← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 86

Sashe 73

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba kome!" Na fada tana barin wurin na kurawa kofar office
insa idanun ina jin wani irin haushinsa, haka na dauke kai na cigaba da aikin har na kammala na koma ban daki na gyara jikina koda na fito babu kowa kusa fitilar wurin a kashe office dinsa ma hasken a kashe, da sauri na tafi wurin zamana na kunna wayata, ina d'ago kai muka yi ido hudu da shi, wani irin kara na sake tare da wurgi da wayata.

Zube a kasa tare da rike kirjina da amsa min da wani irin ciwo.

Ina haki kunna wutar parlourn yayi ya tsaya tare da hade rai.

Kuka na saka ina zaune akan gwiwata.

"Ina da abin yi." Wato yana jirana, da sauri na mike na hada kayan da na zo da shi.

Na bi bayanshi da sauri domin ya kashe wutar parlourn, garin binsa haka na yi karo da bayansa cak ya tsaya nima nayi, tare da ja da baya.

Ina jan hancina na ce mishi.

"Sorry sir sorry Sir." Cigaba yayi da tafiya nima na bi bayansa.

Har muka shiga elevator, tsayawa nayi can bayanshi ina sunkuyar da kaina har muka fito kasa.

Sai da muka fita aka rufe office din baki
aya.

Wurin motarshi muka nufa baya shiga, ni kuma na shiga gaba.

"Har kun taso?" "Eh!" Na cewa Taj da ya tambaye ni, "kamar kin yi kuka?" "A'a ban yi ba!" Na fada, zai kara magana Masifaffen nan yayi gyaran murya, haka muka cigaba da tafiyar har muka iso gida, fitowa Taj yayi ya bude boot din motar ya ciro min wasu paper Bag har guda uku, ya ce min.

"Inji Oga gobe Saturday akwai meeting din da za a yi a Eko hotel da fatan zaki shirya da wuri." "Har Saturday ma akwai aiki ne?" "Eh amma ba wai na office ba.

Wasu mutane ne zasu sayi kayan kamfanin yana da kyau ki shirya da wuri!" "Gaskiya!" "Tow ni yau xan tafi Abuja akan meeting, idan ya ji kina musu tura ki kano zai yi!" Jin haka yasa na ce mishi.

"Tow shi kenan!" Mishi godiya tare da shiga cikin gidan, Ya Ado na samu yaran sun kwanta, Aunty Zakiyah tana kitchen, gabansa na je na zauna.

"Yaya na gaji aikin nan ba irin nawa ba ne!" Na fara mishi kuka.

"Mutumin nan bai da imani, kome nayi fada yake min, ba halin nayi mistake yayi ta fa
a kamar ni daya ce na fara kuskure." Murmushi yayi ya ce min.

"Haka kowa yake farawa, sannan ai ya kira ya gaya min yau da gobe kuna da ganawa da wasu yan kasuwan kasashen ketare, shi yasa ba zaki dawo da wuri ba." Sake baki nayi ina kallon Ya Ado wato Masifaffen nan ya san kan duniya ya kira Ya Ado ya kare kanshi, kada ace na jima har da fada mishi aikin da muke da shi gobe.

" Ni dai ba zan je ba!" Na fada ina kuka.

"Tow shi kenan!" Ya fada yana kallon kayan da ba shigo da shi, kusan kayan ci ne sai pad.

Da sauri na maida shi cikin na wuce dakina na can sama na wanka na shiga nayi sannan na fito na gyara jikina, na fito na ci abinci sannan na dawo na rage sauran aikin na kwanta.

Wayyo Allah dad'i nayi barci har karfe tara na safe, don cikin dare da na sauya pad na koma na kwanta ban kara bude ido ba.

Sai da na ji ana buga min gadon na bude idanuna." Kin yi baki suna parlour." " Baki kuma?

Su waye?" Na tambaye ta bata kula ni ba tayi tafiyarta, hulata na dauka na saka akan riga da wando na barcin da yake jikina.

Ban daki na shiga na yi brush na wanke fuskana sannan na fito,.

Na sauko kasa ina fa
in.

" Kuma dai weekend din ma ina murna na rabu da jarabar wancan Masifaffen mutumin me kama da yan damben turawa.......
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 51
"Fisabiilillahi ko a gidan gwamnati Asabar da Lahadi hutu ake.

Ni yanzu ko Gym na daina zuwa tunda na fara wannan aikin me shegen wahala waye ya sani ko sai na gama aikin ma karshe a ce za a kore, Aunty Mutumin nan ya cika barga, haka ya min shekaranjiya wai zai kore ni, ko jiya oho.

Kin ga yadda ke tafiya kamar wani robot" Na sauko har parlourn, ina kwaikwayar tafiyarsa, kawai kamar ance ns duba kujeran da yake kallon tv, da sauri nayi baya ina fa
in.

" Innalillahi!

" Nayi baya ina toshe bakina, kafin na juya da wani Muslimin gudu aikuwa na ji abu ya kwashe ni sama, na hantsila tare da dokuwa da kasa, takalmina kafa daya yayi tsalle sai a fuskarsa, Allah ban san lokacin da na ce.

"Na mutu!" Na tashi na haura sama da gudu, ina fadin shi kenan.

Abin ya zo wani iri amma kuma Ya Ado sai da yayi dariya yana fa
in.

"Silly girl, don Allah ka yi hakuri bamu san zata fito tana mocking dinka ba don Allah ka yi hakuri!" Murmushin yake yayi yana fa
in..

"Muna jiranta." Ya saka kai ya fita, bai san dalilin da yake son ya ganta a kusa da shi ba.

Bai sai me yasa yake jin haushinta ba, amma a duk lokacin da ya ganta yana jin kamar ita din da ya sani can ita ce a gabanshi.

Sai dai ita wannan ta sauya dayawa.

Fitowa yayi waje, wato asalin yadda aka yi ya shiga cikin gidan, ya zo ya tsaya tare da tunanin wanda zai tura cikin gidan sai ga Ya Ado ya dawo daga Gym da yake weekend yana zuwa, kawai sai ya ganshi a kofar gidan, har zai wuce sai ya dawo ya mika mishi hannu suka gaisa ya ce mishi.

"Kana son ganin Lubnah ko?" "Eh" kawai sabo da a fakaice kallon Ya Ado yake yason ya ga ko mijinta ne amma wani abun mamaki sai ya ga suna kama da Lubnah, sai ya kauda kai har ya ado ya ce mishi zai duba ko ta shirya, yana zuwa ya samu tana barci shi ne ya fita tare da shigo da shi cikin gidan.

Shine ta mishi rashin mutunci.

Lashe bakinshi yayi yana godewa Allah da iya shi ka
ai yazo bai dauko wani ba, balle ya sha kunya.

Tunda na shiga nake jin kamar zuciyata zata kwace a kirjina, "wayyo Allah na!" Na fada a hankali, kamar xan yi kuka.

Buga kofar aka yi daga waje Ya ado ya ce min.

"Ki fito yana jiranki, kuma zaki sani ba dai bakinki bai da lizami ba" bude kofar nayi da karfi ina fa
in.

"Ya ado kun san shine ya zo, ba ku gaya min ba." "Je ki shirya yana jiranki ai ba zai nuna miki ya ji me kika ce."
Kamar nayi kuka haka na haura nayi wanka na shirya tsaf, sannan na dauko abaya na saka tare da daura hula kafin na saka gyale na nad'e kaina.

Haka na shirya ina fitowa Aunty Zakiyah tana mika min wata yar jaka tana fa
in." Baki karya ba, gashi nan ki karya a can." Kamar nayi kuka haka na fito kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki.

Har waje na fito yana mota, ina zuwa na gwada bude bayan mota amma a rufe gaban na zaga na bude na zauna.

Kasa kallonshi nayi domin sai yanzu nake jin abin a raina, har ya tashi motar ban iya ce mishi cikanka ba.

Ni kaina kamar na nutse kasa, haka ya cigaba da tuki cikin kwarewa.

Wani unguwa muka isa wanda yake bakin ruwa.

Yayi horn a bakin kofar gidan.

Aka bude kallonshi nayi naga fuskarshi a ha
e kamar yaga hadiri.

Haka ya shiga cikin gidan, aka zo aka bude kofar inda yake aka yi tare da inda nake.

Haka ya fito, "kafin ki samu abin zagina ki hado kome yana baya!" Kamar ba fasa ihu haka na ji, a hankali na dauki kayan na bi shi da su.

Wani kwali ne mai kyau sai wani jaka paper Bag, muka shiga cikin gidan.

A hankali nake bin bayanshi, har muka wuce ta wani lambu kafin muka isa babban fili manyan mutane, kamar na juya saboda yadda ake kallona tare da da shi.

Yatsawa yayi kamar zan yi tuntube ya ce min.

"Ki nutsu!

Bani kayan!" Mika mishi nayi muka jera tare har zuwa cikin wurin da ake a taron, suna ganinsa baki
aya suka mike suna ta tafawa ana fa
in gashi nan ya zo.

A hankali yake kutsawa wurin manya mutanen da suke can gaban, ni kuma na tsaya daga dan baya baya.

Juyawa yayi ya hango ni ina tsaye a gaban wasu table.

Kallona yayi irin kallon meye haka?

Kawai sai na taka wurin da yake na isa, mika min hannu wani mutum yayi amma ban bashi hannun ba, yadda ya bi mutumin da wata lalatacciyar kallo yasa ya koma nan aka gabatar da abinda ya ha
a su, sannan suka fara jawabi, tare da tsaya akan abinda ya tara su.

Ina jinsu kusan akan taron karawa juna ilimi akan kasuwanci ne, sai wasu fiyale da aka saya, har aka gama maganar ina tsaye, kusan awa daya muka yi kafin aka tashi muka fito, sai hoto ake da shi, a yadda yake hade rai da nuna baya son na shiga hoton na koma can, Masifaffe kawai, na fada a raina.

Muna gamawa da wurin muka wuce Eko hotel, kafin mu bar wannan guest house din ya mika min table tap din, wayarshi ya shiga kira, bayan ya kira aka dauka "Sir kana tare da ita ne?" "Hmm!" "Lubnah dama kin san jiya na gaya miki zaku Meeting tow ki duba abubuwan da zaku tattauna a wurin meeting din, yana cikin table tap din na shirya kome!" "Ok na gode!" Bai jira me zai ce ba, ya kashe wayar.

Haka na cigaba da duba tap din wani abu da na fahimta shine yadda yake tuka motar a hankali kamar ba zai isa inda zamu ba, yana tuka motar yana kallon agogon hannunsa.
Chapter 73 · 0% Book details