← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 86

Sashe 70

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin kusan ganye nace a saka min sai kifi da Dan wake ka
an, sannan na dawo na zauna.

Haka muka fara cin abinci, ji nayi kamar abu me sanyi yana tsara jikina ashe ruwan sanyi ake zuba min, ni kamar na santa.

" Karuwa baki
aya kin makale mishi, kina abu kamar baki san kome ba idan baki kyale shi ba sai na saka an kashe min ke jaka wawuya mummuna baka katuwa!" Ji nayi kunya ta kama ni kamar na nutse a wurin, " Badr meye haka?" Inji Mamar Yaran nan.

" Amma kin san duk wani abu idan na Brother Turaki ne yana da muhimmanci ko?

Ita din sabuwar sakatariyarsa ce, sai ki san yadda zaki mishi bayani ya fahimta." Sai a lokacin tsoro da kunya ya kamata Driban da naji matar ta ce mishi.." Taj baka gaya musu replace Mrs Thomas tayi ba ne?"
"Ma na gaya musu na kai musu a rubuce basu dauka da muhimmanci ba ne!" Riko hannuna tayi Mamar yaran zuwa office dinta, a hanya muka hadu da shi, bai mana magana ba, itama bata mishi ba.. office dinta muka je ta bani kayan da na saka nawa kuma ta kai wani daki ta baza min shi.

"Zauna!" "Na gode!" Murmushi tayi tana fa
in.

"Sunana Jasminah ni kanwar Brother Turaki ce, mu biyu muka rage a cikin mu shida.

Iyayenmu sun rasu." Yadda take bani labarin sama sama yasa na dan ji ta bani tausayi.

Buga kofar aka yi ta ce a shigo Taj ne ya zo da paper Bag ya mika min.

"Ki sauya kayan!" "Na gode na riga da na sauya ai." Amsa tayi tana fa
in.

"Mun gode" ta amsa tare da mika min," yace Idan kin gama akwai aiki da abubuwan da za ayi gobe!

" Mikewa nayi na bi bayan shi, ban jira ta cewar ta ba, muka nufi sama muna hira har muka isa office
insa.

Da dariya a fuskarmu muka isa.

Da harshen yarbanci yayiwa Taj magana da sauri ya fara fa
in.." am sorry sir!" Hakuri yayi ta badawa.

Fita yayi ya bar ni a office din ni
aya.

Wato da mutumin nan yayi ta min fada da masifa tare da nunawa ban san aikina ba, nazo sai dariya nake kamar wata shashasha, mutumin nan ya ci mutuncina.

Haka na sunkuyar dakai nayi ta kuka.

Cikin kalmomin da basu wuce a kirga ba ya ce min.

"Zan kore ki." Haka nayi ta bashi hakuri, karshe na fita.

Koda na fito waje stair na biyo a hankali nake tafiya ina kuka.

Sai da na sha kukana sannan na koma can staff office na dauki kayana sai kallona ake na nufi office din Aunty Jasmin na dauki kayana.

"Me ya same ki Mrs Jama'are!" Kasa magana nayi sai kuka nake, a lokacin ya shigo ni kuma na dauki kayana zan fita ta ce min..

"Wannan fa!" "Na gode na jikina ma ya ishe ni!" Na wuce shi zan fita.

"Koma ki dauki kayan!" Kamar wanda ya dasa ni haka na tsaya cak kafin wata zuciya ta ce koma ki
auka, ba musu na koma na dauka na fita daga office din.

"Brother me tayi maka?" Wani ha
e rai yayi ya fara muzurai kamar Wadda aka mishi karya.

Haka na fito na dawo gidan ban yarda wani ya fahimci yadda nake ki ba, washi gari ya kama Alhamis, kamar ba zan je ba don karfe takwas na isa.

Sai gulmar da ake yi naga sauran mala'ikan nayi, karar aka aiki a can sama yasa nayi mamaki me ya samu saman kuma?

Staff office na shiga na ajiye kayana a locker na, sannan na rufe na fito ina mai nufar sama office din Jasminah na fara zuwa na ajiye mata kayan sannan na fito, kafin na haura ma uban yan masifa, na ga kofar shi aka cire aka saka na glass sai wajen ana ta ha
a karamin parlourn da office ne, wurin yayi kyau sosai.

Juyowa nayi na sauko kasa ina jin kamar yau na koma gida, haka na zauna har wurin karfe goma saura sannan na sauko da sautin.

Ashe da na zauna abina a sama domin ina saukowa na hadu da bala'i fada yake tare da koran ma'aikata gudu biyu, sai kuka suke suna rokonshi da yayi hakuri.

A hankali na sulale daga wurin ina zan iya masifar wannan boss din.

Taj yana ganina ya kwala min kira dole na juya haka na je na amshi jakar masifaffen can.

Muna haurawa na samu har an gama aikin, abin ya bani mamaki yaushe na zo har an gama.

Office dinsa muka shiga Taj ya ce min.

"An yi miki office dinki na wajen nan, nan zaki zauna ke daya babu yawo babu fita ko ina, akwai toilet a can gaba ka
an.

Duk abinda zaki yi kama daga sallah zuwa wani abu ba sai kin fita ba, abinci xan na kawo miki." Yadda yake bayanin saura kiris na kware.

Wannan wacce irin takura ne?

Muryanshi ce ta dawo ni daga duniyar tunanin.

"Zaki cigaba da aiki daga nan ban da sauka kasa." Ban san yadda aka yi maganar ta kwace a bakina ba, sai da na rike bakina.

"Amma wannan bauta ce ba aiki..." Yadda suka zuba min idanu, nayi maza na rufe bakina, da sauri na fita.

Sai yayi kamar bai ji ba, shima Taj din kamar bai ji ba aka bar maganar.

Wunin ranar baki muka yi daya office dinsa zuwa kasa, ni da shi mun sauka ya fi sau goma, kafin na dawo nayi sallah naci abinci, ina gamawa Taj ya kawo min laptop kiran kamfanin Dellu ya ajiye min, ya kara min da table tap, sai takardu da printing machine.

"Ranki shi dade daga ko ina zaki amshi sakon kuma zaki yi printing dinsa ki tura, bari na nuna miki." Haka ya shiga nuna min ina tambayar shi yana bani amsa kamar an ce in d'ago kai, masufaffen mutumin nan ne a tsaye a bakin kofar, da sauri na sunkuyar da kaina..

"wannan anya kanshi daya?" Na tambayi kaina ko da mq d'ago baya nan, sai sake wani irin net yayi a jikin kofar.. ajiyar zuciya na sauke.

"Idan aka tashi zaki tafi da kayanki ba zaki bar ko daya ba." Gyada kai nayi, yana gamawa ya bar ni, kamar mayya wata yar wayar da aka saka a wurin yayi kara dauka nayi nace..

"Hello!" "Akwai baki yallabai yasan da zuwansu ne?" "Ok rike wayar!" Na ce sannan na tashi na isa bakin kofar na buga ya ce ma shiga, ina shiga na ce mishi.

"Sir kasan da zuwan baki ne?" Bai amsa min ba, wannan mutumin dan girman kai ne, tsayuwa na cigaba da yi, can ya ce min.

"Ki duba tap dinki!" Da sauri na fita na duba, daukar wayar nayi na ce mata.

" A kai su dakin tattaunawa gashi nan zuwa!" Na koma na gaya mishi suna jiranshi, kamar ya mangare Ni, haka na biyo bayanshi da laptop dinsa.

A meet room din har da wannan Khamis din, nan aka yi meeting din ina zaune a next na Masifaffen.

Ana gama meeting din Khamis ya zo ya zauna yana mai juya kujerar da nake kai yana fa
in.

"Idan kina da wata matsala ina wancan tsohon side din ki zo!" Yadda Masifaffen ya mike haka nima na mike, tare da bin bayansa.

Sai ji nayi mutumin nan ya kai min mari a mazaunai na, yana fa
in.

"You too hot baby!" Wani irin abu naji ya zo min wuya kamar yadda Masifaffen ya tsaya cak haka na juya tare da kifa mishi mari, sai da ya zauna..

"Koda nazo aiki ni ha kazama ba ce." "Muje!" Haka ya ce ,tare da matsa min na fita ya juya ga Khamis.

" Kayi hauka ne?

Ko an gaya maka kowacce mace kazama ce!

" Daga haka ya bar shi nan da ciwon baki.

Tun kafin mu tashi taj ya gaya min oga zai yi tafiya Abuja, tare da shi ni gobe ba sai na zo ba, tafiyar zata dauki kwanaki uku zuwa hudu ranar Laraba zan zo wurin aikin kenan, wayyo dad'i kamar na zuba ruwa na sha.

Haka muka tashi na hada kome nawa, har lokacin Masifaffen yana office, hala jira yake na je na tattara mishi kayansa Kamar yadda na fada a raina haka ne fa, shiga nayi na hada mishi kayansa yana zaune, ina gamawa Taj yana shigowa na mika mishi.

Ni dai da muka fito motar ma'aikata na shiga, ya kawo ni Garej, sannan na wuce gida.

Wannan marin da Lubnah tayiwa Khamis, ya janyo rigima da meeting.

Da aka zauna ya ce ba zai zo ba tafiya ne gaban shi, ai kuwa abin ya bakanta ran Alhaji Abbas da Alhaji Mudansir, lokacin da Uncle yake music bayanin rashin mutunci da Khamis yayi karyawa suka yi tare da cewa.

"Khamis me zai yi da low background irinta, idan lalata yan mata yake ba ga yan matan da suka fita haduwa a gari ba...." Yadda suke jaraba da masifa kamar an yanki namar fuskarshi.

Haka suka kai
ara wurin Alhaji ELYakub ya zuba musu idanu ya ce a jira Turaki ya dawo sai ayi magana.

Tunda abu ne na bangaren biyu zuwa uku sai aji uku waye mai gaskiya.

Abin ai ba na fada bane, nan ma suka yi ta mita.

Wani abu da suka kasa ganewa akan Turaki Alhaji ELYakub bai da hakuri kuma baya karban maganar kowa haka yasa suka yi ta jin haushi da mitar an ki amsar Maganarsu kome ya faru Turaki ne mai Gaskiya, ba su ba.....
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 49
*Anya kuna fahimtar tafiyar nan kuwa?*
Rigima taki ci ta ki cinya, domin kuwa Hajiya Sameerah ta saka a ranta sai an kori yarinyar da ta kwatsamawa danta mari, haka shima Kawun Khamis sun mai da al'amarin babban al'amari, wannan abin da suka ta yi yasa Alhaji ELYakub ya kira Turaki lallai yana son ganinshi, duk da yasan baya gari amma ya mishi al
awarin yana dawowa zai shigo.

Ranakun da nayi a gida, sai nake jin kaina kamar wata mai yanci.
Chapter 70 · 0% Book details