← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 86

Sashe 49

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gaban wasu tika-tikan shagon sayar da atamfofin wasu yan mata ne suka zo fitar da Ashobe, yadda daya take wani yauki zaka
auka karkashi ce, tunda ya ga Hafiz take wani kashe murya, shima kuma ya fada mata domin yana masifar son mace yar gayu lokacin baya shi da Lubnah idan tayi gayu ba karamin tafiya da duk wani lissafinsa take ba, shi yana son mace mai gayu duk muninta, ko Lubnah abinda yasa shi ya daina ganin gayunta wannan shegen kibar da ta yi sanadin maganin hana daukar ciki da yayi ta bata, amma idan tayi kwalliya kamar ya boye ta yake ji, wannan kallon da yayiwa yarinyar ya dawo mishi da Lubnah haka yasa shi kallon zoben hannunsa.

Yana nazari da shaukin yadda zai hadu da Lubnah, duk ranar da suka hadu kuwa duk rintsi ba zai tab'a yarda ya barta ba, sai ya dawo da ita rayuwarshi tsamo-tsamo.......
(Hafiz kada ka ja min lukutar masifa don Allah
Innalillahi wainnalihir rajoun
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 31
Shi hala dole fa sai ya dawo da Lulu gidansa hankalinsa zai kwantar.

Daya daga cikin yaran shagon mai suna Ukasha ya ce mishi.

"Oga Ashobe suke suna son wannan atamfar kamar turmi hamsin." "A duba idan akwai a saka sunan Amaryan da Unguwar da suke." "Tow!" Ukasha ya samu Amaryan da kawayenta.

Daya daga cikin yan mata ta ce mishi.

"Babu ragi ne?

Muna son cotton da roba ne?" "Akai cotton 9k Akwai roba 5500 yake!" Juyawa Amaryan tayi ga wannan kawarta ta ce mata.

"Mansi kin ji kudin kayan yayi?" Wani juyawa yarinyar tayi cikin yauki da yanga ta ce mata.

"Duk yadda kika ce haka za ayi." Murmushi Amaryan tayi tana kallon Ukasha ta ce mishi " shi kenan ka gaya mishi muna so amma kuma.

" " Bari na mishi magana!

" Ita Mansi ta samu Hafiz cikin yanga tana mishi bayani, kallo daya yayi mata ya dauke kai yana fa
in.

" Ki bawa Ukasha number wayarku da za'a saka jikin kayan.

" Ya fita daga shagon, binsa tayi da idanu, duk wannan abin da take Baban Bauchi yana kasuwa duk iskanci da fitsaran Hafiz baya tab'a yarda ya gwada halinsa a gaban Baban Bauchi, domin ya iya takusan, Alwala suka yi tare da Baban Bauchi suka nufi masallacin da yake cikin kasuwar, amma a ransa ya kyasa da yarinyar addu'a yake yasa Ukasha ya amshi number yarinyar.

Nana yar uwarsa ce amma yau ganin Mansi ta fama mishi ciwon Lubnah tana budurwa yar shaf-shaf da ita ba kiba ba tarin tumbi, ga ta kamar ka goyata ka gudu da ita.

Don haka idan ya koma kafin a tashi sai ta amshi numberrta yarinyar ta matukar burge shi.

Don haka yana komawa ya dauki littafin da ake saka sunayen yan Ashobe ya gani sannan ya ajiye bai kuma bi ta kan zancen ba.

Bayan sun tashi Baban Bauchi da Hafiz suka wuce kasuwar wunti inda nan ma aka zuwa wasu kayan.

Sai da ya gama ganin yadda kome yake tafiya sannan suka fito tare a gidan ya sauke Baban Bauchi tunda ya dawo dutsen tanshi ya zama kamar driban Baban Bauchi.

Buga gidanshi yayi Nana tazo ta bude.

"Sannu da zuwa!" "Yawwa!" Ya shigo tana bin bayansa a parlourn ya samu Yusrah da Yasir suna cin abincin,, kallonshi suka yi ya wuce bai musu magana sai murmushin da ya musu.

Suka cigaba da cin abincin, har ya fito suka mike tare da cewa.

"Aunty Mun koshi!" "Sai kun cinye kullum haka kuke barina da abinci!" "Kyale su sun koshi ne, ba ayiwa yaro dole ya ci abinci." Cikin mita ta ce mishi "shi kenan kana son ka bar ni da abinci." Haka ta saka yaran a gaba suka wanke hannu suka tafi dakinsu, suka kwanta. uban ya gama abinda yake ya fita.
------
Tunda ya sauke Baban Bauchi ya ce mishi.

"Jeka yau naga yaran nan ne a gidan zuwa an jima ka dawo ina son mu magana." Gyada kai yayi yana fa
in..

"tow shi kenan!" Ya juya zuwa gidanshi, babban damuwar Hafiz ya san me yake faruwa a cikin gidan yadda yaga motar Umar da ya sauya wata Jeep Cherokee Ave, shi fa Umar tun da ya bar shagon Baban Bauchi Allah ya ha
a shi da wani Imyamuri suka fara sana'ar mashina sai gashi Allah ya yi sanadin mutumin nan hanyar arzikinsa yake, haka yasa kome ya tab'a yake da albarka.

Dalilin zuwan su kuwa bikin Ya Sani da bude shagon shi na sayar da kayan maza a winti na biyu yana saro agogo da wayoyin zamani a China, kusan shekarar biyu kenan ya fara da sayar da takalma ne, sai ya fara gwada dinka kaya yana sakawa tare da daura hoton a IG da Twitter, Allah da ikonsa da buwayarsa kasancewar Uwa tana tare da da shi, yan uwansa kuwa masu hadin kai ne, sai gashi cikin buqatar mai kowa da kome ya bunkasa ya isa inda ba a zata ba, yanzu haka yana iya dinkawa ango kayan fitar biki, don bikin da aka yi kwanan nan dan gwamna Bauchi state, shi yayi ta kula da shiga da fitar angwayen, ba karamin kudi ya samu ba.

Dama yana taru wurin Aunty Hindatu, ai kuwa ganin haka ya samu kudi aka kara mishi ya sake habbaka kayan auren, da sadakinsa da kome na shi, yana nan a hannu yanzu sun zo ne a gayawa Baban Bauchi shirinsa.

Shine ya gayyaci yan uwansa.

Bayan sallah isha, suka hadu a parlourn Baban, suka gaisa aka yi yan hira sama-sama, kafin Umar ya kawo zancen da ya ha
a su.

Daidai shigowar Hafiz da ya koma gefen Baban Bauchi ya zauna kamar zai koma cikinsa tsabar munafunci, ran Tahir ya b'aci.

Shiru baban Bauchi yayi kafin ya ce musu.

"Tow Allah ya nuna mana, amma naso da zaku amince da Firdausi, domin naga ai yarinyar itama." "Abba Yarinyar da yake so ba jiya suka hadu ba, ba yau ba akala sun kai shekaru hudu suna tare, don tun tana makaranta suka hadu, yanzu kuma sai a kawo wani batu Firdausin da." "Tunda kun shirya mishi yadda zai me yasa zaka kawo min batun amincewata." Yadiko da take bakin kofa ta ce mishi.

" Ai kasan kuwa yadda ka hana Sani zaman shagonka wallahi ba ka da hurumin bashi abinda baya so, Lubnah ma da ya ta kwashe a hannun Hafiz kai ku tashi idan yaso kada ya bashi kwandala yarona ya yi duk wani abinda ya dace wa kansa ko ni da na haife shi bai jira ni ba, haka kuwa ba wanda zai mishi dole!"
Wani irin rikici aka shiga tukawa aka kuncewa, kafin kuma aka kyale kowa yayi yadda ya so, Baban Jama'are ya zo da wasu maza , wanda suke dangin Yadiko aka je nimawa Sani auren Halisah, yarinyar danginta yan Tilde ne, don haka suka tafi aka nima mishi aurenta, ganin yadda suka fito daga babban zuri'a kuma yaro yana da abin yi sannan shima Uban yarinyar ya shirya tsaf, kawai aka karbi sadaki da yanke rana.

Wannan lamarin yayiwa kowa dad'i domin domin kuwa dangi kowa ya fara shiri.

An saka ranar bikin wata uku masu zuwa, a cikin wata ukun gidan da Abban ya bashi wanda yake kusa da gidan Ya Umar, aka fara gyarawa ana cire tsohon tsarin gidan, aka fara yin gyaran na zamani.

Cikin kasa da wata guda da sati biyu aka gama gyaran gidan.

Ashobe kuwa a shagon Aminu da Zubairu, Innah ta cire aka kai dinki na su Lubnah domin Mama ta ce dole ta zo.

Lubnah.

Bikin sani zai zo lokacin mun gama jarabawa, sai dai har zuwa lokacin gabana yana faduwa da maganar zuwa Bauchi.

Domin gani nake kamar duk wani abu zai kara faruwa, haka na sake raina na cigaba da abinda yake gabana.

Duk da na dan sauka ka
an, amma kuma ni kaina sai nake ga kamar da sauran yanayin domin jikina yana min nauyi, wani lokaci haka zan ta fama da haki, sau biyu ina zuwa ganin likita da Dijah Bala take hada ni da su, na farko ya ce kitse ne ya taru a zuciyata, na biyu kuma yace wai a cikina sai abin ya saka ni rud'ani, na shiga cikin wani irin tashin hankalin mara misaltuwa nayi shiga, na rasa me ke min dad'i.

Ban gaya Ya Ado ba, don yana gayawa Mama zata iya cewa ayi aikin yaushe aka cire min karin mahaifa yanzu kuma wani aikin ni na koma kamar wata kazar mayu, ga shi na daina ganin Baby sai kaina yayi zafi,, ranar wata Alhamis na tafi wurin Dr Dijah Bala.

Ta kalle ni a hankali, tana fa
in..

"Ni na ga kamar kina cikin damuwa?" Jinjina kai nayi a hankali ina wasa da yatsun hannunta.

" Me yake damunki?

" Gyara zama nayi na rasa yadda xan yi magana domin har yau bani da kwarin gwiwa yin dogon magana a gaban jama'a, duk da tana kokarin nuna maka kai ma mutum ne kana da damar fadar abinda yake ranka.

Matse hannuna nayi ina motsa bakina nace mata.

"Nan da wata biyu za muje Bauchi bikin Yayana!" Murmushi tayi tana kallon yadda na matse hannuna da
arfi.

Na kasa fada mata abinda nake son fada, go
gewa da tayi da masu irin laluranmu yasa ta matso da kujeran kusa da ni ta rike hannuna da kyau, "ina tsoron kada Abba ya ce ki koma gidan Hafiz ko?" Hawayen da nake dannewa ne suka shiga wasan tsare akan fuskana.

Cikin shashekar kuka na ce mata."ba iya shi ba ina tsoron abinda mutane zasu ce ne." Nan ma nayi shiru ina kallon gefe, jinjina kai take a hankali ta ce min.

"Mutane sun daina maganar kina da kiba ne?" Da sauri na d'ago kai ina girgiza mata.

"Ashe kuwa tunda basu daina ba, akan me zaki yi kuka?

A yanzu Mama da su Barista suna tare da ke, tare da su Innah da Hindatu.

Kina jin zasu bari a mai dake gidansa ne?

Kada ki manta har yau baki yarda da kanki ba ne.
Chapter 49 · 0% Book details