← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 86

Sashe 40

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni mace nake so da zata so ni ba tare da tasan who am I, kada ka je ina ji a jikina ita din mahadar rayuwata ce."
Duk da yan matan da suke hauka da fada da dambe akanshi, haka bai ta
a burge shi ko jin a ransa suna kan daidai ko sau daya basa gabanshi.

Hajiya Khaulatu tana da Yara biyu, Khamis da Khamis baya jin magana, niman mata shaye-shaye, fadar area ta dabba.

Duk wani iskanci ya kare a gindin Khamis sai yar su ta biyu Badar tare da Alhaji Abbas, wacce take zaman jiran Bilal, don tace sai dai ta mutu bata yi aure ba.

Mimi yar wurin Hajiya Zeenatu tsohuwar matar Haris, bayan rasuwarsa aka hada auren da Alhaji Mudansir ELYakub, bayan Jasminah ta haifi Mimi Fatimah, ita bata damu da wani soyayya ba, don ita ce asalin Queen of Kumo Family, ana ji da ita.

Zaheeda, yar gidan Hajiya Samirah itama tana son Bilal, don ita har inda yake ta je mishi.

Badar kuwa a gidansa da yake Lekki take zaune.

Sai Nasmat wacce take nan lagos a gidan Uncle Auta, shima Uncle Auta da yake da Iyali Yaranshi maza hudu ne, kuma kanana ne, Yakub wanda suke kiranshi da Amir, sai Harisu wanda suke kiranshi da Akhi, sai Jibrin wanda suke kira da Aalim.

Kaf duniya daga Ubaid sai Uncle Auta suka san meye Turaki yake so, me yake bukata ja'iri bai da alkibla, akwai wani zuwan da Turaki yayi lokacin Alhaji ELYakub bai da lafiya an dauka mutuwa ma zai yi aka gaya mishi, zuwan da yayi ya tashi wani tashin hankalin da ba taba gani ba, domin ya zo gidan duk babu kowa a gidan domin bai gaya musu yana hanya ba, a lokacin da ya iso gidan domin drop ya dauka har gida, da farko security din basu gane shi ba, domin shigar da yayi sai da ya cire facemask dinsa suka gane shi ne, haka ya shiga gidan akwai wata yar mota da take kai mutane har cikin gidan, ita ya shiga aka kawo shi, zuwan da yayi ya shiga bangaren Daddah anan ya samu Mimi tana yiwa Daddah barna, shi kuwa ya kamata ya zane ta, karshe ya rufe part din Daddah ya tawo asibitin, ana ta murnan ganinsa sai ga kira daga gidan, aka kira Hajiya Zeenatu tana isa gidan ta ga abinda yayiwa Yarta, ai kuwa ta kawo yarinyar, jin haushi da kishin yadda aka wani zagaye shi ta saka hannu a kai tana kuka wai yayiwa Yarta fyade.

Wannan abin ya daki Turaki.

Kiri-kiri Badar tace mata.

"Karya kike Maman Mimi!" Da yake yaran a sangarce suke ba wanda ya kwabe ta.

Case
in sai da aka hura shi ya zama babban al'amari, hankalinsu ya kwanta Alhaji ELYakub yana ji yace su bar mishi gidansa, bai lalata na wasu ba, zuriarsa ba zasu lalata nasu ba.

A lokacin Turaki yayi fushi ya bar musu kasar, suna son ya dawo ko don yanzu a raba matsayi a kamfanin KUMO properties nigeria agency, amma yaki dawowa, yaki yin wani motsi su kansu basu san inda yake ba, idan ka cire Uncle Auta da Ubaid, babu wanda zai baka labarin inda Turaki ya
Ita kuwa Daddah cewa take aljanun sun aure mata jika domin yaki maganar aure, ko irin kiranshi Uncle Auta yayi haka zata gama surutunta baya ce mata cikanki, har mamaki yake yadda bai damu da magana ba, sam shi magana tafi kome bashi wahala.

Don da yayi magana gara ya shiga daki ya kwana ya wuni.

Shi har mamaki yake idan ya ga mutane na magana, idan da zai yi magana tow abun da zai magana a kai me muhimmanci ne.
***
Lulu.

Na samu wata biyu, ina zuwa wurin Mrs Dije Bala, sannan gefe daya ya ha
a min wani tables na abincin da nake ci, domin maganin da haifi yake bani sun yi sanadin da kitse da uric acid ya taru min, haka yasa nake samun wani irin gajiya.

A hankali nake bin kome, kullum haka zan tafi wurinta na dawo.

Ya Hafiz yaso kashe ni ne, Allah bai nufa ba.

A hankali na dan fara samun nutsuwa, ina cika wata uku na gama iddana, a lokacin naji kamar na samu yanci, har da wannan iddar ya saka min traumatic domin gani nake kamar Ya Hafiz zai iya cewa ya dawo da ni, a wurin da nake zuwa akwai Reheb, a nan idan na je naji matsalar wasu ashe ni nawa mai sauki ne, domin gashi wasu yaran masu ku
i ne wasu matan masu ku
i amma rayuwarsu ta lalace, akwai wata yarinyar da muka hadu sunanta Baby Mahaifiyarta yar Jos ce, mahaifinta kuma bayarabe amma gata yasa ta lalace, sai gashi ta samu miji shi ya kawo ta wurin Dr Dijah Bala, yarinyar tana da saurin sabo, duk yadda naso na ki biye mata, haka take makale min.

A bangaren Ya Ado abokan aikinsa har mutum uku suna niman izinin aurena, ce musu yayi su yi hakuri har yanzu Lubnah she still small girl...
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 24
Wannan kalaman ya saka aka shafa min lafiya, tabbas ina bukatar spaces sosai Ina bukatar nutsuwa wanda zai saka naji nima mutum ce kamar kowa, ina bukatar farin ciki da nutswa amma ta ya?

Ta hanyar bani duk wani tazara da zata saka ni farin ciki, a hankali rayuwata ta mike, har watan azumi ya zo farkon watan azumin Ya Ado ya mana albishir da zuwa Umara a can zamu yi sallah, Yadiko Abba ya biya mata da ita da shi, Mama kuma Ya Ado ya hada mu ita xata tashi ta Bauchi, mu kuma ta lagos, wani abu da ya kara d'aga min hankali wannan kibar yana damuwa duk yadda nake son rage shi kamar kara shi nake, haka yasa Doctor Ahmad ya hada ni da wani likita anan lagos a cikin wata azumin kafin mu tafi Umara, lokacin da na ga likitan, ya sake tsara min abinci sannan ya hana ni shan kowani magani da zai saka ni nayi slimming domin na fara shan wasu ganyen shayi, ya hana ni.

Kamar da wasa na fara shan kiyayye maganin da yanayin, sai dai kuma ko ana gobe zamu Umara, sai da ciwon ciki ya taso min, haka nayi ta daurewa har muka tafi umara a can kuwa kasa mai tsarkin na fadi na suma haka aka tafi da ni asibiti hankali a tashe, lokacin da aka min test anan aka hango cutar fabroid a cikin mahaifana manya guda biyu sune suka hura min tumbina, suka ce aiki nake bukata, Ya ado yace su bani magani da abinda zasu bani kawai mu koma gida ayi min domin bai zo da shirin aikin ba.

Lokacin da ya samu Mama da yadda suka yi da likitan, ta ce mishi.

"Wani ba a shirya ba kuma?

Kawai mata aikin na hakura guzurin yanzu akwai abinda za a bukata a rayuwar lubnah nace babu shi?

Ayi aikin Allah ya bata lafiya kowa rai ya amfana baya ga mai shi ne, ni yanzu bata kaina nake ji ba, ta ita nake ji"
Haka aka yi min aiki a washi gari ranar da aka kai azumi ashirin da uku.

An cire tare da kashe wa
anda suka fara zuba karin, sannan aka fito da ni.

Yayuna a Bauchi kamar su tawo, don sun tabbatar zasu zo Lagos ganina.

Sai nake jin kamar ni daya nafi kowa gata, daren ashirin da uku ake ta saka ran alamun laylatu kadr, yadda ake pretending din yanayin sai bai kasance a wannan daren ba, aka wuce zuwa daren 27, wanda tun wunin ranar Mama da take kula da ni take addu'a nima kuwa Addua nake, karshe Mama kasa hakuri tayi ta saka aka bamu keken mara lafiya muka wuce harami, ranar na ga gundarin kauna a wurin mahaifiyata, mantawa da kanta tayi tana zagaya da ni Ka'aba tana "Allah ga Lubabatuna, Allah ka bata duk abinda ta rasa a baya, Ya Allah ka bata miji na gari.

" Sai da naji kamar buga min guduma tayi domin gabana ne ya fadi.

Tsoron maza ya kara shiga zuciyata.

Haka take addu'a miji na gari har wasu yan Nigeria da Nijar suka yi ta mara dariya, wai tana ta addu'a kamar ita
aya ta haifa murmushi take kawai ta ce musu, da kun san irin Izayar da na mata zaku ce ta cancanci haka.

Wannan ranar Mama bata mai da ni asibiti na har aka Sha ruwa, ta mai da ni, sannan ta dawo harami yin sallah tahajju.

Asibitin kuwa ana tasowa sai ga Yadiko da su Ya Ado, da Yaran da Aunty Zakiyah, ai kuwa na ji dadi murmushi nake idan suna hira, haka suka yi sahur bayan sun gama suka tafi masallaci, nima a nan nayi sallah bayan sun dawo, Mama ta koma ma sauki ni kuma aka barni Asibitin.

Ai kuwa Yadiko suka yi fada da Abba ya ce ta nime abokin tafiyarta ta ce mishi..

"da yake makauniya ka kawo ba." Rigima fa wai akan me tazo duba ni, haka ta fada mana da tazo ni dai umarana ta bana a gadon asibiti nayi shi, ranar ya kasance juma'a, don haka nima an fitar da ni domin ita ce Juma'a ta karshe, ranar Litinin ake saka ran karamar sallah, haka yasa aka fitar da ni.

Nayi addu'a Ubangiji ya kawo min nutsuwa da kwanciyar hankali, Ubangiji ya bani kwarin gwiwa, Ubangiji ya cire min tsoron wani abokin halitta a raina, na roki Allah ya mantar da ni rayuwar baya.

Ya saka min hakuri da dangana.

Ganina a dakin Ka'aba ya saka min yarda da cewa Ubangiji yana nan yana jina, shi din rayayyen nan ne da baya mutuwa, bai haifa ba, ba haife shi ba.

Sai nayi kukan farin ciki ya saukar min wani nutsuwa na musamman.

Naji nauyi da zafin da nake ji yana sauka a raina, na ji farin ciki da rabona da naji shi tun ina JIBWIS, a ranar Mama sai da suka yi magana da su Aunty Zakiyah wai sun ga kamar ba ni, haka muka yi ta ibada, har ranar sallah.

Wayyo yadda kowa yayi wanka sallah amma ni ba hali saboda dinkina.
Chapter 40 · 0% Book details