganar auren nan ba, bata san yadda abin yake ba, ni dai ban san me ya faru ba, sai dai na bude idanuna na ganni a dogon kujeran parlourn, su Ya Ado suna ta min sannu, dakyar na tashi.

Rike hannuna Aunty Zakiyah tayi zuwa dakina Yara na kwanta, ta kawo min magani da tea na sha, yana fada min nayi sallah na zo n kwanta tuni barci yayi gaba da Ni, sai karfe daya na dare na farka a lokacin na samu tana kan abin sallah, tashi nayi na shiga ban daki nayi alwala na zo na gabtar da sallah Magariba da Isha, ina idarwa na daura da nafilla.

"Lubnah?" "Na'am!" Na kalle ta, yadda take kallona tausayi na take ji, haka yasa na matukar jin tausayin kaina.

"Tsoro kike ji ko!" Hawaye ne ya zubo min, ashe ta sani?

Ashe tasan ina jin tsoro; bude min hannu tayi na shiga ina wani irin kuka, "Ya isa haka ba zan kara miki maganar aure ba, ba xan kara cewa wani ya miki magana aure ba.

Jiya naji kamar na rasa ki kenan, ban san ashe haka abin yake ba.

Lubnah ko wani ne yace baya son abu ba zan mishi dole ba, balle ke da na yi miki laifi masu tarin yawa, ina jin idan baki yafe min ba Allah ba zai yafe min ba, " ni dai ina jikinta tare da jin wani dumi me dad'i, haka tayi ta rarrashina tana gaya min nayi hakuri da
addarata haka ta zo min, satinta uku, ta koma Bauchi ta bar mu da kewarta.

Haka na cigaba da rayuwata cikin yanci da walwala lokacin da na samu hutu kamar na je Bauchi, amma haka na hakura duk abinda zai hada ni da Hafiz ina kin sa, a zuwan Mama ne muka ji labarin ya
kai sadaki da kayan aure a can garin Mamansa.

Wai Abba ya sauya mishi gida, ni dai ban ce kala ba har suka gama hiransu.

Karshe barci nayi a parlourn ban san lokacin da suka gama hiran aka tashe ni na je na kwanta ba.

Bayan tafiyar Mama na sha hutu na koma school.

Shekara daya da wasu watanni a lagos wnada yayi daidai da wata na bakwai da fara karatu, haka yasa na kara nutsuwa zuwa yanzu karatun shine mijina da duniyata, course mate dina tun suna kirana silver spoon saboda sun gano nice aka musu kashedi akai, suka yi ta min tsiya da tafiya tayi nisa sai suka watsar da makamansu suka kuma janyo ni muka zaka Family, duk yadda zaka so ka kebe da ni na shata layi ba ruwana da soyayya, tsoron maganar namiji nake, department dinmu har sun gano tsoron mazan da nake ji, wani irin tsoron maza da nake ji duk abinda za ayi ayi na karatu amma bayan nan kana fara wani abu, xan fita harkanka.

Duk yadda kowa yaso yasan matsalata da maza ban tab'a magana ba, haka yasa suka kyale ni, na kuma kame kaina na saka a raina ba ruwana da duk wani dan balaja'u.

Haka kuwa muka kasance har muka kusan gama karatunmu, a lokacin ina da shekaru biyu cib a jahar lagos.

KUMO FAMILY MANSION.

Kallon Hajiya Khaulatu Daadah tayi cikin wani irin takaici take kallon yarta da son zuciya ya gama rufe masu idanu.

"Daddah ki bawa Alhaji hakuri wallahi Khamis ba zai kara ba, kuskuren fahimta aka samu!" Ta fada tana sunkuyar da kai kallonta Daddah tayi cike da mamaki da bakin ciki mara iyaka.

"Yake yaronki ce tayi laifi kin zo na saka baki na bawa ita baffanki hakuri Khamis ba zata sake ba." Murmushi tayi irin na manya, sannan ta cigaba da cin mutuncin Hajiya Khaulatu.

"Wato ita wancan Yaro Turaki da bata da kowa sai Allah, kika jifeta da shaidar zur, ita kuma Yaronki da take da Uwa da Uba ka zo kare shi saboda shi ne mai gata, ita wancan tana da waye?

Bata da kowa sai Allah.

Wai na tambaye ka Khaulatu me Yaron nan Aisha da yayunku suka muku da kuka tsane su haka?

Ni a sanina basu muku kome ba idan har akwai abinda zaku yi bai wuce tsayawa da Anne Aisha yayi a Kamfanin Alhaji ba, amma kun tsane shi tare da ita yar uwarku." Yadda Daddah take shiga ba nan take fita ba, karshe haka suka yi shiru ta kori Hajiya Khaulatu daga cikin gidan.

Wurin karfe uku na yamma Jasminah ta shigo cikin gidan, ta samu Uncle Auta da Hajiya Samirah.

" Barka dai datti!

" Yay gaida Alhaji ELYakub Kumo, sannan ta juya ga Hajiya Samirah ta ce mata..

"Aunty Barka dai ya kike?

Yasu Munawara da Abid?" "Lafiya lau Jasminah, kin leka Hajiya Zeenatu?" Yatsina fuska tayi tana kallon Daddah, "Daddah ya kike ?" " Kaci gidanku!

Da kazo ai baka gaishe ni ba sai yanzu zaka ce wai ya nake ba yadda nake ina shure-shure." "Allah ya baki hakuri!" Banza Daddah tayi mata, Alhaji ELYakub ya kalli Jasminah.

"Ina jinki!" Gyara zama tayi ta ce mishi.

"Gaskiya na gaji, tunda shi Turaki ba zai musu magana ba ya kamata a bani damar nayi magana tunda ina da hakkin akan kasona da yake cikin kamfanin!" Kallonta yayi yana murmushi ya ce mata.

"Turaki yayi magana ki ce ya fito da sonkai?

Ke kika ce Turaki yana nuna iko dayawa ko za a bada matsayin CEO baki amince a bashi ba, yanzu kuma ki dawo kina blaming
insa shi da ba a kasar yake ba.

" Yayi mata magana yana murmushi, baki
aya ta ji kamar ta nutse a wurin.

" Ita Turaki ta ce ba zata dawo ba, da irin wannan masfar da kuke yi gara kada ta dawo a sakata ta rame.

" Daddah ta fada tana hararansu.

" Yanzu dai me Jasminah take bukata haka kawai Jasminah bata zuwa akan abinda tasan waye a kai ba?" Shigo da tiren abincin Alhaji ELYakub, tuwon alkama ce miyar kuka wanda yaji kayan kamshi da hadi na musamman.

Ajiye tiren abincin Maid suka yi ta yi, har gaban Jasminah.

" Ina jin Jasminah?

" Alhaji ELYakub ya kara magana, yasan abinda ya kawo ta amma tunda ba zata yi magana ba shima shiru zai yi abinda ya fahimta shine ganin Samirah yasa tayi shiru taki magana, suna zaune a wurin har ya gama cin abincin, Uncle Auta ya shigo suka gaisa shine ma Ya kalli Samirah ya ce mata.

" Ya dai na ganki anan?

" " Yanzu zan tafi, amma Mujitafa me yasa Matarka da Matar Ubaid basu zo birthday din su Abid ba?" Ta fada tana wani hade rai ita nan an bata mata rai.

" Saboda basu fito daga babban zuri'a masu arziki irin naku ba, su zo anayi ta musu kallon banza da basu isa ba!

" Ya fada yana kallon Daddah da take gyada kai.

" Baffa barka da warhaka, Ubaid ya mika sakon wasu bayanai ga Turaki sauran kuma da a ji da shi, gaskiya Khamis yayi laifi dayawa sai dai yana da kyau a dawo da shi, domin ko babu kome yana lura da shashin tallace-tallace.

Amma na gayawa Turaki ya ce duk abinda aka gani shi dai na shi ya saka idanun ne kuma ya yayi bakin kokarinsa sauran na ku ne.

"
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 29
"Murmushi Alhaji ELYakub yayi ya nuna Uncle Auta ya ce mishi.

" Baka da kunya Mujitafa, wato sauran namu ne bayan kai ma kana da kaso a kamfanin!

" Dariya Uncle Auta yayi ya ce mishi.

" Ina ana babbakar giwa wa ke ta zomo, shi dai wancan magajin dubbanin nairori ya ji da kome ni a bar ni a dan aika!

" Anya kuwa?

Na fison ka taya shi riko tunda yaki kula maganar CEO shi baya kasan amma idanunsa yana kan kamfanin." "Cikakken shugaba kenan, baya tare damu amma idanunsa yana kan kome yasan shiga ya san fitar ku
i!" Jinjina kai Alhaji ELYakub yayi tare da gamsuwa da maganar Uncle Auta, ya ce mishi.

"Zenith bank sun kawo kayan wani dan kasuwa nayiwa Ubaid magana!" "Eh ya turo min dazun na kuma turawa Turakin amma bai ce kome ba!" "Alhamdulillahi mu jira mu ji me zai ce.

Amma ba zaka mishi magana ya dawo gida ba kenan?" " In sha Allah zai dawo, Baffa hukuncin ya isa haka yau shekara kusan daya da rabi da hukunta Khamis, duk da an biya kudin harajin ya kamata a sassauta mishi, Addah Khaulatu sai sintiri take tsakanin gidana da gidan Ubaid, ta amshi number Turaki yaki daukar kiranta, na tura mishi apologize letter da suka rubuta bai ce kome ba."
"Shi kenan Ubaid ya gaya min sannan itama Uwar Yaron tana ta bada hakuri, haka Abbas yana ta bada hakuri sai yadda Turaki ya ce ya cire hannunsa nake son ya hakura da kansa, tunda yace akwai mutanen da suke bayan Khamis shi ka
ai kudin yayi masa yawa, na rasa wnada ya karantar kimiyyar ha
a bama-bamai taya ya san kimiyyar shida da fitar ku
i har haka?

"
"Baffa Turaki rabin rayuwarsa yayi ta cikin turawa da larabawa ne, yasan makircin kowa, don haka kada ka yi mamaki don ya
an me yake faruwa a kamfanin da kuma yadda yasan yadda za ahada nukiliya da yadda yasan mutane na kaunar ku
i.

" Cikin gamsuwa da bayanin Uncle Auta ya ce mishi.

" Tabbas ya gaya min cewa kamar yadda nake son zuriarta ta zauna lafiya, ya ce Datti a cikin gidan akwai wnada zaman lafiya baya cikin tsarinsu, ya ce Datti ba wai ba zan dawo cikinku ba ne, kawai nafi son nesa da kune domin idan ina tare da ku, kullum sai na fito da sabon tsarin zaman lafiya, su ma kullum sai sun fito da tsarin tashin hankali." Inji Alhaji ELYakub ya fada yana dariya.

"Baffa sai kace mishi ya cancanci a bashi piece ambassador!

" Dariya suka yi sai a lokacin ya juya ga Jasminah ya ce mata.
Chapter 46 · 0% Book details