← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 86

Sashe 32

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Auta ki tafi ki ci abinci!" " Tow sai da safe."nace mata ina me kashe ki wayar, na nufi hanyar waje, suna ta hira sama-sama cikin nishadi da jin dadi, haka ma sauko na gaishe da Ya Ado da Aunty Zakiya, yaran suka gaishe ni yadda na amsa musu yasa suka fara kallon iyayen, har yanzu akwai rashin sabo a tare da ni, izuwa yanzu ban san yadda zan gyara kaina na fahimci mutanen da suke gefena ba, tsoro nake ji kada a kwana biyu su juya min baya.

A hankali na zauna Aunty Zakiya ta saka min abinci, ta ce min.

" A kara miki ne!

" Kallon abincin da ta zuba min nake ina tunanin.

"Auta lafiya?

Tana magana baki ce kome ba." "Abincin zata rage yayi yawa!" Na fada muryana yana rawa.

"A'a bai su yawa ba, kici kawai idan zaki kara sai a kara miki ba." Kalaman Ya Hafiz ne suka shiga yawo a kaina. _Jaka sai aikin ci ba haihuwa!

Dama a jaka ya dace ki zo ba a mace ba, jakar ma mara haihuwa_ da sauri na tura mata nace mata.

"Don Allah ki rage!" Haka ta rage rabin abincin, shima ban iya ci a gabansu ba, juya abincin nake ina kallon yadda suke ci, tashi Ya Ado yayi ya dauki plat din ya riko hannuna muka bar parlourn dakina ya mai da ni, sannan ya ajiye min abincin a gabana.

"Zauna ki ci!" Ba musu na fara ci ina kallon kofar da ya fita, kafin ya kawo min ruwa na cinye abincin kuma ban koshi ba, ajiye min ruwan yayi ya je ya karo abincin ya zo ya ajiye min.

"Bana son kina zama alone ne amma na fahimci kafin ki saba da mutane zaki dauki lokaci." Shiru nayi haka ya juya ya fita na zauna naci abincin sosai.

Daga nan na dawo hayacina na tashi na wanke hannuna, na tattara kayan na sauko da shi kasa.

Yaran suna parlourn babu wanda ya kula ni, ni tun kan su Yusrah tsoron yara nake, haka gidan Ya Tahir Yaransa basu hayaniya idan ina gidan.

Shiga kitchen nayi na ajiye kayan abincin.

"Hi" gabana ne ya fadi, na juya a hankali Princess ce, mika min hannu tayi ta ce min.

"Zamu iya zama abokai?" Yadda take kallona yasa na dan durkusa na ce mata.

"To!" Na mika mata hannu, kamar yadda ta mika min, sannan na sake hannunta na wuce hanyar sama.

Tunda na koma sallah isha nayi, na kwanta tunawa nayi na dauko magani na sha, sannan na kwanta a hankali.

Tunani mai zurfi nake a sannu sannu barci yayi gaba da ni, daga nan ban kara sanin me nake ciki.

Ya Ado
"Dr kina nufin ba zan samu ganin shi ba kenan?" Kallonshi tayi ta ce mishi.

"SAN baya gari ne, da yana nan da na gaya maka.

" Shiru yayi yana kallon laptop dinsa, "ina son na ga ta fara ganin likita duk da tana da maganin da take sha amma yana da kyau ta kara ganin wani likitan, zuciya tayi rauni akan Lulu, duk halin da take ciki mune muka jefata a cikinsa." " Ubangiji ya bata lafiya.

Ya bamu ikon kula da ita.

" " Amin Ya Allah!

" Ya fada yana cigaba da aikin da yake, tana gajiya ta kwanta ta barshi a wurin.

Ya Ado kasungurmin lauya ne, wanda idan har ka kawo case wurinsa.

Tow fa matukar kaina ne da gaskiya magana ya
are, bai cika amsar case
in da aka yi zalinci ba, haka yasa ya kara zama wani gwaska.

Wurin karfe biyu na dare, ya kashe laptop din.

Sannan ya shiga ban daki yayi uzurinsa ya fito, sannan ya ji kai bari ya leka Yaran da kuma Lubnah.

Haka ya leka dakin yara ya kara musu addu'a sannan ya wuce dakin Lubnah ya same tana shasheka tare da zabura, kamar zata farka sai motsi take, juyawa yayi ta fita ya jira Matarshi wacce tayi nisa a cikin barci haka suka shigo dakin tana hamma.

Zama tayi a gefen gadon tana shafa fuskar Lubnah.

"Ya Isa haka you safe Lubnah." Yadda take shafa kanta tare da magana a hankali, har ta bude idanu wanda suka yi ja saboda yadda take mafarki ganin Ya Ado a tsaye yasa ta razana tare da fashe da wani irin kuka.

K'amk'ame Aunty Zakiya nayi tare da boye fuskana jikinta, jikina yana rawa.

Abin ne da ciwo irin wannan sai anyi da gaske kafin mutum ya manta da shi.

Matsowa yayi na kara k'amk'ame ta.

"Ka tafi zan zauna da ita har ta koma!" Fita yayi jikinshi a sanyayye, yana jin wani irin yanayi yana saukar mishi.

Ina jikin Aunty Zakiya har wani lokaci.

" Ya isa haka, tashi ki yi alwala sai ki yi sallah kin ji." Haka na mike na shiga ban daki nayi alwala sannan na fito na samu ta shimfida min abin sallah.

Wannan sai da ta ga na fara sallah, sannan ta bar dakin bayan na idar ta shigo ta same ni a wurin da nayi sallah na kwanta ina barci, janyo bargo tayi ta lullube ni, ban san me yasa tayi haka ba.. ko kuma tana tunanin idan na farka ba zan iya komawa ba ne, haka yasa na cigaba da barci a wurin.

Duk yadda naso na cire Ya Hafiz na kasa, domin ko yaya na kwanta sai nayi mafarkin Ya Hafiz da irin azabar da yake shirin min, haka yasa na kasa yarda da kaina balle kowa.

Sannan zuciyata tana raya min Hafiz sai zo gare ni.

Washi gari da sassafe na farka na fara yin Sallah, wanka na yi sannan na duba jakata na dauki magani na sha, turo kofar aka yi na kalli me shigowa.

"Lubnah!" Ya Ado ya kira sunana, "Na'am!" Na amsa mishi, shigowa yayi da mug a hannunsa ya janyo stool ya zauna, yana me mika min kofin.

Amsa nayi ina kallonshi.

" Na gode!" Na furta a hankali, zuba maganin nayi a bakina na sha a ruwan tea din.

Sannan na rike kofin ina kallon kofin.

"Naso muje ganin likita yau!" Kafe shi nayi da idanu, kafin na cigaba da kurban tea din ya cigaba da cewa.

"Amma likitan baya nan, gashi zamu tafi aiki zaki iya zama a cikin gidan nan ke daya ko?" Gyada kai nayi ina ajiye kofin a gefe guda.......
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: SHA TARA
"Me yasa sai na ga likitan to?" Na tambaye shi a hankali, ina dan karce farcen hannuna, ban damu da zafin da nake ji ba.

Ni kaina ban san lokacin da na zama haka ba.

"Saboda ki samu nutswa da kwanciyar hankali zaki ga likitan
walwa." "Na haukace ne?" Kalaman Ya Hafiz ne suka dawo min. *Ki dawo gare ni, ni daya ne ba zan cigaba da miki kallon abar tausayi kuma mahaukaciya ba!

Amma duk wanda zai zauna dake kallon mahaukaciya zai na miki* da sauri na kalli Ya Ado, "kana min kallon mahaukaciya ce?" "A'a ko daya bana miki kallon haka."
Kin yarda nayi na fashe da kuka, Ya Hafiz yayi gaskiya tun a Bauchi nake kallon yadda kowa yake min kallon tausayi ko kallon wance rayuwarta ya
are, haka nayi ta kuka tabbas ina jin ciwo amma ban san yadda zan fitar da zafin ba.

Dakyar ya rarrashe ni sannan ya fita, kasancewar maganin akwai na barci tunda na kwanta har suka fita ban sani ba, sai farkawa nayi na ga yar karama not a gefen tiren abincin.. *Idan kin farka ki karya sai ki sauko akwai me aiki tana zuwa mana aiki sunanta Yemi tana nan Please ki karya kin ji*
SAN Adamu U.U Jama'are.

A hankali na wanke bakina na zo na karya lokacin karfe daya saura, sannan nayi wanka na sauya kaya na fito parlourn kasa, mai aikin ce tana ta aiki a kitchen din.

Lekata nayi ma ga tana faman kwashe abinci a cikin kular.

"Good Afternoon Ma!" Ta gaishe ni, gyada kai nayi ina amsa mata a hankali.

Barin kofar nayi na dawo parlourn na zauna a kujeran, lekowa tayi ta ga ina zaune amma na kurawa tv parlourn idanun kuma ba a kunna ba, tana fitowa ta kunna.

Sannan ta koma wurin karfe biyu ta fito tana fadin..

"Zan koma sai an jima!" Gyada mata kai nayi, ta fita na koma na kwanta sai lokacin na nufi zan kwanta na manta ana kashe tv don haka na saka kai zan fita daga tv aka ce.

"Kin zata zaki iya gudu ne?" Da harshen turanci.

Domin film din da turanci ake yi amma sai tunanin da nake na Ya Hafiz ya juye min irin muryansa.

"Nace kin zata zaki iya guduwa ne?

Kin dauka idan kika gudu ba zan iya samo ki bane?

" Yadda na tsaya jikina yana rawa na kasa juyawa gani nake kamar yana bayana.

Hawaye ne ya shiga zubo min a hankali na ji motsin takunshi har har gabana.Wani irin rikicewa nayi tare da zubewa a kasa ina jin kamar zuciyata zata fita.

Kukan da nake naji ya makale sakamakon ce min da yayi.

"Shiiiiii!" Hadiye yawun bakina nayi tare da rintsa idanuna, ina me saka hannu bibbiyu na kare fuskata.

"Ya isa haka, bar kuka na gaya miki duk inda kika shiga zan binciko ai, ya isa bar kukan nan ko sai na mare ki ne?" Ya fada da karfi, ja da baya bayi ya mike tare da zare belt din jikin wandonsa, ya d'aga belt din zai zuga min na fasa wata irin kara me firgitawa, wanda yayi daidai da shigowar Ya Ado yayi mantawa ne ya dawo gidan.

Ganin halin da nake ciki yasa shi isowa gare ni, duk na firgita na fita hayancina sai ihu nake, yayi maza ya rungume ni.

"Ya Isa Lubnah ya isa haka.

Gani nan Yaya Adamu ne, ya isa bar tsoron haka gani nan a tare da ke.

" Kara rungume shi nayi tare da kifa kaina a gefen kafad'arshi, ina fa
in." Ya nimo ni, wallahi na ganshi."
Wayarshi ya cire daga aljuhun rigarshi ya shiga kira da shi.

" Doctor ba wani likita ne?" Daga can ta ce mishi.

" Yanzu nake son kiranka ya dawo!" " Ok gamu nan zuwa!
Chapter 32 · 0% Book details