← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 86

Sashe 19

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ai dama wancan gidan ban san lokacin da ta sayar da shi ba!

" Fitowa nayi daga cikin dakina na zuba mishi idanu.

Na kasa magana kawai sai ya rude.

" Lulu!" Juyawa nayi na koma dakin, na kwanta.

Wacce irin kiyayya ya Hafiz yake nuna min ne?

Me nayi mishi da baya gudun jogana min laifi ko mi kankantarsa?

"Auta!

" Tashi nayi da kyar na leka wajen.

Mika min kudi Ya Tahir yayi yana fa
in.

" Nasan you are broke, gashi ki rage na abin zuwa gobe suna.

" Kallon kudin nayi nace mishi.

" Ina da kudi Ya Abba ya turo min shekaranjiya, Ya Almu ma ya turo Ya Sani ya ce idan nazo gobe zai bani sabon waya ya ishe ni." Ina son naga reaction din Ya Hafiz kuwa Allah bai kunyata ni, sai ga eyes ball dinsa kamar zasu fado kasa kuma maganar gaskiya babu wnada ya bani kudin so nake na ga yadda zai yi, "oya karba nima ga nawa!" Inji Ya Tahir ya juya yana fa
in.

"Ina jiranki fa gobe da wuri domin akwai liyyafa kin san wannan ne farkon samun Ya mace a gidana, kuma ina son nayi surprise dinki ne!" Murmushi nayi na fito ina rako shi, juyowa yayi ya riko hannuna har kofar gidan wurin da ya ajiye motarshi, ina murmushi ko ba kome nayi farin ciki, nauyin da nake ji a raina ya ragu, a kofar gidan su Maman Na'ilah suka zo wucewa sai rike baki suka yi suna fa
in.

"Kunga autar Yadiko da Mama!" Murmushi nayi ina mai gaishe su, Yaransu da yake bana rabuwa da su, suna yawan shigo min haka yasa suka tawo wurina da gudu, Ya Tahir ya saka hannu a aljahun ya ciro kudi ya bawa Yaran, iyayen suka yi ta godiya tare da ni.

Bayan tafiyarsu ya kalle ni.

"Allah ya hadaki da mutane kirki!" Gyada kai nayi, ban ce kome ba daga haka ya kalle ni.

"Auta you are suffering." D'ago kai nayi ina kallonshi, murmushi nayi nace mishi.

"Abba yace duk lokacin da na kashe Aurena na nime wani uban!" Yadda nayi maganar a sanyayye, sannan na d'ago kai ina murmushi, murmushi yayi min ya ce min.

"Mu ai muna raye ba zamu tab'a barin haka ya faru ba." Shiga mota yayi yana d'aga min hannu, murmushi yayi min tare da jan motar ya bar kofar gidan, na juya ashe ya Hafiz yana tsaye, shiru nayi ashe shi yasa ya janyo ni kofar gida, kuma wani abu maganar kudin nan bai bar ranshi ba, ina isa bakin kofar ya mika min hannu.

"Wata nawa baki biya kudin haya ba!" Kallonshi nayi a hankali na ce mishi.

"Ai kayi sanadin da aka hana ni sana'ar balle kace na biya kudin haya!" Bai ce min kome ba sai da ya shiga cikin gidan ya wani taka min kafa sai da kashin kafar naji yadda yayi kara ya ce min.

"Sannu ba da gayya ba ne!" Yadda nayi zafin kamar an zare min raina haka nake jin ciwon haka nayi ta takawa har cikin dakina wanda ya ragani isa yayi maza ya dauki wayata yayi ta saka number check balance, amma bai ga kome sai wasu yan iska dari biyar da dubu daya, da yake account biyu ne da ni.

Haka ya gama dube dube a wayar tunda dama keypad ce, haushi ya kama shi ya wurga min wayar na dauki abina ina me ninke hijab dina, ganin sa gaske naki kula shi.

Sai ya daddume ni ya shiga
arin kwace ku
in ni kuwa naki, gani zai zai cutar da ni na gantsara mishi cizo wanda ya saka shi kara tare da shake min wuya kamar zai kashe ni.

Sai da ya ga na fara fita hayacina sannan ya sake ni.

Dakyar nake sauke numfashi, sannan ya kwashe kudin ya watsa min dubu biyar yayi gaba abinsa.

Hawaye ne ya zuba min in sha Allah na fita na fita kenan.

Ina kwance a wurin har aka kira sallah Magariba kafin na lallaba shiga ban daki nayi tsarki na zo nayi alwala na shiga dakin nayi sallah ina zaune.

A wurin har aka kira sallah isha na mike na gabatar tare da shafa'i da wutir, sannan na kwanta a wurin, idan na kyale ya Hafiz wata rana zai kashe ni.

Kwarai na gano kiyayya a cikin idanunshi.

Dama tun can Ya Hafiz bai sona ne?

Idan har haka ne tow meye amfanin zaman da shi.

Haka na kwana washi gari na shirya zuwa gidan suna, sai da na biya gidan Maman Na'ilah na amshi jakar kudin nan, bayan na cire mata itama kudin da ban saj nawa bane, na juya na fita tana ta min godiya, daga nan gidan Aunty Hindatu na fara zuwa ita tana unguwar Federal locals ne, nan na fara zuwa, tana ganina ta fara tambayata.

"Auta lafiya?" "Lafiya kenan!" Na shiga na zauna Mijinta Alhaji Mas'ud ya fito cikin shirin zuwa kasuwa.

"Matar roba kece a gidanmu!"gyada nayi, "Kiyi hakuri har kika kwanta ban samu zuwa ba na tafi umara ne amma ita wannan matar karfen bata gaya min ba sai da na dawo!" "Na gode Angon bogi!" Murmushi yayi ya ce min.

"Tow ayi min addu'a zan tafi kasuwa!" "Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya!" Muka fada ya fita Aunty Hindatu ta bishi har waje sai da ya fita ta dawo tana kallon yadda nake a takure wuri guda.

" Lafiya Lu'lu'a!?

" Kaina a sunkuye na ce mata.

" Na shirya rabu da shi!" Wani irin sujada tayi tare da ambaton Allah, ta rike hannuna.

" Da gaske!

" Hawaye na zuba min na ce mata.

" Eh!

" Na gyada kaina ina cizon bakina.

Wato ban tab'a jin kwarin gwiwa ba irin na yau sai da ta kira conference call baki
aya aka hadu ina jin su, tambaya daya suka yi min na shirya rabuwa da Hafiz Ali Umar Jama'are?

Na ce musu eh ma shirya.

Aunty Hindatu ta gaya musu na zo da kudi, da yadda za ayi da ku
in.

Murmushi Ya Ado yayi ya ce shi kenan.

" Baby girl get ready muna bayanki!

"
Haka muka gama muka tafi gidan sunan amma bamu tafi lokaci guda kowa da tafiyarsu, lokacin da muka isa gidan kowacce daban daban ya shiga.

Anan muka samu ana ta liyyafar, ina isowa Ya Tahir ya riko hannuna ya kai ni wurin abokansa abin mamaki har da Ya Hafiz a wurin wato don jaraba ya biyo ni, irin kallon da yake min na tuhuma da zargi yasa ni dauke kai, babyn aka kawo min Ya Tahir ya ce min.

"Ga takwara na miki!" Kurawa yarinyar idanu nayi hawaye na zuba taruwa a idanuna, na d'ago kai ina kallonshi hawaye na zuba min, wannan na gudu wannan na koro wannan, kasa magana nayi ina kallonshi.

"Takwara na miki!" A hankali nake shashekar kuka ina me rungume yarinayr har cikin raina nake jin kaunar yarinyar.

Haka Yan uwana suka taru ana ta taya ni murna ban haihu ba amma yan uwana sun min kara domin duk abinda ya dace nayi sai gashi sun yi min kome har da kayan barkatu.

Soyayyar da yan uwana suke min ya wuce tunanin mutum.

Haka na tashi na tafi wurin uwar jaririyan nayi ta kuka, ita kan dariya tayi min.

"Lulu Allah ya sani nafi ki farin cikin saka sunan Yarinyar nan, kuma taki ce har abada!" Haka nayi ta kuka a wurin kukan da na kasa yi shine nake yi ina yi ina kallon yarinyar, yadda nake kuka Aunty Hindatu ta ce a kyale ni, nayi kukan dama tun tuni ake son nayi ban yi ba, sai nayi har kaina ya fara ciwo, suka kai ni dakin Ya Tahir na kwanta, barci ya dauke ni mai karfi.

Sai wurin karfe biyu na farka zan yi sallah na ga bakona, ita mai jegon ta bani sabon pant da ledar pad, na gyara jikina na fita wurin yan uwa da ake ta hidimar bikin sunan, Aunty Hindatu bata gayawa sauran dangi ba, iyamu yan daki daya da dakin Yadiko aka san da zancen.

Wurin karfe shida nayi sallama na wuce gidan Aunty Hindatu.

Itama can ta dawo, ta fito min da kaya kala uku domin gobe da sassafe zan wuce Kaduna wurin Ya Almu.

Hafiz
Karfe takwas ya dawo, koda ya shigo ya g kofar dakin Lubnah a rufe tsaki yayi, yana tambayar Karimah.

"Yarinyar nan bata dawo ba ne?" "Ba ka bani sandar kiwonta ba fa!" "Ikon Allah!" Ya ce daga nan bai kara magana ba, haka har zuwa karfe tara na dawo babu labarin Lubnah, bai damu ba yasan yadda zai ji da ita gobe.. don haka yake shirya yadda zai cika Baban Bauchi.

Washi gari.

Asalin tashar Kaduna aka kai ni, wanda yake hanyar Jos, daga nan Aunty Hindatu bata bar wurin ba sai da ta ga motar ya tashi, sannan ta dawo gida.

Dama wayata na bari a wurinta, ta bani wani tsohon wayarta da layin duk tsoho ne, amma tana amfani da shi.

Haka yasa na kwantar da hankalina don ko na tafi da wayar Ya Hafiz zai iya amfani da kiran na dawo.

Karfe biyar biyu na rana na iso Kaduna, Ya Almu yazo ya dauke ni.

"Auta sannu da
ari, sannu Ubangiji yasa karshen wahalarki kenan!" "Amin Ya Allah!" Na fada a hankali, muka wuce gidansu da yake base na Sojojin sama.

Muna isa Matarshi Aunt Saliha,ta tarbe ni.

Ina zata saka ni ina zata ajiye ni.

Don farin ciki da jin dadi.

Haka nayi ta jin kamar alfarma aka min.

Nayi wanka aka bani abinci naci ka
an, sai kuma na fara jin kamar nayi wani kuskure.

Wurin karfe uku Aunty Hindatu ta kira shi tana gaya mishi yadda Ya Hafiz ya rikice yana bin gida gida yana niman inda nake.

Shiru nayi da Ya Almu yake gaya min yadda hankalin Ya Hafiz ya tashi ya rasa yadda zai cusa ranshi har Jama'are aka bincika ko ina can.

Gashi yau aka yi wani hatsari a hanyar Jama'aren hankalinsa yayi mugun tashi.

Sai jikina ya fara rawa na kasa zama ko na zauna zan tashi tsaye.
Chapter 19 · 0% Book details