← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 86

Sashe 30

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zan zame miki Abba zan zame miki Mama zan zame miki kowa naki, ba zaki kara kuka ba.

" Sai ga hawaye wannan nabin wannan, sharewa nake.

" Ba zai kuma sanin inda kike ba, kai ko takowa ba zai kara ba, in sha Allah ba zaki kara kuka ba.

Lily na gaya miki in sha Allah.

" Kukan da nake yi ne ya sa ya kashe wayar.

" Ya Tahir ni daya ce mace da Ya Hafiz ba zai kyale ba?

Me nayi haka da wannan sharrin yake bibiyarta rayuwata?" Murmushi Yadiko tayi tana fa
in.

" Baki yi kome ba, sai kara samun kusanci da Ubangiji, ai ba kowa Allah yake jarabta ba dai me imani da tawwakali, Allah yana son bayinsa masu hakuri da takawwa, Allah yana son bayinsa masu yarda da imani da shi, idan kika amshi ragamar
addararki Allah zai miki musaya da abinda yafi alkhairi.

Allah zai baki miji na..

" "A'a Yadiko bar kiran wani mijin tsoro nake ji, tsoro nake ji zan iya mutuwa idan naji wannan kalmar!

" Na fada ina cusa kaina cikin cinyoyina.

Jikina rawa yake kamar an kunna min lantarki, iya Ya Hafiz da nasan halinsa ma ban sha ta dadi ba balle wani da ban san shi ba.

Na rantse da Allah gara a gaya min ranar mutuwata da sunan da namiji, gara na ga mutuwata.

Namiji ya shayar dani mamaki namiji ya kashe min duk wani jin dadin rayuwa, mace babu da babu bari ai da ciwo Yaya suna cikin abinda Allah ya bada na jin dadin rayuwar duniya.

Amma ni Ya Hafiz ya kashe min wannan jin da
in, waye zai zauna da ni bana haihuwa waye zai yarda ya zauna da ni da cutar hauka, bayan ya Hafiz ya cusa min damuwa a raina.

Ni a kan kaina na tsani kaina ba zan ina tsayawa kaina ba, taya xan amshi kaina.

Wannan kukan da nake ya dami Ya Tahir don haka ya fita.

A can office din Yan sanda Baban Bauchi da kanshi ya je yayi belin Hafiz, fuskarshi babu walwala ya ce mishi.

"Shin baka yarda da abinda na ce maka ba ne?

Ba na ce ka kyale ta na wani lokaci zan duba lamarinka ba ne?

Me yasa abinda ba ka yi yanzu ka fara?

Na gaya maka ko Lubnah zata mutu a gidanka zata mutu wato ban isa nace kayi abu ba kenan?

"
asa yayi da kai yana fa
in.

" Ba haka bane, Allah ya gani ina son Lubnah, Kuma ban mata haka da wata manufa ba, Sani ne kawai ya kama ni da dambe, wallahi ba zan iya cutar da ita ba.

Bayan ina son raunin baya ya warke don Allah ka yi hakuri ba zan kara magana ba sai ranar da ka min magana in sha Allah.

" Har zuwa yau Abba bai ga gundarin laifin da Hafiz yayi asalima gani yake kamar sharri ne da an fi karfinka, sannan kunyar dan uwansa da amshi case
in a hannunsa, sannan baya son dan uwansa ya hango gazawarsa akan Yaransa wato shi ya iya tankwara Hafiz amma shi kuma nashi Yaransa sun fi karfinsa, haka yasa ya zuba musu idanun su gama abinda zasu karshe dare daya Lubnah ta koma dakinta ko tana so ko bata so, shi ba zaa zubar mishi da zumunci a karon iska ba da darajarshi da kimarsa Yara da Matarshi suna juya shi, ba zai dauka ba.

Ace kamar shi sai yadda aka yi da shi.

"Muje ka ajiye ni a gida." Haka kuwa ya wuce gaba zuwa inda motar Abba yake, don da zai zo ya kira Sani akan yazo ya tuka shi, sai gashi ya ce mishi ai baya gari yana can hanyar Jos dan banza yana nan bai je ko ina ba yana asibiti.

Haka yasa ya tuko kanshi zuwa office din Yan sanda, ya je yayi belinsa, haka ya tuko Abba zuwa gida, a lokacin ya samu Umar ya kawo yadiko yana mai dauke da basket din Abinci, a hankali Mama ta fito tana kallon Abba ganinsu tare da .

Hafiz yasa ta wuce bata kalli inda yake ba, sama sama Umar ya gaida Abba din ya budewa Mama mota.

"Ina zaki Salamatu!" "Asibiti wurin Lubnah!" "Da izinin waye?" "Ai bana jiranka akan Lubnah, ka zabi abinda kake so, nima na zabi abinda nake so ai ba kuskure ba ne?

Muje Umar." Tana shiga motar Umar ya shiga tashi motar suka bar gidan.

Bayan fitarsu Hafiz ya shiga tashin hankali, kamar yayi kuka yake kallon kasa.

"Abba kayi hakuri amma ba zan iya rayuwa babu babu Lubnah ba, gara na mutu da na rasata!" "In sha Allah ba zaka rasata ba." Ya fada yana kara tausayin Hafiz domin har ga Allah tausayin Hafiz din.

Dakyar ya shigar da shi cikin gidan.

Bai iya cin abincin da aka bashi ba, kanshi a sunkuye kamar zai yi kuka ya rasa yadda aka yi har yayi shirme haka.

Ajiyar zuciya na sauke lokacin da nake kallon Mama yadda ta zuba min abinci tare da ita, ina murmushi nayi tana bani ina murmushi.

" Mama nifa ina kishin yarinyar nan!" Inji Sani, ya fada yana hararata.

" Mama ka kalli yadda yake wani hura hanci!" Murmushi tayi tana fa
in." Sani na, kyaleta tayi maka shigar sauri."
A hankali yake murmushi ya dauki spoon ya fara bani abincin shima Mama tana bashi, shigowa Aunty Innah tayi tana fa
in.

" Ikon Allah yau naga abinda ya ture turatu uwar Turanci a ramin tururuwa, ok nima bari na shiga." Ta dauki spoon ta fara ci, a hankali tana mai diba itama ta bani, Ya Sani ya bata.

Turo kofar da Aunty Hindatu tayi tana fa
in.

"Cin amana a jinin gidan Baba Malam Umaru yake oya ku matsa min." Haka yasa ta zauna ta fara ci itama kafin ta kai loma sai da ta fara bani, Aunty Innah ta bata.

Bayan mun gama Aunty Innah ta ce mana."an sallame ki yar nan!" "Na gode sosai." Haka muka shiga tattara kayanmu dama ba wani kaya ba, gidan Ya Tahir na koma,
A can gidan kuwa sai ga Hajiya Asiyah tazo Ita da su Aunty Nana Asma'u.

Kwanansu daya suka roki Abba ya basu damar ganina ya ce su sami Yadiko, haka ya gayawa Mama.

Mama kuwa ta ce musu.

"Kunzo ku kara sa min ita ne?" "A'a zamu bata hakuri tayi hakuri Hafiz ya gane!" "Ya bita makaranta ya rufe da duka ko?"
"Amma ai Alhaji yace zata koma!" Inji Hajiya tana murmushi.

"Murmushi Mama itama tayi ta ce mata.

" Ba mamaki idan na fitar da gawata Lubabatu zata koma gidan Hafiz kamar yadda ya ce ta haramtawa wa wani da namiji in sha Allah ya haramta mishi.

Idan kina ganin karya ne ki same shi ki ce ni Salamatu Galadima nace Lubabatuna ta haramtawa Hafiz ya ce bata haramta ba." Yadda take d'aga murya shi kanshi Baban Bauchi yana ji amma ba yadda ya iya ta kara da cewa.

" Ni ba haifi lubnah kuma naga wanda ya isa mata dole!

Wallahi tun daga karamin kotu har babban kotu sai an jimu da shi, ku fita kafin na haukace muku lokacin da kuke musguna mata kun manta tana da uwa ko?

Kun zata kowa haka yake, ke baki ji kunya ba ita da take juya zaki biyo ai Lubabatuna ta gama da danku sai dai wani ba shi ba."
Ba sai ga gagarumin rigima kai karshe suka dauki ai Hafiz bai sake ni ba, magana har kotu, abinda ya kara lalata lamarin.

Kamar yadda Ya Ado ya ce, ranar da yasa Yayuna maza da mata suka raka Jos tare da rakiyar Mama, haka nayi ta kuka da xan shiga jirgin.

Na k'amk'ame Mama ina kuka.suna tsaye har jirginmu ya tashi, daga nan suka wuce gidan Aunty Raliya, taji haushi tayi ta mita suna sallah la'asar suka baro Jos.

Nan suka sami bugun Bala'i da masifa na Baba Malam ya ce shi ya bada umarnin a mai da auren Lubnah Mama kuwa ta ce babu mahalukin da isa wannan aikin rigimar da ta kaure har Abba ya ce mata..

"Sai ki zaba aurenki ko Na Lubnah domin ba gaji da lalata min zumunta da kuke da sunan kuna bayan Lubnan?.........

Alhamdulillahi baki
aya anan na kawo karshen Free pages.
*08130269641*
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 18
Lagos
Mun bar Jos karfe biyu da rabi, karfe hudu cib muka sauka.

Garin yayi wani irin yanayi na alamar da ayi ruwan sama.

Tun daga Murtala Muhammad International airport na shaki kyakyawar iskar da babu hadi a cikinta.

A hankali nake takawa ina jin kamar an sauya ni rayuwata
addarata.

A yadda na fahimci mutanen garin kowa akan kafarshi yake, yadda suke kujiba-kujiba.

D'ago kai nayi ina niman Ya Ado, daga can nesa na hango shi a wurin Arrived, da dan sassarfa na isa babban wurin taruwan baki tare da masu barin kasar da komawa jahohinsu.

"Lubnah" ya d'aga min hannu, murmushi nayi wanda kana gani kasan yake ne.

Hannu ya mika min na isa gare shi ya
an rungume ni, irin side hug din, sannan muka jira kayana ya iso, ya tambaye ni ba gaya mishi sannan ya dauko min.

Ya riko hannuna yana fa
in.

"Welcome to lagos!" Yake nayi har muka shiga mota, ina zaune kamar wata bakuwa, duk na kasa sake jiki da shi.

Haka muka bar airport din minti goma sha biyar ya kai mu estate din da Ya Ado yake zaune.

Royal Garden Estate, close alausa Mitv, alausa Ikeja.

A kofar wani gida me kyau muka yi parking, ya kalle ni a hankali ya ce min..

"welcome to home!" Murmushi nayi na bude kofar na fito ina kallon yadda tsarin kowani gida yake ba kamar mu nan arewa ba, karya ka yi parking a kofar gidanka, aka bi motar har cikin gidan ma aka dauke.

Sai naji na samu nutswa musamman da garin yake hade rai, alamar zasu sha ruwa don gari ne na ruwa.

"Sweet haka muje ko?" Gyada kai nayi na bi bayansa da yar karamar hand bag dina, har muka shiga cikin gidan.

Aunty Zakiya ta zo ta rungume ni hannunta dauke da ludayin miya.
Chapter 30 · 0% Book details