← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 86

Sashe 74

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin na
auki biro da takarda a cikin jakata na fara rubuta abin da ya dace ina gamawa na ajiye mishi tap dinsa, ai kuwa da azabar gudu ya ja motar muka bar titin, lokacin da muka isa saura minti biyar a fara taron, yana tafiya ina bin bayanshi har inda za'a yi taron, tunda muka shiga ya samu wuri ya zauna aka fara dogon turanci nan, aka fara gabatar da kai, nima na kalle shi ya dauke kai, sannan na gabatar da kaina.

Sannan na fadi abinda ya kawo.

Bayan na gama na zauna.

Cikin abinda bai wuce minti talatin ba, aka fara gabatar da abinda ya kawo an sayar da kayan shi akan ku
i me yawan gaske wasu yaci riba wasu ya fadi sosai, kuma dama kasuwa ta gaji haka, amma ribar tafi asarar yawa, yana gamawa.

Muka fito , wani dan kasar China ne ya ce mishi.

"Mr Turaki ko zaka zo mu ci abincin rana ne?" Sai lokacin na tuna fa na zo da abinci, "Mr Ma na gode." "Haba ko ita ba zata ci ba!" Kallona yayi ya ga yadda nake kauda kai.

"Itama!" "A'a Mr Turaki barta muje ta ci!" Haka muka wuce aka kai mu wani wurin cikin abinci irin VIP nan!

Wurin ya hadu kamar me iya haduwa zama nayi, aka kawo abincin hatta yadda abincin yake tururi sai da ya sa naji cikina yana wani irin
ara irin ina jin yunwa.

Kallonshi nayi na kai hannuna cikin, bai wani damu da ya kalle ni, abincin ya fara ci ina kallon abincin, "Dig!" Ya ce min, haka nayi ta juya abincin ina hadiye yawu, tashi yayi tare da barin wurin, da sauri na fara cin abincin, ina ci ina kallon ta inda ya bi kada ya dawo ya samu ina ci, na kai loma kenan na hango, haka na ajiye cokalin.

Na bar abinci me shegen dad'i.

Da yazo ya ga yadda na ci ba sosai ba, haka ya ce min.

"Zan tafi fa!" Mikewa nayi kamar na juye abincina, sau biyu yana kamani ina kallon abincin har ga Allah ban koshi ba, haka yayi gaba abinsa, sai da muka shiga mota sai ga masu aikin wurin sun kawo min leda me dauke da Chinese dish, kallonshi nayi naga shi ba ma tani yake ba, a hankali na risina ina fa
in.

"Na gode!" Daga nan bai tsaya da ni ko ina ba sai Lekki.

A kofar wani hadadden gida ya tsaya, fitowa yayi yana mai nufar cikin gidan nima na bishi, muna shiga Yaran nan suka lullube shi da murna, suna ganina suka fara ihu.

Haka na shiga na same su, ya fita ya shigo da ledojin nan, daga nan ya juya yayi tafiyarshi.

Cikin gidan muka shiga ina tambayar su.

"Ina Mamanku?" "Ta tafi Kumo Family Mansion" abinci na juye mana muka ci ina kallon yadda suke ta wasa da abincin, na ce a raina Yaran attajirai fa haka suke basu damu da abinci ba kamar irinmu yan medieun class, kazar guda ce muka ci rabi me aikin ta dauki sauran ta saka a frij, muka cigaba da hira har bayan la'asar da malaminsu ya zo, sai lokacin Mamar ta shigo tare da shi, tana kuka idanunta yayi jajjur ganin yadda baki
ayansu suke kallona yaushe nazo.

"Ke me ya kawo ki?" Kafin na bashi amsa ya shigo yana waya , da hannu ya min alama da na fito mu tafi.

Haka na fita muka wuce gida, kular abincin da nazo da shi na dauka sai nayi wayam, babu kome a ciki, s hankali na ajiye ina satar kallonshi, wani hade rai yayi irin baya son wasa, lokacin da muka isa gidan na fita tare da
aukar kular na rufe mishi kofar, na shiga cikin gidan.

Ina shiga cikin gidan na zube a parlourn ina nishi, na gaji sosai.

Duk da ban yi wani aiki ba amma kuma zama wuri
aya ya dame ni.

Da wuri na kwanta bayan mun sha waya da Mama, kai na ji dadi.
----
Wato wani irin rigima ake a family house
insu, akan Jasminah sun matsa lallai sai ta koma dakinta , ko kuma ta bawa Fahad Yaransa.

Ita kuma ta ce sai dai ta mutu da ta bashi Yaranta, akan idanunta ma aka yiwa yarta fyade.

Wannan abin ya tab'a Turaki, don haka ya ce a shigar da maganar kotu domin ta bata damar rike Yaranta, uwarta kuwa ta ce idan ta haifeta kuwa ta kai Fahad kotu, sai ta mata baki shine, abinda ya d'aga mata hankali, wani irin kuka take wanda yake damun dan uwanta.

Yana ajiye Lubnah ya wuce gidan Noma family, ana cewa gashi nan ya zo a lissafinsu ya zo basu hakuri su kyale ta, sai dai lissafinsu bai zo yadda ya dace ba, domin yana shiga gidan da shi da Barista Abdul Hakim, wanda ya samu yana jiranshi a kofar gidan a tare suka shiga cikin nan, yan gidan na ganinsa suka fara dariya, zama yayi ya ce.

"ina son ganin Alhaji Noma." Fitowa Dattijon yayi yana wani bu
ewa kamar kifi ya samu wurin zuba kwai, yana kallon Turaki gabanshi ya fadi amma kuma sai ya dake har ya shigo cikin parlourn ya zauna.

"Na ji ka kafa dokar ko Yaran Jasminah ko dakin Mijinta." Tashi turaki yayi yana kallon parlourn baki
aya ya ce mishi.

"Ni kuwa sai naga kamar wannan gidan da duk abinda Noma yake da shi, aro Alhaji Haris Kumo ya bashi domin akwai sa hannun a wurin nan......
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 52
Ya mikawa Barista abdulhakim hannu, sai ga takardu.

Da aka saka abu kusan shekaru ya kalli Baristan ya ce mishi.

"Amma kasan takardun nan sun yi kura?

Dai dai kuma kome tar kamar yanzu aka saka hannun!" Ya fada tare da kardakade takardan, yana mai daura takardan a kan table, ya kuma d'ago kai ya kalli Alhaji Noma.

"Na baka awa ashirin da hudu ina bukatar kudin nan, ko kuma kilu ta ja bau, idan" daga haka ya mike zai fita Alhaji Noma ya ce mishi.

"Me kake bukata?" Shafa sajensa yayi yana kallon kanshi a madubi.

"Duk wata matsalar da yake kunno kai a kashe ta ta hanyar da aka bi, ko kuma ni na kashe ta, ta irin wannan hanyar?!" Ya fada yana d'aga kafad'arshi.

Yadda ya juya yana fa
in.

" Ina da thousands of this copys" sannan ya juya ya kalli mutumin da akalla zai yi sa'ar Babansa ya saka yatsu biyu ya saka a saman idanunsa alamar ina kallonka, daga nan ya wuce yana mai barin gidan shi da Barista abdulhakim, " Amma baka niman zaman lafiya, yanzu kana ganin haka zai yi aiki?" "Sosai kai, zuba idanu ka ga ikon Allah." Daga haka suka rabu.

Kamar yadda ya shiga tsakaninsu, haka lamarin ya mutu kamar daukewar wuta.

Ai idan kana da kudi babu abinda ba zai yiwu ba, sai ikon Allah.

Da wannan Jasminah ta samu zaman lafiya, Fahad ya kirata ya ce ya janye ta rike Yaranta idan yaran suka samu lokaci su zo hutu, ta amince aka kashe maganar baki
aya kamar bai tab'a faruwa na, dama ai zancen kenan.

Kallon Ya Ado da yake waya da Ya Umar yake tambayarshi.

"Na shiga maganar ne domin na kara nisanta ta da shi, sannan yadda suka yi juya hankalin Abba yasa na shiga lamarin amma idanun kamfanin yana kanshi a duk inda yake saboda sun ce suna da case nasu a kasa tow sai CEO din ya kama shi yana
arin cutar da ita ba wani abu ba ne, shi a nashi lissafin ya razanata ne ta amince da shi, amma akwai wani abu da na fahimtar da nayi mishi, kamar akwai sanayya da juna!"
Kallon Ya Ado nayi da kyau kafin na kara mai da hankalina, kafin ya gama wayar anan na fahimci wato da wancan Masifaffen rufe shi yayi, da yadda aka fito da shi, sai na ji kamar ni aka ceto daga farmakin Ya Hafiz.

Tunda na ji haka sai na ji mutumin ya
an yi abin arziki, kuma sai ban damu da na ji wani abu daga gare shi ba, washi gari ya kama Monday, sai da na jira Ya Ado ya sauke ni,da wuri na isa na fara aikin da na ga an jibga min, sai da na harari kofar ya kai sau goma, ina tura baki gaba.

Tun karfe takwas nake abu daya har wurin karfe goma da ya shigo, na tashi na bi shi na karanto mishi menu na yau baki
aya.

"Yau bana son ganin kowa!" "Ok sir!" Na fito na cigaba da aikina wurin karfe sha biyu saura wasu mata shigo da sauri na fito na gaishe tare da cewa.

"Yau ya ce ba zai gana da kowa ba, yana da aik...." Saukar wani gigitaccen mari na ji a gefen fuskana, wanda yayi daidai da fitowarshi zai fita.

Ban san wacece ita ba amma yadda ta mare ni, ya saka ni jin wani abu.

"Me tayi miki?" Ya tambaye ta, "Ubanta ne ya gina kamfanin da zata dakatar da ni!" "Ba Ubanta ba ne, amma Ubana da Uwata suka tsayar da kamfanin haka,.

Kin yi dacen na fito da sai ta rama domin na gaya duk shegen da ya ta
a ta ta rama!" " Ni ce shegiya?" Gefenta ya bi ya wuce, ta kama ihu da fada akan ya kashe mata auren yarta, ni dama tunda na ganta nasan ba arziki ya kawo ta ba, don haka ban wani damu ba.

Ganin yadda Jasminah ta zo tana kallonta cikin fushi da b'acin rai.

" Na rantse da Allah, idan baki rabu da shi ba sai nayi ruined rayuwarshi." Duk yadda ta kai da dakewa, sai da ta ce mata." Ba zaki iya ba, tun yana Yaro kike kokarin haka me yasa baki yi nasara ba, rayuwarki xa kika cika shi da karya da yaudarawa babu abinda kika sani.

Anya ke uwa ce?

Shi bai tare miki kome ba, ko ba kome zan ji kamar Abba yana raye!" Rike ta nayi ina girgiza mata kai, ina fa
in.

" Kada ki.

Aikata haka, Uwa ce ba a wasa da lamarinsu.
Chapter 74 · 0% Book details