← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 86

Sashe 51

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan tana da past dinta Mai duhu sai na daura mata nawa labarin ta gane nima ban gina nan ba sai da nawa labarin, akwai mata victim irina da irinki, anan muke bude zuciyarmu, ki saki jikinki Adam ya gaya min kome ya kuma bukaci mu taimaka miki, idan har da gaske sauya kanki ke kanwata ce dole na baki special class domin bana son na hada ki da kome, na tuna lokacin da Babanmu ya rasu har kudin da aka biya na motar da zaa dawo damu Alhajinku ya biya mana hatta abincin da zamu ci na tsawon wata shida, kafin mu bar tsohon unguwarmu Alhajinku yana mana aika duk bayan wata shida, kayan abinci da sutura daga baya fitinar dangin Babanmu yasa muka bar unguwar, daga muka rasa taimakonsa.

Yau ga Lulu da na tafi na barta tana Yar shekara shida a gabana!" Murmushi nayi ta ce min.." zaku school ko?" " Karfe bakwai muke tashi idan kin taso sai ki zo ki amshi tips dinki!

" Godiya na mata sannan na bar office din, sau yawa mukan yi alkhairi ba tare da mun san zai dawo ko ya tafi ga mizaninmu, duk da abinda Abba yayi amma yau alkhairinsa da rokon marayu ya saka na samu nima wata alkhairin da shi ya aikata.

Murmushi nayi duk da laifinsa yau naji ina sonshi ina kewarsa.

Don haka da na shiga motar da zai kai ni makaranta, na fito da wayata ina kallon wayar number shi ne don ko na rasa number kowa bana iya manta number shi da Yadiko da Mama, haka nayi ta kallon wayar.

Har muka isa makaranta na biya kudin na fara tafiya, sai da na shiga makarantar sannan na samu wuri na zauna.

Da yake karfe daya zamu shiga class na kira Number Abba, haka wayar yayi ta ringing bai dauka ba, na sake kiran bai dauka ba, sai a karo na uku ya
auka.

"Waye ke kira haka?" Haka yayi ta magana na kasa magana sai hawayen da yake zuba min haka ya gaji ya kashe shi wayar, kuka nayi ta a wurin na rasa abinda yake min dad'i, sake kiran Mama nayi tana dauka na ce mata..

"Mama ina kewar Abba ina son ganin Abba Mama ina son Abbana, Mama ki koma wurin Abba ko don ni, Mama ina son Jin muryansa da farin ciki da annashuwa, amma na rasa Mama." Abinda ba zai tab'a sauya our Afrika mother, wato da ta danna min wani Ash'ar tare da zabga min warning idan na kara kiranta akan Abba sai ta ci Ubana sai na tsinci kaina da yin shiru, ban kara magana ba, kai na ga jidali da lukutar masifa, tass ta wanke ni kafin kuma ta sauko tana rashina, daga haka nayi shiru bayan mun gama waya sai ga kiran Aunty Innah ina gamawa Aunty Hindatu ta kira ni, sai ga Ya Umar da Tahir, ban gama nutsuwa sai ga Ya Ado.

Ina zaune a wurin ya kira ni na dauka ya tambaye ni ina aji ne?

Nace a'a gani a lambun makaranta bari na fito, har a lokacin kuka nake a hankali na dauki jakata na fita yana tsaye ina isa wurinsa na goma gefen da yake tsaye na kifa kaina a gefen hannusa ina kuka.

"Kina kewar Abba ko?" Jinjina kai nayi, kiranshi yayi bayan sun gama gaisawa ya ce mishi.

"Abba kai min wata alfarma daya?" "Ina jinka!" "Zaka yi magana da Lulu ne tana kewarka, gata nan." Kafin ya kara magana ya manna min wayar a kunnena, sai dai kuma nayi danasanin kiran Abba da Ya Ado ya min, Abba ya kara watsa min bakin fentin da ba zan tab'a mantwa da shi ba, sau gani ina wani irin hakki zuciyata, ta kasa
aukar mugayen kalmomin Abba, tun ina jin shi a tsaye a har na jingina da motar na zame kasa, domin kafana sun kasa
aukar nauyina, zuciyata ta gagara daukar maganar da Abba yake gaya min, wani irin nauyi na ji tare da bude bakina ina niman numfashi, fisge wayar Ya Ado yayi ya saka a kunnenshi ya ce mishi.

"In sha Allah ba zan kara kiranka akan Lubnah ba, ba zan kara ce maka ga ta ba, Abba idan ka yi sanadin mutuwar Lubnah Allah ba zai barka ba!" Kashe wayar yayi ya d'ago ni tare da saka ni a motar domin har an fara taruwa, ruwa wani dan ajin mu ya mika mishi yana fa
in.

"Bata tana bukatar ruwa!" Amsa yayi ya bude min ya kafa min na shanye, sannan aka kira class rep dinmu aka gaya mishi halin da nake ciki ya ce a je da ni gidan, da taimakon Allah na samu nutswa, daga haka na rufe idanuna, a hanya Ya Ado ya kira Mama ya gaya mata, halin da na shiga amma bai san me Abba ya gaya min ba, ai kuwa Mama kamar ta dirko ta wayar fada take yi kamar zata aro baki ta kara.

Kuma tayi alkawarin sai ta kunyata Abba shima kamar yadda ya min a gaban Jama'a domin ranta yayi mugun b'aci.....
(Kuna ganin mu bar Mama tayiwa Baban Bauchi tijara a bainar nasi?

Yes or no
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 33
Gida Ya ado ya kawo ni na kwanta, duk da bana jin barci amma na za
i nayi lumo.

Ina jin kamar na ni ba, taya mahaifin da ya haife ni zai tsane ni ya kira ni da karuwa?

Abba ya kira ni da karuwa!

Naki zaman aure na biyewa Adamu ya yanka min tikitin karuwanci a lagos, tow in sha Allah idan n kwaso kwanjamau sai dai na kare ni daya na domin suma guduna zasu yi.

Bude idanuna nayi tar ina kallon hannuna.

Wani irin sarawa kaina yayi kamar an hada karfe da karfe a hankali na ji abu yana zubewa daga hancina, ban kula ba sai da na ga zubar yayi yawa na tashi zaune ashe jini ne, yadda kaina yayi wani irin nauyi haka na koma na kwanta tare da lumshe idanuna, bana son karawa Ya Ado wani damuwar a hankali nayi ta ambaton Allah har na samu sauki na tashi zuwa ban daki na sakarwa kaina ruwan sanyi, can kuwa jinin ya tsaya, na jima a ban dakin na fito na sauya kaya.

Na sauko kasa ba kowa sai mai aiki haka na zauna a parlourn har lokacin sallah yayi na wuce nayi sallah na kwanta barci ya dauke ni.

Mama kuwa da suka gama waya, tashi tayi gaban wardrobe dinta, kayanta tayi ta sauko da shi, ta ciro wabujejen wando mai matu
ar girma kamar palazzo, ta saka ta dauko wani babban hijab dinta ta saka, sannan ta fito zuwa bangaren Umar ta bugawa matar gidan kofa da sauri aka bude tana ganin Mama ta ce mata.

"Mama ke ce?

Fita zaki yi?

Lafiya dai?" "Central zan je!" "Lafiya dai ko?

Ai da an gayawa Baban Nawwara ya miki ba sai kin je." "Yanzu xan dawo" ta juya ta fita yadda zuciyarta take tafasa idan ba tsinkawa Abba rigar mutunci tayi a idanun duniya ba, ba zata tab'a jin dadi ba.

Don haka ta nufi waje, tana fita matar Umar tana kiranshi, sai aka yi rashin dace ya shiga sallah, baya kusa da wayar ma.

Mama kuwa tana fita ta samu me keke napap, ta ce ya kaita Central ya fada mata kudin bata damu ba, ta ce su je.

Kawai yadda zata yiwa Abba rashin mutunci kawai take hasashe.

Duk da gudun da me Napep din yake amma Mama gani take kamar ba tafiya yake ba, kamar ta rufe shi da duka haka take ji, haka ya sauke wasu mata a unguwar Jaki, sannan ya fito ta masallacin Shehi dahiru Usman Bauchi, ya iso daidai office din Yan sanda na Central ya tsaya ta fita ta biya shi ku
insa,.

Sannan ta tsallaka cikin Central, sai da tayi tafiya sosai kafin ta isa layinsnu Baban Bauchi, an taru a kofar shagon ana cin abincin da ake kawowa kasuwa kullum daga gidan domin saukakawa Yaran shagon kashe kudin abincin.

"Usman Jama'are nazo wurinka ne?" Da mamaki kowa ya juya yana kallon Mama.

Wacce ta hade rai sosai kamar ba ita tayi maganar ba.

Da kamar ba zai kulata ba sai can ya ce mata.

"Ki je gida zan zo!" "Ba isa ba!

Ka gaya min yaushe ka ci maita da kake son kashe min Y'a?

Mai Lubabatu tayi maka da zafi har haka?" Shiru yayi kai dan kanzagi ya taso yana fa
in.

" Mama kasuwa ne nan don Allah ki yi!..." Tass Mama ta wanke shi da mari, ta kara wanke shi da mari sai da yayi baya kamar zai fadi, Baban Bauchi ya ce mata.

" Wacce irin hauka yake damunki?

" " Irin wanda kake dauke shi!

Irin wanda yake kanka, irin wanda ya saka ka yi fatali da zancen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, kowa Ni shugaba mai kiwo ne, kuma za a tambaye shi akan kiwonshi.

Gaya min kuskure ne don na kashe Auren Lubnah da wannan Tsinannen yaron da ya bata maganin hana haihuwa?

Laifine don ka kashe aurenta da azzalumin Yaron nan da ya nemi haukata min ita?

Me yasa Victims na mata yafi na maza yawa?

Me yasa?

Yau da Lubnah daukar wuka tayi ta soke shi wannan shagon ka rufe shi kenan saboda abin kunyar da tayi, amma daure ta yayi a cikin gidansa yana gana mata azaba, muka rufe idanunmu saboda zumunci!

Eh kalmar zumunci tana daga cikin sunayen Allah, gaya min me yasa ka saka min ita cikim Ukuba?

Yau ni Salamatu Galadima na zo gabanka da muryata da Muryan Y'ata, idan wani abu ya same ta.

Zan tabbatar da na tab'aka na kara tab'a ka sai na mai da kai zero plus zero yadda kowa sai ya yi tir da kai.

" Wani abokin shi ya ce mata.

" Hajiya don Allah ki yi hakuri a karasa a gida don Allah, anyi miki laifi muna rokon arziki a bar maganar nan!

" Ta kalli mutumin ta ce mishi.

" Alhaji Imarana!

Idan maita ce ni da shi Bismillah, idan kuma ina ganin babu maitar hali ce kawai Ni dashi shege ka fasa!
Chapter 51 · 0% Book details