Sashe 59
Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan sun tsane ni saboda Lubnah har yau Lubnah matata ce tunda ba ni na sake ta, kuma ban amince da sakin ga har yanzu ina son Matata." Yadda yake maganar a dame yasa Uban shima ya shiga damuwa, ya tafi dakin da Baba Malam yake ya gaya mishi, nan dai suka kara kulla wata munafuncin zasu zo lagos su ga halin da Abban yake ciki su gaya mishi abinda Yaransa suke zargin Hafiz da shi.
Wannan kuwa ya yiwa Hafiz dad'i, wanda ya kai har cikin ransa yaso ya biyo su.
Amma suka hana shi, da yake sun san al'amarin na kudi ne, basu fara zuwa da batun kudin jirgi ba, can bypass suka nufa anan suka biya kudin mota dubu sha bakwai daga Bauchi to lagos, sannan suka dawo idan bar aka samu fasinjoji zasu tafi, a Hajiya da ta ji labarin abinda ya faru bata yi kasa a gwiwa ta kira Malaminta ta gaya masa.
Abin da ya gaya ya, ba karamin dadi ya mata ba, ta kuma ta ji a ranta idan har Lubnah zata dawo rayuwar d'anta bata ki tayi kome a kai ba, wannan abin ya saka ta kara tura ku
i.
Sai dai shima ai ya boye mata gaskiya ya barta da duhun zuciya.
Bayan haka ita kanta tasan yaudarar kanta take amma da yake ta sauka akan hanyar da ya dace kyaleta kawai ta dace ayi ta ji a jikinta.
****
Lokacin da su Aunty Hindatu suka iso sai da suka fara biyawa asibiti kayansu aka kawo, ina kan injin motsa jiki nayi zufa shakaf kunnena ina sauraren karatun Alqur'ani, suka turo kofar.
Zuba min idanun suka yi kasancewar na basu baya.
A hankali Aunty Innah ta lallabo sai da ta zo kusa da ni na ji an tab'a ni, da sauri na juya ina ganinta ba fasa ihu, tare da rungume ta.
Da sauri na koma wurin Aunty Munah da Aunty Raliyah, sai Aunty Hindatu da ita kan har da daukata.
"Auta kece haka kika koma fine lady haka ashe da gaske Tahir yake da yace mana, wallahi kuka ga auta sai kin rantse ba ita ba ce, yarinyar nan ta kara kyau dole idan Hafiz ta ganta ya kusan mutuwa." Murmushi nayi ina kallonsu na shiga kitchen na dauko musu ruwa da kayan abinci.
"Kun yi sallah ne?" "Omo ku ji yadda take magana kamar ba lulunmu ba!" Inji Aunty Munah, "kai Aunty Munah Hausar ma dabance da taku;" "kwarai da gaske baki ji yadda kike maganar a ganyance!" "Ni din nake yanga." "Wallahi Innah har da wani kalar shagwaba irin na Ajebo." Dariya suka bani na haura sama da gudu na sauya kayana, "Jama'a ku ga yadda take gudu kamar dama can ta saba da zuba gudu!" Inji Aunty Raliyah, murmushi Aunty Hindatu take tana mai share kwalla da yake shirin sauka mata.
"Kamar ba yarinyar nan ba ce ta kusan haukacewa, yau ku ga yadda ta koma?" Hawaye ya zubo mata, duk sai suka koma tuno abinda ya faru.
Ni dai watsa rywa nayi na sauya kaya sannan na fito kafin nan sai da na kara auna tsawona, na ga dai na sauka ajiyar zuciya na sauke na sauko sanye da riga da zani na atamfa, ina zuwa na zauna a gefensu har mun fara hira na mike na hado fruit salad, na zo na zauna ina sha ina kallonsu, murmushi nake.
"Yan mata babu bazawari ne?" Kwarewa nayi na fara tari Aunty Hindatu ta make Innah da tayi maganar.
"Ke dai baki da girma sai na jikinki yaushe ta samu lafiyar da za'a fara maganar aure?" Inji Aunty Munah, "kyale ta mana Lulu take your time, duk abinda ya zo maka mai kyau ko mara kyau daga Allah ne, kada ki yi rushing a hankali Mijinki zai zo miki." Ji nayi fruit din ya hau min kai, na ajiye shi ina kallon tv.
"Ya Abba da jikin?" "Da sauki tunda gashi nan yana gane kowa ."
Murmushi nayi na ce musu.
"Allah ya bashi lafiya yasa zakkar jiki ne." "Amin Ya Allah!" "Ya batun aikinki yaushe zaki fara?" Tura baki nayi nace mata.
"Dukkanku aikin gwamnati kuke ya ado ya nima min aikin kamfanin ni wallahi tsoron aikin kamfani nake kada sai ka sake jiki a kore ka!" Murmushi Aunty Raliyah tayi tana kallon yadda nake magana.
"Auta kin ga yadda kika yi kyau da maganar nan, asalin kin fito yan mata babu wnada zai yarda kin tab'a aure, like how you look beautiful and charming, auta gaya min me ye sirrin!" Rufe fuskana nayi ina dariya, " bude na ga beautiful lady din da take gabana, wallahi kamar na sace ki Yar nan!
" "Innah dube ta fa, yadda kika san irin yan 23 uku nan koda yake yanzu wasu daga cikin sa'oinki suke aure dubi yadda ta samu natsuwa da kwanciyar hankali." Yanzu maganar Wasim da Aunty Nuratu Kafaya ya dawo min daga lokacin da kike tsaya da kafarki a lokacin kowa zai soki." Murmushi nayi haka suka ci abinci, sannan suka shiga ciki suka yi wanka da hutawa la'asar tana yi muka shirya baki
aya zuwa Asibitin, tunda Rufa'i ya ganni ya rike baki.
" Adamu yarinyar nan sakata kuka yi a injin amma?
Ke Lubnah gaya min wanke ki aka yi a injin ko?" Dama can na san halins sai haka bai wani dame ni ba, haka muka yi ta hira na leka Abba yana barci.
" Shi barci kullum yake yi ne?" Murmushi tayi tana fa
in.
" Eh yana farkawa har ya ci abinci ma, tow jininsa da yake yawan sauka ake son a iya sarrafa shi." "Allah ya bashi lafiya!" Kuka sai na fara kuka idan har wani abu ya sami Abba bai saka min albarka a rayuwata ba, ba zan yi kyakyawar karshe ba.
Kukan da nake yi ne ya dami Mama ta ja hannuna muka fita.
Kusan yadda abin ya tashi hankalina.
"Tow meye na kuka?" "Mama idan Abba bai yafe min ba, rayuwata zata lalace domin ina jin a raina ni ce sanadin wannan ciwon nashi." Kura min idanun tayi tana jin wani irin abu a ranta.
"Wani ya zarge ki da cewa ke ce sillar ciwonsa ne?" Cikin shashekar kuka na bude baki xan yi magana tura min kwakwa tayi a bakina.
"Ya isa haka, ba ke ce sanadin ciwonsa ba haka kuma ba zaki tab'a zama sanadin wani ba, ina da yakinin cewa Ubangiji ya amsa min addu'ata akanki, don haka ki daina kuka akan abinda baki da ikon sawa ko hanawa, kada ki manta Mamanki tana tare da ke a kodayaushe, kofata a bude take." Haka tauna kwakwan da nake ya hana ni kuka, Mama tana sona sama da baya Mama tana kokarin bada har Rayuwarta domin ni..
"shekaranjiya nayi mafarkin wani kyakkyawan bafulatani ya dauke min ke." Ta fada tana murmushi, kallonta nayi sai kuma na tura baki nace mata."Mama dauke ni fa!" "Eh amma na gaya mishi idan ya saka ki kuka ba xan yarda ba, idan ya saka ki damuwa ba xan yarda ba, idan ya sake wani abu ya same ki ba zan yarda ba, domin na hango shi cikin kuraye da macizai ne, sai dai ina ji a jikina shi jarumi ne domin shi
aya rike da sanda ya rike hannunki har wani kyakkyawar gida, kin ga kenan idan ba jarumi ba, babu wanda zai iya ratsa wa
annan halittun ya wuce lafiya lau.
Da haka nake jin a jikina Ubangiji ya amshi addu'ata ya kuma ajiye ta zuwa lokacin da zai biya min ita." Yake nayi mata domin naga Mama ita fa tayi nisa a kaina,Aqur'an bata jin kira.
A hankali ta riko hannuna ta zaunar da ni a kujeran da yake gaban wata office.
"Kin san yadda nake son ki yi farin ciki kuwa?
Kaf duniya babu wanda ya kai ni son ki yi farin ciki, sai dai abu daya zan gaya miki daga yau kada ki kara zama wani ya wulakanta ki, kada ki kuma cutar da kanki saboda zaa ce kina yawon aure kada ki damu ban kuma ce ki rena duk wanda zai zo rayuwarki da sunan aure ba, amma kuma kada ki rena kanki." Kwantar da kaina anyi a kafadar Mama ina jin wani irin nutsuwa na shiga ita uwa duniya ce ga Yaranta, baya ga ita kanta tana bukatar kowa a tare da ita.
Uwa ita take manta da kanta tayiwa danta addu'a.
Mama she is amazing mother of me, ta gwammace ta rayu da ni akan aurenta.
Mika min goran ruwa tayi wanda ta ciro a jakarta tana fa
in.
"Gashi sha na san kina shan ruwa dama da kome!" Amsa nayi na sha domin bakin a bude ya
e..
"Mama kina ganin na karbi aikin da Ya Ado ya nima min ni nafi son aikin gwamnati ne!" Zungure min goshi tayi tana fa
in.
"Waye yasan gobe ban da Allah idan kika yi hakuri kafin ki dauki lokaci sai Allah ya sauya miki da abinda yafi alkhairi, ki cigaba da addu'a duk wata rayuwa tana bukatar addu'a, ita Addu'a mukulin dukkan wata Alkhairi ne da toshe duk wata sharri." "Mamana, in sha Allah."
"Wai Mama nan kuka zo kuka zauna kun manta da da wasu a cikin." Inji Aunty Raliyah, ta ce mata.
"Raliyah bana son gulma taya zaki biyo Uwa da Autartar!" "Allah ya baku hakuri ya kuma bamu hakuri ."
Dariya na saka muka wuce cikin asibitin mika cigaba da hira, har na manta abinda ya faru.
Kusan mutane da suke zuwa ganin Abba abokan aikin ya Ado ne, kwanakin su Aunty Hindatu biyar suka juya zuwa gida, nayi kewarsu sosai.
Itama Mama tana cika sati biyu ta koma Bauchi aka kawo Yadiko, zuwan Mama ban tab'a shiga wurin Abba ba, amma yadiko tana zuwa ta saka ni a gaba har inda yake zaune suna magana da Rufa'i, yana ganina ya dauke kai, haka na koma bayan Yadiko na tsaya ta ce min..
"fito ke ai shi ya samar dake idan ya isa sai ya gayawa Allah baya kaunarki sai na san inda zan ajiye lamarin,." Abinda na lura Abba ya
an yi sanyi.
Haka dai tayi ta surutu koda na gaishe bai amsa ba, ban kara ba.