← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 86

Sashe 54

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan yana da sau
i kuma yana da fa'ida sosai.
* Gudu Ko Gudun Tsalle: Idan za ki iya, ki dinga yin gudu ko ki yi 'skipping' (tsallen igiya) don
ona Kalori da yawa.
* Yi Motsa Jiki Akai-Akai: Ki maida shi wani
angare na rayuwarki, ko da sau uku (3) ne a mako.
3.

Shan Ruwa
* Yawaita Shan Ruwa: Shan ruwa kafin cin abinci yana taimakawa wajen rage yawan abincin da za ki ci.

Ruwa yana da matu
ar muhimmanci ga lafiyar jiki.
4.

Kula da Barci
* Samun Isasshen Barci: Rashin isasshen barci na iya canza sinadaran jikinki wa
anda ke sarrafa yunwa da koshi, hakan kuma na iya sa ki ci abinci fiye da yadda ya kamata.

Ki tabbatar kina samun barci mai kyau na awanni 7 zuwa 8 kowace rana.

Abincin da Ya Kamata Ki Dinga Ci
Ga wasu misalai na abincin da zai taimaka miki wajen rage kiba:
Nau'in Abinci | Abincin Da Ya Dace Dalili
Ganyaye | Alayyahu, kubewa, kabewa, latas (Lettuce), kabeji (Cabbage) | Suna cike da sinadarai kuma suna da
arancin Kalori.

'Ya'yan Itace Tuffa, lemu, abarba, kankana, ayaba (ka
an) | Masu zaki na halitta, suna da Fiber.

Protein | Kwai (Boiled/Gasashe), Kifi, Nono marar mai (Yogurt), Wake/Gya
a, Naman Kaza (Chicken Breast) | Yana sa
i da ciki na dogon lokaci, yana rage sha'awar cin abinci.

Abinci Mai Fiber | Hatsi (Oats), Dambu, Gurasa (Whole Grain Bread), Rogo (idan ba mai yawa ba) Yana taimakawa wajen narkewar abinci da sau
i a ciki.

Muhimmin Bayani:
"Ki nemi shawarar likita ko kwararre kan abinci (Dietitian) kafin ki fara wani tsari mai tsanani.

Za su iya duba lafiyarki su ba ki shawarar da ta dace da ke."
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 35
" In sha Allah!" Haka na mike ya ce min, "Lubnah!" " Na'am!

" Na amsa mishi, ki duba time table dinmu, sai ko zabi ranakun da kike so, sai ki nime kayan da zaki na amfani da su." "In sha Allah!" Sannan na fita sai da na leka Aunty Nuratu Kafaya, na mata sallama akan gobe laraba zan fara zuwa ranar Saturday.

Haka na koma gida na samu Ya Ado na mike mishi takardan ya ce mu shirya mu fita, haka muka fita dukka gidan muka je wani super market anan Ikeja, sannan ya kai mu wani shagon sayar da kayan kwallon, ya saya min kayan da zan na fita zuwa Exercise da sassafe da kuma wanda zan na sakawa zuwa Gym din, haka ya saya mana har da Yaran da su kansu iyayen muka dawo.

Kamar yadda Ya Ado ya kawo kayan Aunty Zakiyah ta amsa ita ta fara nuna min yadda ko bata nan zan iya dafawa.

A ranar dai ban ci abinci dare ba, sai ruwan tea da fruit da sha.

Washi gari da safe ya Ado ya cika min water bottle da ruwa ya tashe ni muka fita.

Ana sallah asuba muka fita bamu dawo gidan ba sai shiga da arba'in, wanka muka yi na sha nikakken ruwan fruit, sannan na kwanta.

Ban tashi ba sai karfe goma, ina fitowa na samu, kunun tsamiya, da faten wake da yaji ganyen alayayu, sai agada, sai da na sha ruwa kafin na karya, ina zaune a parlourn aka yi knocking, Mai aiki ra bude kaya aka kawo, a kwali.

Suka shigo da shi Ya Ado yana bayansu.

Zuwa yayi nuna inda za a saka sannan ya koma wurin aikinsa.

Washi gari ya kama juma'a, shima sai da muka zaga unguwarmu sannan na dawo, kayan da aka kawo machine ne na Exercise, Ya Ado yana dawowa daren jiya ya ha
a ya gwada aiki da shi a daren jiya.

A ranar bayan sun fita nima kusan a kai na wuni, dadare kuwa abincinsu suka ci ni kuma na ci nawa tuwon alkama zalla miyar ayoyo, daga nan kuma na sha fruit na kwanta, ranar asabar karfe goma na tafi Gym, sugar kuwa tuni na yi bye bye da shi, wunin ranar Yorghurt na sha daga kuma sai ya rike min ciki.

Karfe biyu na bar gym din zuwa gida yau nayi rayuwa da ban tab'a yi ba, sai nake gani kamar mafarki.

Ina typing har na iso Unguwarmu, na karasa gida, a harabar gidan na hango Ya Umar wani murmushi ne ya kwace min na isa gare shi, ya dan rungume yana fa
in..

"Auta manya an zama yan gari.

Daga Gym ko?" Gyada kai nayi ya ce min.

"Shiga bari na gama waya na shigo." A parlourn na samu Mamana, wani ihu da nayi na isa wurinta da gudu na rungume ta, tana buga bayana.

"Sannu Autana, sannu yar jinjirana!

Ai tunda suka ce ba zaki zo biki ba nace ban isa ba, zan zo na ganki kada na mutu ban ga autana ba!" "Mama me yasa kike kiran mutuwa?

Mama me kika kawo min?

Mama ina Yadiko?" "Suna lafiya tana ta shirin bikin Sani!" "Allah sarki!" Na ji dadi sallah ya tashe mu na ja ta sama, tayi ta mita ita bata son sama, ai kuwa tunda ta hauro tace ba isa da ciwon kafa ba, karshe Abinci ma sama aka kawo mata, ni kuwa dad'i kamar na nutse kasa, tun a daren na gayawa Nasiba ta gayawa Mamanta Mamana tazo daga Bauchi.

Kwana muka yi da Mama muna hira tana bani labarin abinda ya faru, hakuri nayi ta bata, karshe nayi barci na barta tunda na fara Exercise barci ya daina min wahalar yi.

Washi gari Lahadi sai ga Aunty Nuratu Kafaya, ita da Mijinta, Mama ta ji dadi nima na ji dadi gashi an hadu ana ta hiran arzikin, sai la'asar Mijinta ya zo ya dauke ta.

Koda na zauna ina cikin ganye Mamaki Mama take ta kasa hakuri ta ce.

"Wannan wacce irin rayuwa ce?

Yarinyar da rayuwa da ganye ita ba akuya ba ita ba tsutsa ba, Auta dole aka miki ne?" "A'a yana cikin kayan karin lafiya ne, idan ina ce kibar zata ragu ko ta tafi baki
aya." "Aiho yanzu na fahimci yadda lamarin yake.

Allah ya kara lafiya shi yasa idan na zoma zan ta dafa miki zogale ina shanyawa da rama da yakuwa." Haka Aunty Zakiyah tayi ta mana dariya, satin Mama biyu ta koma Bauchi ta bar ni da kewarta sai waya kawai muke.

Bikin saura wata gudu muka fara jarabawa, na kara mai da hankali sosai sai fa muka sha wuta na tsawon wata guda sannan muka samu hutu, rayuwa tana cike da darasi na musamman Ya Ado da Aunty Zakiyah sun tafi, ni kuma na cigaba da kula da kaina, da taimakon Aunty Nuratu Kafaya, sati daya suka yi wanda aka sha biki da karamin gurmi aka dawo aka bamu labarin wai Yan uwa Ya Hafiz da Yan uwanmu ana ta habaici an tura ni karuwanci suna jiran sakamakon bariki, shine fa Yadiko ta rufe Aunty Nana Asma'u da fada ta ce mata.

"Har kina da bakin magana?

Karuwanci ai ya kare tunda tana gindinku!"
Rigima sosai a gefe guda Matar Hafiz itama ta kashe auren ne ko yana lilo oho amma dai ana ta rigima tace tunda ta aure shi ita bata gamsuwa, hakuri take da shi.

Aka ce Abba kamar yayi hauka yayi ta fada yana rarrashin Hafiz, wannan ya karawa Hafiz wani irin tashin hankali, yayi ta kuka yana rokon Abba ya dawo mishi da Lubnah shi yasa kaf duniya babu Macen da zata iya rufa mishi asiri kamar Lubnah, yadda ya shiga damuwa sosai Abba shima jininsa yayi ta hawa kafin a gama bikin nan sai da ya kwanta a asibiti sau biyu.

Abu fa ba dad'i sai gashi har Abba da kanshi wai ya je wurin Mama yana rokon arziki ta dawo da Lubnah, ai kuwa da Abba da Ya Hafiz Mama ta ce sai ta kai su kotu ta ji Uban da suke bukata da Lubnah.

HAFIZ
Don shi kanshi bai kawo a ransa Lubnah ba zata zo ba, saboda yadda ya santa da Sani, amma wani ikon Allah bata zo ba ya kuma kudira a ransa da ta zo sai ya san yadda yayi dawo gare shi yadda ba zata kara barin Bauchi ba sai da izninsa amma dai gashi bata zo ba abin ya bashi haushi, ga Nana da ta gudu ta fasa auren.

Gashi ya ga hoton Lubnah a wayar Rufa'i da yake zolayar Aunty Zakiyah ta dauke mishi First love dinsa wato Lubnan kasancewar dan Goggo Alti ne, yana jin su yayi kamar baya wurin yana ganin lokacin da ya bashi number Lubnah da kuma hotonta.

Bai nuna zallamarsa ba sai da washi gari ana hira ya ce Rufa'i ya bashi aron wayarshi, zai yi abu ne ai kuwa yana amsa ya binciko number Lubnah wanda Rufa'i ya saka mata bazawarata Lubnah, sai hotonta da ya tura kusan kala goma tayi shi da gym outfits, wani baki da ratsin pink yayi azabar kyau ga kanta da ta saka wata hula me kyau gargasar gaban goshinta sun kara fitar da kyanta da ya boya behind kibar ya fara fitowa, wani murmushi tayi, daya kuma ta fitar da harshe waje kamar tana gwalo, wani kuma tana kan abin motsa jiki na gidan daga ita sai riga da wando ta tufke gashin kanta, wani irin gigicewa Hafiz yayi kamar zai zauce.

Bai ta
a kawowa a ransa zata dawo kamar da ba.

Wannan abin ya d'aga mishi hankali wani hotonta kuwa wani yatsina fuska tayi tana dariya, alamar magana ake mata tayi haka sai kuma ita da yaran, wani kuma a makaranta.

Zufa ke karyo masa yana ji ina zai iya ganinta yasan yana ganinta zata fit hayacinta ta nemi dawo mishi, haka ya mai da wayarwa Rufa'i sannan ya koma gidansa yana kallon Yaranshi da suka ci abinci suka koshi, Hajiya tana gidan ita fa Fido.

Zuba mishi idanun tayi ta ce mishi.

"Duk akan matsiyaciyar yar nan ne?" "A'a Hajiya Lubnah na gani!" Ya cire mata hoton ta gwalalo idanun waje kamar tsohuwar mayya tana fa
in.

"Ina ka samo ta don Allah dama yarinyar nan zata dawo kamar da?" Murmushi yayi ya ce mata.
Chapter 54 · 0% Book details