← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 86

Sashe 79

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aunty Lulu!" "Na'am yau kunne!" Zama nayi nace mishi.

"Ina kwana?" Hankalinsa yana kan wayarshi sai latsawa yake, kamar bai ji ni ba, sai da na sake gaishe shi ya amsa, kitchen na nufa na shiga aikin gaggawa domin Yaran gidanmu sun tafi Islamiyya.

Babu wani abin karyawa don dumamen tuwo suka ci, doya na fere na turara musu, tare da miyar sauce din kwai, sai kunun tsamiya da na dama musu na shiga fito da shi, na hada baki
aya a gabansu, yaran na zuba musu.

Sannan na koma na matse fruit nayi musu juice da shi na fito na zuba musu.

Abin ya bani mamaki yadda yake cikin abincin kamar bashi ba.

Komawa sama nayi, wanka da brush nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa, na karya dan daurin dan kwali, Ban san me ya ke fisgana ba, amma na samu kaina da shafe jikina da humra mai kamshi, sannan ka fito na samu ya gama yana fama da wayarshi ne, lokacin da na iso parlourn kura min idanu yayi, sai da na kama shi yana kallona ya wayance kamar bai yi kome ba, na wuce kitchen na zauna a can na karya sannan na fito yaran suka gama cin nasu na tattara na kai kitchen.

Sai Santi suke.

"Aunty Lulu zaki raka mu, muje birthday party na yar class dinmu, kuma ance anan son two parent su zo ne, kin san Mom ba zata amince ba, shine muka zo da Uncle ko zaki bi mu.

Please!" Yadda suka yi maganar kamar nayi kuka, domin na fahimci ba wai zuwan kansu ba ne ba mamaki shi ya shirya musu haka.

"Bari ka kira Mijina na gaya mishi!" Na tsinci kaina da fadar haka, bai d'ago ya kalle ni ba har na haura sama na gama abinda zan yi ja fito sanye da wata laffaya akan kayan jikina.

Na fito a hankali nake takawa, yadda na iso yaran suka yi ta murna, haka muka fita satar kallona yake sau biyu ina kama shi, amma sai wani ha
e rai yake..

A wurin Birthday din hidima sosai aka yi, mu kanmu iyayen yaran sai da suka saka mana wani gasa.

Kusan a tare muka ci gasar, karon farko da naji wata irin soyayyar Yara ya kama ni, domin saboda Yaran nan sai da nayi kawaye Iyayen Yara, dayawa a wurin dauka suka yi ni Matarshi, ce kasancewar an san shi sai ya zamana idanun mutane akanmu, a kyautar da ya bada har da dollar guda ashirin, sai gift da yaran suka bada.

A waje haka mutumin nan yana da mutunci, rashin mutuncinsa a office suke.

Haka muka gama bikin muka dawo suka ajiye ni a gida, fitowa yayi daga motar yana dan matsa hannunsa, ni duk a tunani na crwa zai yi na gode.

"Idan kika shiga ki yi wanka domin turarenki." Kambu, banza nayi da shi na wuce humran nawa ne zan yi wanka akan shi wanda idan ba kazo kusa da Ni....

Rufe bakina nayi wata irin kunya ta kama ni, kenan turaren ya.

Da gudu na shige parlourn tare da haurawa sama, yayi gaskiya Innalillahi wainnalihir rajoun, wanka nayi tare da tsarkake jikina.

Duk kunya ya kama ni, haka nayi ta juyi har lokacin cin abinci yayi, ina cin abincin kawai sai naji gabana yana faduwa, sakamakon tuno maganarshi, gaskiya tafiya Japan ba zai yiwu ba, don ma azumi ya kusa.

Haka nayi ta cakalar abincin har Ya ado yace min.." idan ba zaki ci ba ai ba a miki dole ba!

" Mikewa nayi na dawo parlourn da Yorghurt ina sha a hankali, ni fa yanzu na lura wannan aikin ya kara ramar da ni, domin yan dukiyar fulanina basu zama a cikin yar bra da nake sakawa.

Haka nayi ta juya maganar, nan har barci ya dauke ni,
Washi gari lahadi, sakon da na gani ya turo min ya ce min. *Daren yau zamu tafi please kada ki hada kayanki d wannan perfume din yana da karfi bana sonshi* kambu mutumin nan ya rena min hankali, buga kofar da Ya ado yayi na ce mishi.

"Na'am!" "Dazu oganki yake gaya min tafiyarku karfe shida na yamma!" "Tow!" Haka na shiga hada kayana baki
aya dogayen ruguna ne, humran nan barinsa nayi na dauki body spray sai roll on na hammata, saukowa kasa nayi na samu Aunty Zakiyah na ce mata.

"Wai Aunty Zakiyah humran nan meye amfaninsa ne?" Dariya tayi tana fa
in.

"Kin saka ne?" "Eh kai yana da dad'i." "Sannu ko, tow na masu miji ne ranar ina ta son hanaki
auka, amma saboda Maman Amal ta cinye ki da baki kika
auka." Kasa kasa ta ce min.

"Na masu maza ne.

Idan kika saka namiji haukacewa zai yi akanki...." Da gudu na haura sama ban yarda na ji karshen bayaninta ba, na je na dauka na boye idan aka samu Mama ko Aunty Hindatu suka zo zan basu su su raba fa Aunty Innah.

Allah sarki shi yasa duk ya shiga damuwa.

Har dare ina kwance kawai nazarin yadda zan ganshi ne, karfe biyar da rabi Ya ado ya saka muka fito, na saka kayana a cikin motar dukkan yan gidan suka rako ni.

Yana cikin mota shi da Ubaid da Uncle Auta, kallonshi Uncle Auta yayi ya ce mishi.

"Bilal zaka tafi da Yar mutane kuma kace matar aure ce, please and please ka taya ta kare kimar aurenta, don Allah kada ka sake wani abu ya tab'a kimar aurenta Please."
"Wai wace ce ita da ya damu kansa da ita ne?............
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 56
Shiru Uncle Auta yayi, suka fito domin raka Turaki har cikin airport
in, ganin yadda take rungume Yayanta yasa shi jin wani irin abu.
auke kai yayi har suka gama alamar rarrashinta yake ita kuwa sai wani kukan shagwaba take, haushi ya kama shi kamar ya ce ya fasa kowa ya kama gabansa.

Anan dai suka daure har suka gaisa da Uncle Auta da Ya Ado, Ubaid ma sama sama suka gaisa da juna.

Wurin bakwai da wani abu jirginsu ya tashi.

Kallon Uncle Auta Ubaid yayi yana fa
in.

"Kana ta ja min tai wacece ita?" "Lubnarsa yarinyar da ya so ya Bauchi.

A yanzu Allah ya ha
a su a wuri guda amma ita kamar bata san shi ne wanda ya sota a Bauchi ba." "A'a renin hankali dai ni dama tun ganinta na ji bana sonta, haushi take bani kawai bata dace da shi ba shine yake haukarshi akanta, gaskiya ba zan tab'a barin ta kara saka mu, rasa shi ba domin babu alkhairi a tarayyarsu."
"Ba ruwanka da ita idan har kaso son alakarku tayi tsawo kada ka shiga tsakaninsa da ita ka ga yadda yake jin kishin nan tas zai iya yanke hukunci rabuwa da kai, a yanzu haka bai san bata da aure ba. baffa ya nuna mishi tana da aure kada ya ce zai yi wani abu na daban.

Don Allah kada ka yi wani abu da zai lalata alakarku!" Jin shi Ubaid yake amma yasan tabbas tazo sake yaudarar dan uwansa ne kafin tayi haka tabbas ya shiga tsakaninsu har abada."
Zance wannan ce karo na farko da nayo tafiya da wani ba muharramina ba, duk sai na takura.

Wani abinda na fahimta inda muka zauna VIP ne.

Tunda muka shiga wurina daban wurinsa daban, amma sau biyu ina kama shi dumu dumu yana kallona, na dauke kai ban kara kallon inda yake ba, har muka isa dubai da rana.

Mun bar can dare ya shiga mun shiga dubai da rana, anan muka yi sallah asuba da na duhur, kafin muka dawo airport
in ya zo min da abinci, na amsa ina kallon kasa.

Har muka shiga jirgi ban ci abincin ba.

Haka yasa baki
aya yayi ta duba ni ko naci abincin, ni kuwa naki cin abincin.

Haka muka isa kasar Japan da dare anan mukumukun sanyi, abin bai kara bani mamaki ba sai da na ga garin na kara godewa Allah da ya hankad'o ni nazo na ga sabon duniya, mun sauka a Tokyo anan aka yi taron na tsawon kwanaki uku, daga ni har shi bamu haduwa da juna sai zamu tafi taron, idan muka dawo kowa ya shige dakinsa, zai matu
ar wahala ka ga mutum ya leko, a cikin sati daya zuwa kwana goma sau biyu muka zauna a wuri guda.

Sai ana jibi zamu dawo ya buga min kofa, ba bude kallona yayi daga sama zuwa kasa ya ce min.

"Ins jiranki!" Komawa cikin nayi na gyara jikina, sannan na fito sanye da doguwar riga sai katon coat na sanyi da na daura, sannan muka fita yawo.

A ranar yawo kan munyi shi, sannan ya ja ni zuwa wurin part na abokansa, a lokacin da suka hadu aka yi ta hira, amma hankalinsa rabi yana kaina, ban san me aka mika min a kwalba ba, dawowa kusa da ni yayi a hankali ya sa hannu a ture ruwan, kallonshi nayi domin ruwan har wani hayaki yake, kallonshi abokan suka yi ya kalli wata daga cikin abokansa mata ya ce mata.

"Tinah kaita ta wanke jikinta." Muna tashi suka fara mishi magana.

"Me yasa zaka zubar da liquor din da muka ba ta?" Murmushi yayi ya mike tare da
aukar jakarta.

"Ita muslmace kamar ni, kamar yadda Allah ya haramta haka nima hakkina ne na kare mutuncinta, sannan kuma ai baku gaya min zaku bata wani abu ta sha ba, da ta sha kuwa sai ka hadiye kwalbar!" Iya nan naji ya mika min jakar muka bar wurin.

A hankali muke tafiya daga ni har shi jikinmu a mace yake, na rasa me zance me shi, shima kuma bai min magana ba har muka isa masaukinmu.

Sai da na bude kofar na shiga ya wuce abinsa.

Washi gari da sassafe ya tashe ni muka je sayayya.

Muna gamawa aka wuce da shi airport kafin gobe sun gama kome, da la'asar na dan fito daga hotel din ina tsaye a waje na hango Airah da shi suna magana, yaushe ta zo?

Abin ya bani mamaki ganin na hango su yasa ta karaso.

Cikin yanga da jan hankali ta ce min.
Chapter 79 · 0% Book details