Sashe 6
Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda har ta kai ya saka wannan gidan a kasuwa." Dafe kirjina nayi cikin wani irin bugawa da yake kamar zuciyata zata dirko daga kirjina, "haba Hajiya me yasa zaki gaya mata?
Me yasa zaki bari ta sani?
Idan wani abu ne na amince zan fuskanci hukuma akan laifina gara na fusk." Rufe mishi baki nayi ina girgiza kai.
" A'a don Allah kada ka ce haka, ba zaka sayar da gidan nan ba!
"
" Au ka ji ba, saboda gidanta ne, gidan da Ubanta ya saya maku, da ace gidanka ne wani ya isa ya hana ne?
" Maganganun Hajiya suka kara birkita min
walwa sai kaina ya fara juyawa, na fita da gudu na nufi dakina.
Bayan fitar Lulu suka kwashe da dariya, Hafiz ya ce "mahaukaciyar banza yanzu zata dauko jikinta yana rawa.
Amma kun taimaka min." Tijjani da ya cika bakinsa da abinci ya ce musu.
"Amma maganar gaskiya, ya kamata ka kyale yarinyar nan, iya adalci ta maka tayi maka kome, idan ka cigaba da abinda kuke akwai lokacin da kome zai lalace wallahi." "Dalla yi min shiru, ba gara shi ba kai ina sai dai na rike ka na rike matarka." Inji Hajiya, "Kyale shi Hajiya ai yadda Lubnah take kaf duniya babu me iya juya ta sama da ni, sannan idan kana ganin zata iya rayuwa babu ni zan gaya mata a gabanka zaka ji me xata ce, kuyi shiru gata nan zuwa!"
A hankali na shigo parlourn ba kome a tare da ni, suka zuba min idanu.
" Ya Hafiz ko zaka zo!
" Shiru yayi kafin ya mike yana dafe kirjinsa da yake nuna min alamar yana mishi ciwo.
" Don Allah riki ni, jiri nake ji." Haka na matsa jikinshi, muka fito har zuwa parlourna, ya zauna a dogon kujera ya kishingida yana lumshe idanunshi.
Dakin na wuce na dauko kwatin yan kunayena,.
Na ajiye mishi sannan na koma gefe na zauna.
"Ban san me ya faru ba, amma ga shi ka.
Biya abinda ake binka." Kallona yayi kafin ya dauke kai yana dafe kirjinsa.
"Lubnah bar dukiyarki kada yan uwanki su ji, su kara himmar raba mu, ki barshi kawai Allah yana nan." "Kudin ne ba zai iya ba?" Hawaye ne ya zubo mishi ya ce min.
"Wato wani
addara ne ya fada min, a shagon Baban Bauchi.
Gashi saura kwana uku na hada kudin." "Baban Bauchi bai sani ba ne?" Dafe kanshi yayi da hannu bibbiyu yana nishi.
Ban san lokacin da na kara rudewa ba, na riko hannunshi tare da janyo shi jikina ina tab'a shi.
"Ya Hafiz ko mu tafi asibiti ne?
Innalillahi wainnalihir rajoun!
Ya Hafiz lafiya?" Yadda ya mike min kamar gawa yasa na kara kidimewa, garin juyawa na ci tuntube da center table din parlona, ban damu da zafin ba amma har cikin raina na ji ciwon sai dai halin da Ya Hafiz yake ciki yasa na manta da ciwon da naci, sai na kasa gane kukan da xan yi na ciwon ne ko kuma na halin da ya Hafiz yake ciki ne?
Baki
aya na shiga tashin hankali, ban san adadin soyayyar da nake yiwa ya Hafiz ba, haka yasa na kara birkice na rungume shi, ina kuka sosai, domin zuciyata ta karye ainun.
Bana son naga abinda zai d'aga mishi hankali, a daren muka kai shi asibitin ni'ima aka bashi kulawar da ta dace har da karin ruwa, Tijjani muka bari a can asibitin muka dawo gida, Hajiya sai kuka take, tana shashekar duk sai naji na damu da kai, dakyar muka dawo tambari inda Unguwar yake, na tura kan motata zuwa cikin gidan, dama motar da yake hawa tawa ce, tunda ya sayar da tashi kwanakin baya ya dauki tawa yana amfani da shi.
Koda muka fito Hajiyarsu ta ce min.
"Lubabatu dama nace ko." kallonta nayi ina son naji me zata ce, sai ta ce min.
"Dama kada ki gayawa Iyayenki halin da ake ciki domin idan kika gaya musu abin ba zai yi dadi ba, idan babanku na Jama'are yayi cewa ga abinda ya faru.
Ki zama mace mai rufawa Mijinta asiri haka zai saka Allah ya rufa miki ta yadda baki zata ba." Gyada kai nayi ina fa
in..
"in sha Allah Hajiyarmu!" Na fita daga motar na nufi cikin gidan, na rufe bangarena parlourn na zauna nayi ta tunani kafin na shiga na kwanta, karfe biyu da arba'in da biyar na farka sallah dare, ina yi ina gayawa Allah kuka ta da matsalata, nayi tawassali da sunayen Allah tsarkaka, Allah ba zai tab'a wulakantamu ba.
Ina zaune har aka yi sallah asuba, sannan na yi raka'atu fijir, ina idarwa na daura da sallah asuba, sannan na fita na fere doya na daura a wuta, sannan na daura ruwan tea, a hankali nake bin kome ina lissafin yadda xan shawo kan matsalar ya Hafiz, wurin karfe bakwai sai ga Tijjani yazo daukar mota zai je dauko shi, "kenan ba sai an saka muku abincin ba zaku dawo ?" "Eh!" Ya ce ya fita, kafin bakwai da rabi, na hada abincin Yusrah na kai mata, na tashe ta na mata wanka, sannan na shiryata tana ihu, sai ga Hajiya ta fito.
" Wai me kike mata ne?
" " Wanka na mata Hajiya zan shiryata ne!
" " Wanka ko mugunta?
Ke fa muguwa ce ba mamaki ruwan da zafi kika yi ta kona mara mutunci, ke baki haihu ba amma salon muguntarki yafi karfinki wallahi ki ji tsoron Allah!
" Kwalla ne ya cika min idanu, na gama shiryata na kawo mata abin karyawanta, tana sha tana kukan rashin mutunci.
" Ni tea din ya min zafi, yana kona min baki kaka yana kona min baki!
" " Ai dama nasan muguwa zata kashe ki ne!
" Hajiya ta fada tana daukar tea din ta kurba, sai zare idanun tayi tana fa
in.
" Takwara ai ba wani zafi, yadda yayi sanyin nan ma kulle miki ciki zai yi!
" Kamar nayi kuka haka na bata doya ta furza min a fuska.
" Ni kin cika yaji!
" Wani irin bakin ciki naji ya cika min rai, na ce mata..
"ayya Yusra me yasa kike min haka ne?
Ki ci don Allah!" Kamar nayi kuka nayi maganar, sai tura baki tayi tana fa
in.
"Ba zanci ba." "Ai ba dole ba ne sai ta ci a barta haka don Allah!" Haka na hakura na barta, na kuma wuce na barsu na kawowa su Hajiya nasu don ta fara min ihun ita yunwa take ji taliyar jiya bai rike ta ba.
Haka na kawo abin karyawan, tana ci tana fa
in.
"Kin iya girki amma salon mugunta irin naki sai kin azabtar da mutane!" Kaina a sunkuye na barta na riko hannun Yusra na kai ta makaranta, har lokacin ban ga Karima ba, sai da na kaita makarantar na juyo zan dawo gida, na hango su Ya Hafiz, na zata zasu tsaya su dauke ni ne, a'a sai suka yi tafiyarsu.
Haka ba karasa gidan a gajiya na shiga na hada mishi abin karyawa yana zaune a parlourna, sai da yayi wanka ya dawo ya zauna yana karyawa hajiyarsa ta shigo ita da Tijjani da Yasir da har lokacin bai yi wanka ba.
"Lulu waye zai yiwa Yasir wanka ne ?" Ya Hafiz ya tambaye ni, "ni ce!" Na fada ina daukar yaron da ya fara tsalla ihu, haka yayi ta ihu har kaina ta fara wani irin juyawa, gashi ya cika kashi a pamper dinsa, haka na wanke na mishi wanka na fito na shirya shi, garin shirya Yaron nan na kara fama tuntube na, wani irin kuka ne ya so kwace min, haka na daure na kai shi waje na koma daki na shiga ban daki na fashe da kuka, don sai yanzu na lura da farcen kafana ya fashe, baka hawaye yake zuba min ina jin kamar na mutu da bakin ciki, haka na gasa kafar na fito nayi wanka, na shirya cikin material.
Bayan na saka kwalli da man baki na fito, na samu sauran abin karyawan nawa da yake kitchen Hajiya da Karima sun dauka sun cinye, kitchen din na koma na dafa indomie da kwai, na zauna a kitchen din naci, sannan na fito na samu suna ta magana.
Shi kuma yana zaune yana jin su, can aka buga gidan na zata Almajirin da yake min aiki ne, na koma daki tare da dauko Hijab na saka sannan na fita na bude gidan, wasu magidanta ne guda biyu, suka shigo gidan.
"Alhaji Hafiz yana nan?" "Eh yana cikin bari na mishi magana,!" Na fada tare da nufar cikin gidan, "tow mun gode" haka suka jira na koma parlourn na ce mishi.
"Ya Hafiz kana da baki a waje" "sun iso kenan?" Ya fada yana yatsina fuska.
"Yaya kasan likita ya ce kada ka saka damuwa a ranka domin zuciyarka tana dab da bugawa!"
Lumshe idanunshi yayi ya bude a kaina yana min alama da idanu wato naji dai.
Sunkuyar da kai nayi ya fita, shi da Tijjani, Hajiya ta zauna tana ta zuba kwadayi tana bawa Karima labarin yadda ta sha wahala akan Ya Hafiz ni dai na wuce kitchen na wanke kayan da nayi amfani da shi, sai gashi ya shigo kitchen din, "Ina takardun gidan nan?" "Yana dakina!" "Ko zaki bani aron gidan na sayar idan na biya bashin da ake bina zan!" Rufe mishi bakinsa nayi da hannuna, ya sumbaci hannun yana cire bakinshi a hannun ya tako har jikin dogon deeper freeze na, ya ha
a ni da jikin freeze din ya shiga sumbatar goshina da manyan kumataina.
Abu daya nake bukata a gare shi, shine soyayya amma na rasa ni dai a bangarena bai rasa soyayyar da nake mishi ba, haka ya gigita ni, daidai shigowar Karima kitchen din ta kawo kayan da suka ci abinci da shi, ganin halin da muke ciki yasa ta jan tsaki tayi waje, sake ni yayi ya ce min.