Sashe 80
Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Duk iya kwanakin da kika yi da shi bai isa ba sai kin biyo shi?" Ban fahimci me take nufi ba, don haka kallo daya na mata na dauke kai.
Na cigaba da kallon garin sai da ta hauro inda nake zata tab'a ni na rike hannunta.
"Kul kada na ji kada na gani, ni ba sa'ar yinli ba ne don haka ba zaki saka hannunki a jikina ba." Na ture hannunta, "karuwa me bin namijin da bai damu da ita ba." Wannan maganar ya min ciwo, murmushi nayi nace mata.
"Ke ya kamata na kira haka tunda zuwan da kika ce kina so ya nuna baya yin zuwanki sai ni.
Yana da kyau na kira ki da Uwar karuwai ni wancan abin ko a kafa aka daura kin shi bana yinsa." Na wuce abina, ita ta damu da namiji har take fa
a akanshi, amma ni da na sha wuta a hannun da namiji har wani abin burgewa ce da su da zan damu kaina.
Mtseew, na ja tsaki.
Ashe ina barin wurin kai
arata tayi wurinsa, ban san ya suka kare ba.
Da asuba muka hadu da ita a nan airport.
Ni ban shiga harkanta ba, kuma ban wani damu da ita ba.
Ban san me ya gaya mata ba amma tabbas naga ta shiga hankalinta, amma tana harara ta idan muka hada ido ba mistake.
Mun iso Nigeria kai tsaye, da misalin karfe sha biyu saura na dare, kallona yayi ya ce min.
"Ko zaki kwana a gidan Uncle Auta idan gari." Ban barshi ya kai aya ba nace mishi.
"A'a bamu yi haka da kai ba, kawai kai ni gida!" Na fada ina kallon gefe tsaki tayi haka muka kira Uncle Auta ya zo, ya dauke ni, ni da ita muna baya.
Shi da Uncle Auta suna gaba, har kofar gidan Ya ado aka ajiye ni sai da ya buga gidan Ya gaisa da Ya Ado, sannan ya ce mishi.
"Ga amanar da ka bani!" Murmushi yayi ya ce mishi.
"Na gode sosai da wannan abin da ka yi na yarda kai me amana ne!" Ya ji dadi, ni kan dakin kasa na wuce ka kwanta, tunda nayi sallah asuba na koma na kwanta sai sha biyu na tashi da mugun mura na kwaso sanyin can, ai muryata ta dishe, mura sosai da zazza
i na kwanta.
Ban sani ba ko Ya Ado ne ya gaya mishi, bayan isha sai gashi da kayan dubayya, ya zo duba ni.
Kaya niki-niki sai da abin ya dasawa Aunty Zakiyah ayar tambaya.
Ganin haka yasa bayan tafiyar naki magana duk yadda taso nayi magana naki, sai ta zuba min idanu.
Bauchi
Jikin Abba da sauki sai dai ya daina zuwa kasuwa, koda yake kasuwar ma yanzu suna ce domin shagonsa ya mutu murus na atamfofi, sauran da yake ba a hannun Hafiz suke ba yasa kome yake tafiya normal, wani abu da Abba yayi shine raba hannunsa da yayi, shine kawai Allah bai bada ikon karya shi ba, amma shagon sai da aka rufe domin babu kome a cikin shagon kamar wacce aka yi mata yasa.
Ya nima da lafiyarsa da karfinsa amma yau an wayi gari kome ya kare shi.
A haka shima Baba Malam ya kwanta rashin lafiya, sosai fa ya kwanta jinya.
Duk da wannan yanayin da yake ciki sai da ya kai ya kawo yana fama da jinya amma yana sakawa a kira Abba ya tuna mishi lallai ko bayan ransa ne a tabbatar na koma gidan Hafiz, shi Abba ba lafiyar ce da shi ba, amma a haka ya tafi jama'are ya samu tashin hankalin da ya wuce tunanina domin Hafiz ya zo ya gaya musu karya da gaskiya, lokacin da suka dawo daga lagos, bai magana ba kuma Ya ado bai fadawa iyaye mazan abinda ya faru ba, Yadiko ce ta sani, ai kuwa rako su Baba Malam gida domin inda Baban Jama'are zai makale an rufe gidan da yake shirin rikewa Ya Umar ya ce an saka a kasuwa saboda zasu saka kaya a shago, wannan ya kara bawa Hafiz daman zuduma sharri son ransa.
Wannan abin yayi bala'in d'agawa Abba hankali wanda ya haifar da saukar jininsa har ya nemi faduwa, don ma Allah ya so da Sani suka tafi.. haka suka yi ta kula da shi, wato cewa Hafiz yayi shi duk abinda zasu mishi zai karba amma su sani ba zai tab'a gudun Lubnah da take karuwanci a Lagos ba, haka yasa har Rufa'i sai da ya bada shaidar Lubnah karuwanci take har da hotonta suka nuna wanda take motsa jiki a cikin gidan.
Wannan abin yayiwa kowa zafi Mama da bata da hakuri har Jama'are ta isa aka yi uwa ubanka, wannan abin ya tsaya mata a rai, tayi kuka har ta godewa Allah, Hafiz ya ki rabuwa da Lubnah duk inda ya zauna sai ya zage ya ce shi zai rufa mata asiri, koda ciwo zata kwaso zai zauna da ita a haka, wannan abin ya saka aka manta da itin cutar da yayiwa Lubnah aka fara ganin
arinsa da yadda ya ganta kuma zai zauna d
a ita, sharri kuwa ai dan aike ne.
Haka Abba ya dawo Bauchi da ciwo hade da bakin ciki, Yadiko ta ce mishi.
"Alhaji ai baka ci ta kuka ba, Maman Lubnah ce da kuka domin ita aka cuta kuma Allah sai ya saka mata, wannan zalinci har ina kuma kaima Hafiz bai barka ba."
Wannan abin ya taru ya mishi yawa, ga bakin ciki ga takaicin Hafiz.
Lagos
Kwana uku a tsakanin wanda yayi daidai da Monday na koma aiki, yadda naga ana kallona yasa na dan tsargu.
Ashe gulma aka yi me zafi.
Wanda Sarah ce ta iya bani labarin wai ai Airah ta ce mata a daki daya muka sauka sannan mun ta yawon dare da sheke ayarmu.
Kallonta nayi tare da dariya na ce mata.
"Duk abinda aka fada a kaina da wanda na sani da wanda ban sani ba na yafe, idan kin gadama ki yarda idan baki gadama ba ki watsar.
Ni ban zo kamfanin nan don shirme ba, su da suka ga zasu iya Bismillah."
Haka lamarin ya cigaba da tafiya, ba dad'i ga gidan Jaridu da suka sako shi a gaba da kafe hotonshi a magazine ana cewa yana sheke ayarsa da sakatariyarsa, kanwar wani babban lauya a nan lagos, har kamfanin ake zuwa leken asiri wannan yasa na ajiye aikin na tafi hutu don ma Allah yasa saura sati biyu a fara azumi.
Kanshi ya dauki wuta haka yayi ta min masifa akan me zan dauki hutu bayan ba ni daya ba ce a cikin wannan tashin hankalin har dashi, kashe wayar nayi na tattara na bar lagos da goyan bayan Ya Ado na tafi rives wurin Aunty Munah hutu, a can na yi sati biyu, Ya ado da fari ya zata ko ina sonshi ne nake wannan abin ni kuwa ba wannan tunanin kawai na gaji da matsalar kamfaninsa ne, wata na biyu kenan a kamfanin amma kamar don ni aka bude kamfanin satin biyu cib Ya Ado yazo da kanshi wai na koma gida Mama tazo.
Haka muka iso gidan cike da farin ciki, na ga Mama na ji dadi sosai.
Kusan kwana muka yi a tare muna hira, washi muna karyawa ya jifo min tambayar da tasa na kusan kwarewa.
"Ance kina aiki da wani namiji wanda ake ganinku tare waye shi?" "Mama oga na ne na wurin aiki." "Sonki yake yi ne?" "Amma aiki ya ha
a mu fa, babu wani maganar so ni yanzu babu aure a gabana." Shiru tayi kafin ta ce min.
"Babu aure a gabanki taya aka yi har wannan hotunan suka Bayyana a idanun duniya."
Ta watsa min hoton, wani irin razana nayi tare da rufe bakina.
Zan yi magana ta dakatar da ni.
"Bana son jin kome a bakinki.
Ki ajiye aikin ki hada kayanki mu koma Bauchi.."
**
"Na gaya maka bata bukatarka, wannan gayen da ka daka a kanta wanan ranar shine Mijinta, har yau yana nan bai rabu da ita ba, idan akwai abinda kake yi da ita tow ka daina ita din matar aure ce." Inji Ubaid.
Cike da mamaki yake kallon Ubaid cikin sanyin murya ya ce mishi.
" Zargina kake?
" Gaskiya na gaya maka, ka rabu da ita."
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 57
Murmushi Turaki yayi mishi tare da mikewa, ya nufe shi ture shi yayi har suka fito waje.
"Idan na kara ganinka, a rayuwata ko a rayuwar lubnah, sai na kashe ka!" Ya tura shi waje.
"Akan mace zaka rabu da ni?
Akan mace zaka lalata alakarmu?" "Dama can Alakar ta lalace, ai dama can alakar babu ita, dama can babu wata kauna ko soyayya da yake tsakaninmu, stop pretending like kana tare da ni bayan na san kai da sauran yan gidan so kuke su kashe ni da goyan bayanka, idan ma Lubnah tana da aure zan cigaba da tafiya ba zan tsaya ba, idan bata da aure zan tsaya na ga me take bukata a rayuwata.
Ba kai ba Mujitafa idan ya ce zai nunawa Lubnah yatsa sai na karya shi balle kai karan kade miya, fita kada na kara ganin munafikar fuskarka." Cike da mamaki Ubaid yake kallon Turaki da ya kore shi.
"Korana kayi fa?
Korana kayi Turaki?" Murmushin takaici ya sake mishi tare da cewa, "abinda yafi haka ma zan maka fita!" Ya daka mishi tsawa.
Girgiza kai yayi ya fita, duk fuskar da aka bibiya shine bai kyautata Alakarshi da turaki ba, ya san yayi kuskure amma duk lokacin da yayi da wani katobarar kara nisanta kanshi da Turaki yake ya rasa me yasa yake jin haushin Yarinyar.
Tsare Mama nayi da idanu, na rasa abinda zan fada.
Amma sai na ji akan kaina Mama bata yi kuskure ba, ta yiwu wani abu aka kintsa mata, duk yadda aka yi da wani abu.
"Mama Bauchi kuma?" Yadda nayi maganar sanyin murya sai ta kuma sauko da kanta ta ce min.