← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 86

Sashe 78

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me aka miki zaki bar aikin?" Kashe wayar nayi baki
aya, na sauke ajiyar zuciya ina kallon wayar da nayi switch up dinsa, ina zaune a wurin Adil ya shigo da gudu yana haki.

"Aunty Lulu ki zo kin yi bako!"zare idanun nayi na ce mishi.

"Baba gaya min waye?" "Wannan wanda Abba ya ce oganki ne!" "Shi kenan!" Na fada a raina, kafin na saka jalbab na sauko kasa, ina jin wani abu yana yawo a kaina.

Wucewa kitchen nayi na dauko kunun aya da sauran breakfast din da aka yi na dumama masa ce fa sauce din kodar saniya, na kawo mishi a hankali na jera mishi.

Sannan na ce mishi "ka kaci!" Ba musu ya saka sannu ya fara cin masar da yake miyar da dan yaji tari ya fara na bude mishi kunun aya na zuba mishi ya sha, sannan ya kalle ni, kafin ya ajiye ya cigaba da cin masar, har zuwa lokacin bai ce min uffan ba, nima kuma ban ce mishi ba kaina a sunkuye, nayi mamakin da yaci abincin sosai, ya ce min ya koshi, na tattara kayan na kai kitchen, na dawo na zauna a can gefe.

Shiru muka yi kafin ya ce min.

"Gobe ki dawo aiki!" "Tow Allah ya kai mu!" "Amin Ya Allah!" Daga haka ya mike zai fita ya ce min.

"Yaranki nawa?

Mijinki yana ina?" Bai tsaya jiran amsata ba yayi gaba abinsa, wannan dan renin hankalin, shi kuma haka yake rayuwa kamar me aljanu.

Bayan tafiyarshi Ya Ado ya fara zolayata, "wato Lubna baki da mutunci, don kina son ganinsa shine kika kira shi." "Ni wallahi ba kiran shi nayi ba!" Na fada ina tura baki, dariya yayi suka yi ta tsokanata.

Washi gari.

Na same shi a office din ne.

Ga sabbin ma'aikata, da gaske koran wadancan yayi.

Gaisawa muka yi da wata ina ga irin kabilun arewan ko yar Kaduna ko yar Jos, sai dai ban gama tantance ta ba ta ce min.

"Sunana Sarah daga Gombe
aramar hukumar kaltungo." Murmushi nayi nace mata.

"Lubabatu daga Bauchi, karamar hukumar Jama'are." "Allah sarki akwai yar uwata Ayrah tana sama wurin CEO!" Gyada kai nayi nace mata.

"Da kyau bari na isa office din!" Na wuce sama, kofar dama a rufe take, sai da na ajiye kaina na kunna table tap, na shiga office.

Matar da na hango tafi Sarah a shekaru, cikin girmamawa na gaishe ta sama sama ta amsa sannan na gaishe ya amsa yana aiki na fara zayyano mishi abinda yake da su a a yau, ban gama ba sai ga Tajudeen........
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 55
Murmushi nayi na juya ina kallonshi, a hankali na ce mishi.

"Nayi kewarka!" Murmushi ya sakar min ya wuce gaban Masifatu ya ajiye document
in da ya kawo, sai lokacin na mai da hankali kanshi ashe ya shaka, wani irin kallon rashin mutunci yake min, yayi shiru rubutu yake a laptop ya rufe ta da karfi tare da mikewa ya fita ya bar ni nan tsaye, anya mutumin nan bai da aljanu?

Fitowa nayi na same shi yana magana da Taj, wucewa nayi dan zauna ya ce min.

"Kin gama report din ne?" Kallonshi nayi cikin mamaki yanzu fa ya fito a office din, ban gama ba sannan ya zo yana tambayar na gama nima share shi nayi kamar ban ji ba, mamaki ya kama shi.

Na kuwa hade rai domin ga irin kallon da matar take min na kusa da shi.

"Ina jiranki a mota!" Ya saka kai ya fita sai da na gama abinda zan na taso na nufi kasa, don ma na bashi haushi stair zan bi ba zan bi elevator ba, kuma a hankali nake sauka ya jima bai kore ni ba.

Sai da na shafe minti goma kafin na iso, na hango Taj yana ta leke ta ina xan fito.

"Gani ta nan!" Na fada ina nufar hanyar waje, ina zuwa na same shi ya cika kamar balloon, sai kallon agogon hannunsa yake, hango matar nan da nayi sai na koma gaba na zauna kuma ai dama gaba nake zama, muka dauki hanyar inda zamu.

"Sir maganar zuwa Japan din yana nan ne?" Shiru yayi yana kallon table tap din da Taj ya mika mishi.

"Kamfanin Rivers sun tara kayan sosai, dole sai an je da su Japan." Shiru yayi sannan ya ce mishi.

"Na Kano ma haka, Abuja babu kayan gaskiya." "Ka shirya tafiyar har da sakatariya." Jin an ambace ni yasa na juya na kalli Taj," tafiya ina?

Har da ni kuma?" " Eh ai aikinki har da tafiye-tafiye!" Yana sane ya fadi haka ya ji ko ya zata fuskanci Mijinta.

Hadiye yawu yayi yana kin zuciyarshi kamar aka lugude a kai, wani irin yanayi yake ji a kanshi, yana tsoron kada ta ce tana da miji.

"Amma gaskiya ba zai yiwu ba, domin ko ka tambayi iznin zuwa ba zaa a bar ni ba, ka duba ni mace ce kuma Bahaushiya idan nace zan yi tafiya wata
asa da wani namijin ai abin ba zai making sense ba, ina ga a cire sunana a bar ni anan, abinda ya shafi gida Nigeria.

"
"Idan don Mijinki ne, ki bada passport
insa sai a tafi da shi, but i need you!

" Daga haka ya fita a motar domin har mun iso bankin UBA, gaba yayi na fito airah ta ja min tsaki, kallona Taj yayi yana fa
in.

"Kina sa'ar Oga, tunda har da mijinki zaku tafi." "Ni fa ba zan bishi ba." Haka na cigaba da tafiya, ya juya yana kallon yadda nake bawa Taj amsa, tsaki yayi yarinya karamar da ya sani a wancan shekarun bata da wannan kula kowa, amma wannan da aurenta ma, sakewa take da kowa shi yaushe zai zama dan iska irin Mijinta, idan da shi ne Mijinta, zai ga yadda zata kula kowa domin a banza zai ta sare kan mutane ne, tsaki yayi ya cigaba da tafiya.

Har inda aka yi zaman muka isa sannan muka fita inda aka ajiye kayan, na shiga ina rubuta abubuwan da Taj yake gaya min, har muka gama na juya kenan kawai muka ci karo da shi, kamar xan fadi ya riko hannuna, ya tsayar da ni.

Ya harare ni cikin masifa ya ce min.

"Idan Mijinki baya kishinki, ke ba zaki iya kishin kanki ba ne?

Kin zauna sai wangale hakora kike da wani?

Ki sani ba zaki janyo min masifa a kamfanina ba, idan aurenki aurenki idan kuma kule-kule ne sai ki bar min aikin na gaya miki, kuma xan gayawa SAN yasan abinda kike aikatawa." Irin kallon da nake mishi na tausayi ne, domin baki
aya masifarshi ta rufe mishi idanun kawai fada yake kamar zai dake ni, wani abu da yake bani mamaki shi fa idan yana masifar ma baka tab'a jin tashin muryan sai dai ayi ta maganar cikin wuya da baki, irin kada a ji yana fada, tattara kayan nayi na rab'a gefenshi na wuce, kafin na isa wurin motar na shiga Taj na min magana na ki kula shi, shima da yazo ya zauna a motar muka bar bankin muna hanya amma naki kula Taj, ganin haka yasa shi cewa Taj.

"Ka kai mu Chinese dish." "Ok sir!" Bayan mun dauki hanya naji muryan Airah.

"Turaki ni ban ga wani aikin da sakatariyarka take ba, maganar tafiya kuwa sai na yi replace dinta." Duk muna jinta, ni sai na fi kowa murna cikin farin ciki na ce mata..

"Alhamdulillahi Ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, kai Masha Allah." Ganin yadda na nuna farin cikina tare da musu addu'a, ya cika da mamaki yana ta ta
a table tap amma zuciyarshi kamar ta dirko daga kirjinsa, har sai da ya kai hannu ya danne kirjin, ko da muka iso shagon ita da Taj ya tura shagon.

Tunda na ji ya ce ita da ita da Taj su je su fita su amso na fahimci zai hau masifa ne, dauko airpies na saka s kunnena na kunna wayata.

"Cire!" Ya fada a fusace, na cire daga kunnen na juya ina kallon titi raina yana b'aci, "tafiya da ke xan yi idan kin so ki ajiye aiki yau!" Daga haka ya cigaba da aikinsa.

Haka suka dawo muka bar shagon, koda muka iso office mika min abincin Taj yayi na ce mishi.

"Ina azumi!" "Yau wacce rana kenan?" Banza nayi mishi ban kara kula shi ba.

Har aka tashi na wuce gida, ina isowa gida abin mamaki na same shi har ya rigani zuwa gidan, na samu suna magana da Ya Ado.

Wuce su nayi na tafi cikin gidan.

Ban san tafiyarshi ba, sai ganin Ya Ado nayi ya zauna yana kallona.

"Kuna da tafiya ne a kamfaninku?" "Eh amma ni nace ba zan samu zuwa ba, saboda." "Zaki je, abu daya nake so dake ki kama kanki, sannan ki rike mutuncinki.

Kada ki manta Allah yana ganinki, kada ganin bamu nan yasa ki fada wani irin yanayi, ki sani Allah yana kallonki." Idanuna ne suka cika da kwalla, haka yayi ta min nasiha duk da ni na nuna bana son zuwa amma ya ado ya ce na je, haka na cigaba da jin wannan abin haushin, ranar juma'a ba wani zama muka yi ba, aka tashi yau kan shi da kasan yazo kamfanin don haka da aka tashi, na fito zan je Garej ya tsaya tare da cewa.

"Shigo!" Kamar ba zan shiga ba, sai kuma na shiga na ja belt na daura, muka cigaba da tafiya.

Wannan dan renin hankalin ba abinda ya ce min, har muka isa gida na cire belt din xan fita ya ce min.

"Are you angry?" Share nayi na bar shi a wajen ai tun da naje ya ga yadda fuskata take masifar ha
e, haka yasa shi fahimtar raina a b'ace yake, wai kuma don renin hankali yana tambayata wai ina jin haushi ne?

Ranar asabar, ina tsaka da barci domin duk jikina a gajiye nake tun daren jiya Aunty Zakiyah ta ce zata shiga asibiti.

Wurin karfe goma, mai aikin ta ce nazo ina da baki, saukowa nayi shine da su Ilham.

Cike da mamaki yaran suka taso da gudu na sauko nima na rungume su.
Chapter 78 · 0% Book details