← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 86

Sashe 53

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan idan da kowani mutum yana da iko da
addaransa da dayawa basu yarda ajn haife su a low background ba, amma da yake mu musulmai ne masu bin tafarkin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama." Muka karasa salatin tare ta daura da cewa." Me kike tsoro wanda da baki gani ba?

Me kike gudu wanda da bai same ki ba, me yasa ba zaki yi accepting din kanki ba?

Tsoro yana da kyau amma rashin karban kai shine asalin tsoron da ake gudu, dayawa masu kashe kansu a duniya tsoron karban kansu suke, accepted yourself, love yourself, and move on, idan kika yi haka zai matu
ar wahala wani ya rusa ki, ko yan uwanki zasu kara jin dadin you accepted yourself, zasu iya miki yaki ne idan sun ga kin karbi kanki a yadda kike, a duniya ma zata girmamaki ne idan kin amshi kanki, ko waye zai girmama ki ne idan yaga kin amshi kanki a yadda kike, duniya da mutanen cikinta basu damu da ka mutu ko ka rayu ba, damuwarsu shine taya zaka gaza a maka dariya, amma daga lokacin da kika nunawa Duniya zaki iya survive idan da mutanen cikinta, ko babu ita da mutanen cikinta zaki iya tafiya da kanki, daga lokacin duniya zata dawo bayanki, zata koma tana yayyataki ai ke jaruma ce, a kowani raunin dan adam zaka samu na kusa da shi sun bada gudummawar maganin warka da raunin, amma idan raunin ya gaza warkewa kowa zai watsa a kan rauni, ki kaunaci kanki, duniya sai ta kaunace ki.

Ki koyo saka kanki farin ciki duniya sai ta taya ki farin ciki.

Ki kashe tsoron da yake ranki sai ki tayi cikin sallama, idan har kika rayu da farin ciki babu wnada ya isa kallonki ya gaya miki magana, shi mutumin da yayi gwagwarmayar domin ya rayu don lafiyarsa zai matu
ar wahala bai samu soyayyar gaskiya ba, kina bukatar ki girma da kanki ba tare da wani ya ce shi ya saka ki girma ba.

Open your heart and make a wish, kina son ki rayu ki ga idan Allah bai raya ki ba, ko da zaki yi addu'a matukar baki yarda da kanki ba, matukar baki saka yakinin ba tow babu inda zaki domin Allah yana amsar Addu'ar wanda ya yarda da shi ya kuma saka yakinin zai taimaka mishi, idan kika ga matan da suke gym din nan, akwai wacce mijinta har sayar da ita yayi ta tafi karuwanci, akwai wacce Mijinta watsa mata ruwan battery yayi bai samu fuskantar ba ya zube a bayanta.

Akwai wacce kullum dukarta yake saboda ta haifa mishi yarinya handicap, baki godewa Allah ba da ya miki ni'imar da sauran basu samu ba?

Idan da zan bude miki file din kowacce, sai kin ji kamar taki matsalar ba kome ba ne, mu anan
abilarmu babban abin tashin hankali namiji ya sake ki, za a nuna miki iyakarki, ina son ki zama mace ta farko Bahaushiya daga arewacin Najeriya da ta san kanta ta kuma yarda da kanta.

Idan har kin yarda da kanki, Auntynki Nuratu Kafaya tana kiranki, idan kuma kika sake tsoron nan ya mamamye ki.

" Murmushi tayi ta mike tana me daukar jakarta tare da yiwa Aunty Zakiyah magana.

" Madam zan tafi!

" Fitowa Aunty Zakiyah tayi muka rakata.

Cikin wata motar alfarma ta shiga, ta d'aga min hannu, haka naji kamar anya xan iya zama mutum kamar yadda ta ce?

Jiki a ma ce na shigo cikin gidan.

Ina kallon kasa.

"Ya kamata ki kara gaba, sannan ba zaki bikin Sani ba, ke da Bauchi yanzu sai wani Ikon Allah.

Ba zaki ko ina ba, ki zauna ki gina kanki na jima da sakawa a raina ba zaki Bauchi ba, ita dai wacce aka koran nan sai ta zama wacce ake kwadayin ganinta, idan Mama kike son gani Allah ba zai hana mu kudin kawo ta nan ta kwana biyu ba, zamu tafi Bauchi ni da Yayanki, ke da Yara zaku zauna anan, a matsayina na wacce makarancin likitanci, idan muka je Bauchi aikin da muka sha wahalar yi dare daya Hafiz da Abba zasu rusa mana, babu inda zaki kin ji aiki domin ba zamu yi gini wani ya rusa mana ba.

" Ji nayi kamar an kara yanta ni, murmushi yayi ban ce mata kome ba muka shigo cikin parlourn na tayata kwashe kayan da ta kawowa Bakuwa muka kai kitchen.

Nan na wuce dakina na kwanta sai lokacin sallah ka tashi nayi, a cikin addu'ar da nake har da Allah ya bani ikon yarda da kaina.

Sai dai kuma ina gama addu'a naji wasi-wasi a raina, haka na lumshe lekowa har na wani lokaci.

Kafin na bude ina kiran sunan Allah.

Wasi-wasi ya saka ni a gaba, washi gari na shirya na tafi makaranta, karfe biyu na taso, sai na tsaya a gym din, yan wurin na ganina.

" Lulu!" Fuskarsu cike da fara'a suna ta min barka da zuwa.

" Tunda kika zo baki kara zuwa da fatan dai lafiya domin dukkanmu nan mun zama daya." Gyada kai nayi ina fa
in.

" Ban ji dadi ba ne?" Ai kuwa a rud'e suka yi ta tambayata meke damuna, na ce ciwon kai nan suka yi ta min sannu sannan na shiga wurin Aunty Nuratu Kafaya, na samu tana tattaunawa da wata mata sai kuka matar take.

Itama dai katuwa ce.

" Ku yi hakuri ba ri na jira a waje!

" " A'a gashi ki tafi daya office din ki bawa Wasim zai miki bayani." Gyada kai nayi ina fa
in.

" Na gode sosai!

"
Na fito na tsaya a bakin kofar ina raba idanuna, yarinyar ta Nasiba na gani zata fita ta ce min.

" Aunty kina son abu ne?

" Gyada kai nayi mata ina mika mata.." office din Uncle Wasim zaki!

Muje na kai ki." Ina bayanta ta kai ni har office dinsa, da sallama muka shiga, shima yana bako, yadda yake magana a nutse zaka fahimci shi din Coach ne da yake ganin mutane daban-daban.

"Kanwata shigo!" Ya fada yana murmushi, kafin ya kalli mutumin ya ce mishi.

" Yawwa kamar yadda na gaya maka, zaka iya kawo ta mu fara ganin yadda zamu gina lafiyar jikinta.

" Mika mishi hannu Mutumin yayi sannan shima ya mika mishi ya mike matsawa nayi mutumin ya fita ya zauna yana nuna min wuri na zauna.

Mika mishi takardan Nasiba tayi tana fa
in..

"Uncle ni fita zan yi, naji wai an sake sakamakon Allah yasa ina cikin wadanda zasu diba." "Allahummah Amin Daughter Allah ya bada sa'a." Ya fada yana mata murmushi fita tayi, ya kalle ni.

"Shekara biyu kenan tana niman aikin masu kula da fasinjoji na jirginsa, bata tab'a sarewa ba.

Bana ma haka har azumi take da sadaka Allah ya bata sa'a.

Kin ga kuwa dole mu taya ta da addu'a Allah ya bata sa'a ko?" Ya fada yana kallon takardan hannun..

"Da kibar aka haife ki?" Girgiza kai.

"Bana son body language, speak!" "Tow!" "Kin tab'a haihuwa ne?" "A'a;" kallona yayi da kyau, kafin ya ce min..

"kin ta
a birth control ne?" Anan na sunkuyar da kai ina matse hannuna, bude drower yayi ya ciro wani irin ball ya mingiro min, "idan kika shiga irin wannan yanayin us it, kina matsawa yana rage damuwa.

Me yasa kika sha birth control?" "Tsohon Mijina ya bani." "Amma yana sonki!" Matsa ball din nayi murmushi yayi sannan ya ce min..

"duk
mutumin da yake sonka baya naka abin hana daukar ciki am sorry!!" Shiru yayi ya cigaba da cewa.

"Zaki ragu amma sai kin saka a ranki zaki ragu, kina da saurayi ne?" Da sauri na kalle shi.

"Oops babu ko?" Ya tambaye ni yana murmushi.

"Tow daga yau ki saka a ranki, kina son ki burge saurayinki ne, kin san waye saurayin?" Girgiza kai nayi, murmushi yayi ya ce min.

"Kanki, kanki zaki burge ki ji a ranki soyayyar da zaki yiwa jikinki don kanki zaki yi ba don wani ba.

Kin san me?

Dole ki fada soyayya da kanki haka zai baki damar kula da kanki, sannan ki yi hakuri da kowa ki yi hakuri da kome kada ki sake wani ya ba'ta miki rai, ki ji a ranki kina da kanki da ya tsaya miki all I want to you love yourself, ki yarda da kanki ni kuma zan yi
arin baki step by step na kula da kai.

Wannan sune tsarin abincin da zaki fara ci kullum da wanda ya haramta miki,.

Idan kina da soyayya da bread da fanta irin naku na Fulani ayi hakuri daga yau an daina shan duk wani abu me zaki, kin ga kibar nan naki idan da za a bincika ba za a rasa uric acid da Diabetes ba, sannan akwai tarin kitse da dole a narka da shi, sai kuma rage cikin abinci mai yawa, idan za a ci a sha ruwa sosai, sai a hada akwai bayani akan nan duba ki gani."

Ga wasu hanyoyi da za su taimaka miki wajen rage kiba da kuma wasu shawarwari a kan abincin da ya kamata ki ci:
Hanyoyin Rage Kiba da Inganta Lafiya
1.

Kula da Abincin da Kike Ci
* Rage Abinci Mai Sukari da Mai: Ki rage cin abinci mai zaki (kamar su alewa, lemo na kwalba, da waina mai sukari) da kuma abinci mai yawan mai (kamar soyayyen abu).
* Yawaita Cin 'Ya'yan Itace da Ganyaye: Su na
auke da sinadarai (fiber) da ruwa da suke sa
i da ciki, kuma suna da
arancin Kalori (calories).
* Cin Abinci Mai Wadataccen 'Protein': Irin su kifi,
wai, nono marar mai (yogurt), da wake/gya
a.

Protein yana taimakawa wajen rage yunwa kuma yana
arfafa tsoka.
* Rage Cin Abinci Mai 'Starch' (Carbohydrates): Abinci irin su shinkafa, taliya, burodi, da fura.

Idan za ki ci su, ki ci da 'ya'yan itace ko ganye.
2.

Yin Motsa Jiki (Exercise)
* Yin Tafiya: Ki fara da tafiya mai tsawo ko da na minti 30 ne a rana.
Chapter 53 · 0% Book details