← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 86

Sashe 58

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah sarki Abbana Ubangiji ya bashi lafiya." "Ke kashe wayar kada ki fara min kuka!" Haka na kashe wayar ina jin wani iri a raina, karfe shida na yamma ta dawo gidan ita da Ya Ado don Aunty ta dawo da wuri tayi abinci ta kai, naso na bita ta ce min.

Na zauna saboda Yara.

Tana kaiwa bata jima ba sai gata nan.

Tow dai gasu Mama ma sun dawo, Kallonsu nayi na tafi na rungume ta.

"Mama ya Abba da jikin?" "Da sauki matsa min na je nayi isha,." Ta fada tana wucewa haka na bi bayanta ina fa
in.

"Mama zasu min dariya!" "Yo ba sai na musu rashin mutunci ba!" Haka dai ta amsa min anan ta shiga ban daki tayi Alwala da wanka sannan ta fito ya sauya kaya na kawo mata abinci, tana idar da sallah ta fara cin abincin, ni kan gasashen kaza Ya Ado ya kawo mana, na fara ci ina kallonta.

Tashi nayi tafi kitchen na hada Yorghurt fruit na dawo dakin ina sha.

"Yanzu haka rayuwarki zata koma ba abinci mai taimakawa sai irin wannan?" "Mama kibar da ba aso zan yi!" Gyada kai tayi tana kallon yadda na ci ka
an na namar sauran kuwa na barshi sai Yorghurt din na shanye, muka cigaba da hira..

"Lubnah!" Kallonta nayi don yadda ta kira sunan yasa na fahimci maganar ba na wasa ba ne.

"Kin san yadda kome yake tafiya ko?" Gyada kai nayi ta cigaba da cewa.

"Yanzu na ji Adamu yana cewa zai nima miki aiki babu wani ne da yake nimanki?" Wani irin tsoro ne ya lullube ni har nake ji kamar an lullube ni da danyen nama.

" Ko har yanzu tsoron yana nan!" Bakina yana rawa na rufe shi, domin sai naji kamar xan yi amai ne, a hankali jikina ya
auki wani irin rawa.

Ai kuwa da sauri na shiga ban daki sai da nayi aman abincin da na ci, na dawo na kishingida bata kara min magana ba, ta yi shiru da zancen ranar a wurinta na kwana.

Washi gari Yaran gidan da gulma wai.

" Aunty Lulu yau ta kwana a wuri Mamanta." Sosa kai nayi na ce musu.

"Oh dai Mamana ce!" Haka na raka su har inda school
insu yake, daga can kuma zasu wuce islamiyya don an sauya musu na yamma nan, idan suka dawo zamu yi karatun dare da su, har da home work.

Bayan na karya su Mama suna ta shirin tafiya Asibiti, Mama take gaya min ai tun asuban fari Ya Ado ya kaiwa Tahir abinci, ya dawo ya tafi aiki.

Ina can ina baza kafasiti a wurin Uwata.

Karfe goma Aunty Nuratu ta zo muka tafi asibitin da ita, daga waje na tsaya ina kallonshi da yake ta barci.. hawaye ne ya zubo min haka na koma na zauna ina kallon ina share hawayen da yake zubo min, fitowa suka yi a lokacin Ya Tahir ya iso yana min tsiya.

"Who is this fine lady?

Daga wata kasar take anya ba daga Somalia ba ce!" "Ya Tahir zaka fara ko?" "No na ga wata hadaddiyar baby doll ce, mai kalar Somalias." Murmushi nayi ya kai maganin sannan ya fito nan aka yi ta gaisawa da raha.

"Kafaya kin ga yarinyar nan ko a hanya na hadu da ita dai dai na juya nace kamar na santa!" "Allah ya ganar da kai Attahiru." "Mama da dai kin ce Dahiru zai fi gane yana tsokanata!" "Mama don Allah kada ki biye mata!"?

Haka muka yi ta hira, wurin karfe biyu sai gashi ya je ya sayo abinci, ni nawa kusan rabi ganye sai fried rice da grilled fish, sai soda drink.

Ya ajiye min yana fa
in.

"Nasan ba zaki hada kifi da madara ba, shi yasa na amso miki soda!" Da yake an kebe dakin mutum daya ne, kuma maganar gaskiya a can amenity muke akwai parlourn da family zasu zauna, kuma abin dad'i babu al'umma sosai a wurin haka yasa na sake naci abincin, wanda a lokacin ya lura da yadda nake cin ganye ya ce min.

"Ganye yafi kara lafiya kenan?" "Eh shi shinkafar akwai starch a cikinsa, shi kuma yana bin jini ne!" Matsa lemon tsami nayi akan abincin da kuma kan kifin, "shi kuma na meye?" "Yana narka da kitse da maiko!" "Sodar fa?" "Ita tana hana ciki cika ya kumbura, ruwan da na fara sha shi zai hana ni cin abincin kamar yadda baa so!" Jinjina kai yake sai a lokacin Mama ta ce min.

" Tow idan kika auri talaka fa?" Murmushi nayi nace mata, "Alayawu, kafi Egu, tafasa, bawon kabeji.

Lemo da gwaiba ba arasa su a gidan talaka, rama da yakuwa duk suna da amfani zanci ai babu inda Allah baya kai mutum."
"Yanzu bakya cin kome fa!" " Eh duk wani abu me starch bana sonshi, saboda akwai wata
waya da nayi tasha bude tsoka take sai mutum ya bude kamar an hura shi, har da shi a karin kibar jikina." " Allah ya kyauta!" " Amin Ya Allah!

" Daga haka muka cigaba da hira kar yamma sallah yake tashinmu, wurin karfe biyar sai ga Ya Ado da fruit da abincin dare, nan aka sake bude hira anan na ji sun ce ashe Rufa'i da su Aunty Hindatu da Aunty Innah zasu zo.

Shi Ya Tahir zai koma, sai Ya Sani yazo.

Idan Allah yana sonka da arziki sai ba ka ikon yiwa Yaranka hidima a kananun shekarunsu da zarar sun girma su biya wannan abin da ka yi musu.

Wannan abinda ake kashewa babu kwandalar kowa Ya Ado ne yake a cikin aljuhunsa abu daya yace ba zai dauki nauyin kawo kowa ba.

Su kuma da yake sun saka ransu zasu so suka ce ya huta, muna isowa gida na ga sakon River State ya iso doya ce manya manya.

Kamar yadda nake zaton akwai wani abu da yake faruwa yadda na ga Ya ado da Ya Tahir tattaunawa, ban sani ba amma ko Mama basu bari ta sani ba.

Da muka dawo ina kwance a dogon kujerar parlourn ina kallon wani yoroba film da yake zuwana nima na zama jikar oduduwa, ina son film dinsu musamman irin na kauye na zamanin baya, yana nuna yadda suke kare martabarsu da kimar kabilarsu.

"Lulu!" Tashi nayi ina amsawa, "kin san wannan kwayar?" Kallonsa nayi kafin nace mishi.

"A ina ka samu?" Gabana yana faduwa, "Kin san shi kenan?" "Eh!" Na fada idanuna yana kawo ruwa, ba dai shima Abba ya fada irin matsalar da nake ciki ba ne.

"A ina kika san shi?" "A wurin Ya Hafiz!" Daga haka ya maida aljuhunsa, ni kuwa na fashe da kuka, bai gaya min kome ba.

Amma na ji a raina akwai wani abu.

"Ya Ado mai ke faruwa?

Ka gaya min don Allah!" "Ba kome kawai bincike muke!" Duk yadda naso yayi magana yaki, "ki yi shiru kada Mama ta san me yake faruwa zan tafi Bauchi ranar Monday, idan na dawo dan miki bayani!" Haka ya Ado ya bar ni a dame.

Kamar yadda ya ce kuwa haka ce ta faru, ranar Monday ya wuce Bauchi.

Sai dai zuwan shi Bauchi bai haifar da
a mai ido ba, domin anyi wani irin tashin hankali ne akan maganin Baban Jama'are ya ce shi ya kaiwa Abba yayinda yan uwanmu baki
aya aka zargi Ya Hafiz amma kiri-kiri mutumin nan ya wanke danshi, sannan suka ce ko da basu da arzikin Jirgin sama zasu zo su ga dan uwansa.

Karshe haka Goggo Alti ta kashe case
in, amma don goyan bayan sun goyi bayan Hafiz har da cewa ai kafin suyi yunkurin kai Abba lagos waye yake kula da shi, Baba Malam tsohon munafuki har da cewa a gaya min na dawo dakina na daina yawon gantali da karuwanci.

"In sha Allah Ubangiji ya
are Lubnah wannan fatar sai dai ka ganshi a cikin wasu jikokin da kafi so!" Inji Yadiko, kai anyi gurmi Goggo Alti ce kawai bata yi magana ba, tace ita bata ga laifin Yaran Baban Bauchi ba, da gaskiyarsu, haka suka bar zancen washi gari shi da su Aunty Hindatu da Aunty Innah suka bar Bauchi har da Rufa'i aka tawo jos daga Jos suka hadu da Aunty Raliyah suka biyo jirgi, sai tsiya suke ta yiwa Rufa'i wai Allah ya kira shi lagos, amma yana da rabon zuwa lagos.

Da yake shima akwai baki tuni ya kare kanshi.

Hafiz
Ya razana yadda aka fahimci shi yake bawa Baban Bauchi magani tow meye dalilinsa?

Amma haka suka bar zancen shi babban damuwarsa ya ga Lubnah in sha Allah duk ranar da ya ganta ko tana so ko bata so sai ya kwanta da ita, domin a yanzu da yake nan babu wata mace da take tare da shi, ko ya dauko maganar aure za a lalata mishi, ga Baban Jama'are da ya dawo Bauchi shima ya dawo shagon
an uwansa, hmm wani abu da Yaran Baban Bauchi basu sani ba shine ana ta murkushe kudin shago domin kuwa na karamin barna Hafiz yake yi ba.

Wanda haka da Baban Bauchi ya d'ago ne yayi sanadin da Hafiz ya fara dirka mishi magani.
(Wash hannuna
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 39
Ganin yadda lokaci guda asirinsa ya nime tonuwa ne Baban Jama'are ya saka shi a gaba da tambayar me ya faru, sanin cewa Babanshi yana tare da shi amma sai ya kasa fa
a mishi gaskiya ya ce musu.

"Kawai don sun tsane ni ne, amma me nayi musu da zasu ji haushi bayan ni nake kula musu da mahaifinsu da suka yi watsa da shi, meye ban shi ba.

Me kuma bana mishi kawai ban san me na musu suka tsane ni ba ne." Wannan magana sai yayi tasiri a ran Uban Hafiz ya cigaba da cewa.
Chapter 58 · 0% Book details