← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 86

Sashe 84

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka aka fara azumi, azumi na da kwana biyu muka wuce Umara, ashe ta Bauchi Mama itama ta zo haka muka yi ta ibada tayi min addu'a kamar zata kara haifa na, wani jallabiya me tsadar gaske Mama ta saya mishi da agogon azurfa da zube, ta saya mishi da wani turare wanda ku
insa zai kai Naira dubu dari biyu, hidimar da tayi mishi kamar wani danta haushi suka bani har da kukana bata saya min ba, haka ta ha
a min a kayana, wai na kawo mishi haka nayi ta mita ina kuka, sallah saura kwana tara muka dawo, cike da farin ciki muka iso, kwana uku na dawo aiki yadda zaku san bana gabanshi, kallo
aya yayi min yayi ta wani cin magani.

Tsarabar Sarah da Taj, Sai na Jasminah da Yaranta.

Shi kuwa ko dabino ban bashi ba.

Uncle Auta kuwa da ya min barka da dawowa na bashi kyautar wani zoben azurfa da turare.

Wayyo Allah, ina wutar da za a saka ni.

Fushi sosai yayi, ya daina min magana sai dai Taj ya min Magana.

Ina sane nayi mishi wannan wulakancin.

Sallah saura kwana biyar aka bamu hutu kowa yayi Sallah, wannan shine karon farko da zan zo Bauchi sallah.

Sakonsa na wurina da Mama ta bani yaki zuwa gidanmu, ranar na kira Taj ya zo ya amsa na gaya mishi inji Mama ta turo mishi.

Bayan an sha ruwa Mama ta kira ni, "ke ce kika bashi number na ya kira sai godiya yake min, wato ke dai ba zaki bar halinki ba, sai yanzu kika bashi sakon?" "Mama daga shan ruwa zaki fara min fa
a." Murmushi tayi tana fa
in.

"Allah ya shirya ki!" Nan muka sha hira, ban san Ya aka yi yasan zamu je Bauchi sallah ba, koda yake ba mamaki Mama ta gaya mishi.

Haka yazo da katon jaka wai na kaiwa Mama kayan sallah da na azumi da bai mata.

Kallon kayan nayi na nad'e hannun a kirjina.

Lashe baki nayi nace mishi.

"Kayi hakuri ba zan tafi da kayan nan ba!" Na fada ina me juyawa zan bar wurin ya ce." Ai ba ke na bawa ba, wa Mama na ce a kai min idan ma baki ba ai shi san zai kai min!" Takaici ya sa na juya ina kallonshi amma kwarjininsa da cikar halittarsa ya sa ya cika min idanu.

Sunkuyar da kai nayi ina cizon bakina.

"Dauka ba naki ba ne!" Y fada yana shiga motarshi ya bar gidan nan wannan dan renin hankali ne wallahi, dauka nayi na tura mishi da sakon. *Don Allah wannan ya zama last da zaka kara kawo mata kaya because we are not money Morga, min iya da rufin asirinmu*
Daga haka na wurga da wayar ina hararan kayan kamar na rufe shi da duka.

Haka na wuni da takaici, washi gari muka nufi airport domin da wuri muke son shiga Bauchi, tunda Ya Umar yana hanyar Jos.

Abin ya matukar min dad'i sai dai me muna isa airport
in na hango shi.

Suka gaisa da Ya Ado a raina na ce *wannan kamar maye* wai ma ya aka yi wancan lokacin na iya biyewa shashancina na kula wannan mutumin, haushin kaina na ji sosai fa.

Da gayya na saka airpies a kunne na, har zuwa lokacin da muka tashi tafiya.

Ashe shima Gombe zai wuce, tab'e baki nayi har mu
ka bar lagos idanuna a rufe.

Karfe daya na rana muka sauka a Jos, muna isowa sallah muka yi a masallacin da yake gefen airport
in, muka yi sallah Aunty Raliyah ta kawo mana kayan lambu da fruit, daga nan muka yi sallama.

Bamu tsaya ko ina ba sai a nabardo muka sayi fura da nono, sannan muka wuce Bauchi.

Karfe hudu saura muka isa dutsen tanshi, na yi kewar Bauchi sai na zama kamar Bakuwa haka muka isa gidan, da yake cike da yan karban sadaka.

Mun samu tarba a wurin Yan uwana da suka zo shan ruwa tunda aka ce zan zo na ga gata sai da nayi kuka don farin ciki.

Abba ma ba yabo ba fallasa haka muka gaisa.

Ranar sai sha daya Yayuna suka bar gidan na kwana a bayan Mamana, cike da so da kauna nayi kewarta.

Lokacin da na tashi sahur na ga sakonshi. _Da fatan kun isa lafiya ya Mamana da Abba tare da Yadiko?

Nima na isa lafiya._ share text din naso yi sai na ji ban kyauta ba, kawai sai na tura mishi..*Alhamdulillahi kai ma ya naka tafiyar?

Da fatan ka isa lafiya,* can kamar minti
aya zuwa biyu sai ga sakonshi. _Masha Allah, baki ce min akan Mamana ba?_ wani iyayi da shishigi tura mishi nayi da ce. *Oops tana lafiya* daga haka na share wayar na cigaba da abinda nake, bayan na idar da sahur nayi Nafilla, sannan na zauna aka yi sallah asuba, kafin na kwanta ban tashi ba sai karfe daya, muka yi wanka ashe Aunty Zakiyah ta wuce gidanta da yake Ibrahim bako tare da kannenta maza biyu da mata uku, kiranta nayi a waya nace mata.

"Shine baki tashe n?"
"Ikon Allah Auta ta zo wurin Mamanta taya xan tashe ta, jinjira tana jin dumin Mama!" " Aunty Zakiyah gaya min magana mike fa a fakaice fa!

" Dariya tayi tana fa
in.

"Allah Yayanki ya ce a bar ki wurin Abba shi yasa ban tashe ki ba, kuma suna bukatar wani a kusa da su.

" Haka na jita, muka rabu na fito n taya su Mama aiki Abba yana tsakar gidan yana jin yadda Mama take waya da Turaki tana ta saka mishi albarka, ta ji dadin wannan sakon da ya aiko mata, bayan ta gama ta kalli Abba ta ce mishi." Mai gidanta na wurin aikin ta ne ya turo min sako!" Ina jin ta tana gaya mishi har da wani shadda ya turo bashi yace baya son kayan da sai da aka sabawa Allah sannan aka kawo ni.

"Eh fa haka ne, bayan sa
on Allah ya wuce na annobar da aka kawo muku a cikin zuri'a, in sha Allah taraba da yasin zamu cigaba saboda harshenku!" Inji Yadiko, Mama kan murmushi tayi tana fa
in."Ai shi kenan!

Zan turawa Yayana ya samu a mishi dinkin layya."
Bayan isha ta dauki turmin yadiko ya bata tare da sauran kyaututtukan da ya hada har da madara da milo, duk ta turawa Yadiko, kaya ne me tsada.

Washi gari ana gobe sallah aka nimo mana mai lalle ni da Yaran Jiddah da Ummu da aunty Zakiyah aka zo aka mana sallah da yake baki suna zuwa daga Jamaare su ne suka yi aikin kome mu kan ana mana lallen hannu da kafa ni kan ja aka min me kyau da
aukar idanu, a daren muka wuce gidan Aunty Hindatu aka mana saloon a can wurin karfe biyu na dare muka dawo.

Washi gari tun asuba muka tashi, muka tashi saboda Masallacin Malam Idris zamu bi.

Da wuri muka fita domin bakwai yake sallah idininsa, muna idarwa muka iso gida ta saman dutse, muna shigowa gidan aka sake shewa aka rungume juna, nan aka bude chapter yaushe gamo.

Kusan kowa yayi kewata, Aunty Munah tana azare sun zo itama zasu karaso Bauchi, haka muka yi ta farin ciki.

Har dare ana tare sai hoto ake, sai lokacin Mama ta kawo musu tsarabar da Turaki ya turo ni da shi, ta cirewa Yaranta kowa turmi turmi, dakin Yadiko ma ta cire musu, bayan tafiyarsu na shiga wurin Abba da aka ce yana kirana, kaina a sunkuye yayi shiru.

Kafin ya ce min.

"Shi abokin shaidancinki, aurenki zai yi?" Rike zuciyata nayi amma tabbas yadda Abba yake danganta Turaki da wasu irin kalmai yana saka ni jin wani irin yanayi, mutumin da ko hannuna bai taba rikewa ba, me yasa Abba yake yin haka ne?

Haka ya gama fadarshi iya hakuri nake bashi ina kara nutsuwar da kai na, har zuwa ya gama abinda yake sannan ya ce na je, lokacin da na koma daki Mama tayi tayi tasan me yake faruwa ban gaya mata ba.
-Washi gari.

Tun safe na ga Mama da Yadiko suna ta aiki kamar zasu yi wani abincin sallah bayan daga gidan Yayuna ake kawowa sallah da kwana biyu ake wunin gidanmu, haka yasa nayi ta mamaki.

Amma ban tambaya ba don yadda suke aikin cikin nishadi, na fahimci akwai wani abu.

Wurin karfe tara muna gama shirin tafiya kallon hawa da yake a g.r.a muke kallon, Ya Sani dasu Aunty Inna muna dauki wata sienna muka fita bayan Ya Ado ya turo kudi aka zuba a cikin motar.

Muka fita sai kudin da Ya Umar ya bamu, haka muka tafi da kular ruwa da kayan ciye-ciye, haka muka kutsa da kyar zuwa old GRA Bauchi daidai alhayat nan muka samu wuri har an fara wucewa.

Sanye nake da wata lace mint green wanda aka min dinki Bubu sai daurin da na kafa a kaina mayafina fari ne da takalmi da jakana, sai madubin da na saka.

Ruma Mai shadda muka hadu da ita ina tsaye da lema.

"Lubnah Shehu Umar?" Dariya muka saka, na isa inda take ina mai amsar Yaronta alamar sabon haihuwa ce.

"Mai shadda kece haka?

Kin zama Mama!" "Ke nan ce min zama wata yar 18yrs ba sai ni yar renin wayo!" Wata yar budurwa Yarta na gani tana mai gaishe ni, ta hado kan kannenta.

"Ruma beautiful familynki kenan?" Murmushi tayi tana fa
in.

" Kema ai naki suna hanya in sha Allah, ki ,zuba idanun suna nan tafe fa wallahi uku uku zaki ya dirke mata duk bayan shekara daya." Murmushi nayi amma nasan ni ai narasa wanan damar har abada.

Haka muka sha hira kafin ta wuce.

Sai bayan tafiyarta na nutsu sosai.

Ina son Yara, ina son Yara amma ni bani da rabon Yaran domin na gama da mahaifana.

Taya xan samu haihuwa ko nayi aure?

Ina ga Madadin na sakawa kaina damuwar auren gara na hakura na rike aikina, domin babu namiji da zai aure ne ba tare da ya karu da ni ba.

Tab'a ni Aunty Innah tayi na kalle ta.
Chapter 84 · 0% Book details