← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 86

Sashe 8

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya gaya mana Tijani zai kawo Hajiya Asiya an jima Asibiti kuma ya kamata ace kina gidan." Yadda Mama take shiga ba nan take fita ba, sai naji zuciyata tana wani irin ciwo kamar kaikayi.

Ni dai kamar yadda aka saba kaina a sunkuye, wayar Mama ne yayi kara ta dauka tana fa
in.

"Na'am Alhaji gata nan tazo!" Ta mika min wayar.

Yadda ya balbale ni da fada yasa nayi shiru kamar yana gabana ya cigaba da cewa.

"Kin san Abokiyar zamanki bata gari, sannan ta bar miki Yarinyarta taya zaki kai yarinyar makota?

Ke wacce irin mahaukaciya ce?

Don Allah bai baki haihuwa ba sai ki na wulakanta mishi Yarshi?

Wai ma da izinin waye kike fito?

Ga Hajiya Asiya can da Tijjani sun je gidan ba kowa, ke a rayuwarki idan baki saka mu magana ba, bakya jin dadi ne?" baba yana yin nashi a waya, ta yadda yake shiga ba nan yake fita ba, haka Mama tana yin tana kamar ta rufe ni da duka.

Nasan cewa duk lokacin da zan zo matu
ar ba shi zai kawo ni ba, tow na rantse da Allah kamar yar riko haka nake komawa amma idan ya kawo ni kowa yayi ta ririta ni.

Aunty Hindatu na ta kasa jure fadar Mama ta ce mata.

" Mama dai, ya kamata ku fahimci Lulu ba zata fito don kanta ba, sannan taya zata fito a ce!

" "Gafara can, an gaya miki bamu san yadda kike hure mata kunne ba ne?

Ko an ce miki bamu san yaddA kika mata wayo kina rabata da ku
inta, me yaron nan ya rage ta da shi?

Ko an gaya miki ban san me nake yi ba ne?

Wallahi Hindatu idan baki daina shiga rayuwar Lubnah da gidan aurenta ba na rantse da Allah sai na miki Allah ya isa, kuma ki zauna yanzu su Hajiya Asiya zasu tawo ku koma gida Wallahi, ina zaman lafiya da Mijina ba zaku kashe min aure ba ke da Yan uwanki!

" Cikin fushi Aunty Hindatu ta shiga hada kayanta Ya Sani daga waje da Aunty Munah, suka shiga kananun magana, yadda Ya Sani yake mita yasa Yadiko ta dirko musu kamar zata rufe shi da duka, har tana fa
in.

"Idan wani ya kara shiga rayuwar auren Lubabatu sai na mishi Allah ya isa, tunda burinku shine ku kashe mana aure, idan da kuna da hankali tausarta zaku yi ba ku tsaya kai da fata bata yin kuskure, tun kafin ta iso muka san cewa gaban kanta tayi, haba me yasa Lubabatu take haka ne?

Yaron nan yana girmama ki amma ke kin dage sai kin zubar da mutuncinki."
Kiri-kiri suka hade kai suka min tas Aunty Munah da haushi ya mata itama barin musu gidan tayi ta nufi gidan Ya Umar da yake makama jahun, Ya Sani ma haka ya bar gidan babu shiri, ni daya kamar mayya haka suka yi ta fada bayan sun gama, kuma suka sauko tare da min nasiha, har Yadiko ta shigo da abincin da na kawo suka ci da Mama, ni dai kaina yana kasa har lokacin ban d'ago kai ba, sannan ban ce musu cikanku ba.

Kai mai karatu wannan sai ya zame maka sabo amma a wurina ba sabon abu bane, da na san haka zai faru da Hajiya tace na fasa zuwa da na fasa.

Kiran Sallah la'asar ya saka na mike zuwa ban dakin Mama nayi alola na fito na gabatar da sallah la'asar.

Bayan na idar ina zaune sai ga Hajiya da Yusrah, tana zuwa da gudu ta fada jikina tana fa
in.

"Lulu shine kika tafi kika bar ni." "Yusrah babu Mama sai Lulu ba uwaki ba ce?" D'ago kai yarinyar tayi ta ce mata.

"Allah ya kiyaye ta zama Uwata, ko Hajiya " wani diriricewa Hajiya tayi Tijjani ya daka mata tsawa, yana fa
in.

"Kun ga yarinya mara tarbiyya, Lubnah haka kike tarbiyyar Yarki!" Ni dai bance musu kome ba, ina jin suka gaisa da su Mama da Yadiko, sannan aka zubo musu abinci suka ci sosai.. har a lokacin mamaki bai daina kamani ba yadda suka tawo da tsaraba niki -niki, suka bawa su Mama da Yadiko, yadda Hajiya take wani tarerayata, abin sai yafi kome bani tsoro tabbas Hajiya idan suka saka mu jariri zasu cije shi ya mutu har lahira.

Duk uban abincin da na saka musu amma anan da aka kawo musu abinci sai da suka ci kamar ba mutane ba, har zuwa lokacin idanun Hajiya yana kan kular abincin, sai da Yadiko ta zuba mata hankalinta ya kwanta tana ci tana murmushin, a hankali na tashi na koma dakin Mama na kwanta, wayata ta ce tayi
ara na
auka tare da kallon screen din wayar, shine dauka nayi a sanyayye ya ce min.

"Da fatan kin sami kowa lafiya!" Murmushi nayi nace mishi.

"Suna lafiya!" Sai yayi shiru.

"Luluna ki yi hakuri wallahi nayi haka." "Wani abu ne ya faru kake bani hakuri?" Shiru yayi yana jina kafi
n ya ce min.

"Sai kin zo gida zan miki bayani!" "Wani bayani babu abinda ya faru, don Allah ka daina damuwa akan haka." Daga haka na kashe wayar, na kwanta duk da haka sai da ya kira ni ina gani naki dauka har na kwanta kaina azabar ciwo yake, da yake mun san cewa barcin yamma babu kyau amma saboda yadda kaina yake ciwo yasa na kwanta.

Karfe shida da wani abu ba ji kiran sallah, sai lokacin na lura da yadda aka lullube ni da mayafi.

A hankali ba bude idanuna da suka min nauyi, na dafe goshina ina jin kamar kaina zai rabe gida biyu.

Zama nayi ina dafe da kan har Mama ta shigo dakin.

"Baki da lafiya ne?" D'ago kai nayi ina murmushi na ce mata.

"Lafiya lau!" Na mike da kyar na nufi ban daki na yi alola na fito, na gabatar da sallah, itama sallah na samu tana yi ina idarwa na zauna a wurin shiru sai da ta shafa addu'a sannan ta ce min.

"Me yasa kika fito ba da izninsa ba?" "Ba kome!" Shiru tayi tana kallon yadda nayi shiru.

"Kina son Abbanku ya sake ni ne?" Girgiza kai nayi, sannan ta cigaba da min nasiha tare da fada domin babu wani abu me kama da rarrashi a cikin kalma ta don gaya min take zan kashe mata aure ne, tunda nasan cewa akan Hafiz Baban Bauchi bai da hakuri, ni dai ban ce mata cikanki ba har ta gama maganarta sannan ta fita, bayan isha na isa parlourn Abba na gaishe shi, ashe Ya Hafiz ya iso sai lissafi yake tare da gaya mishi abubu
yan da ya faru a tafiyar da wasu dalilai da yasa aka samu matsala.

Yadda Baban Bauchi ya yarda da Ya Hafiz kaf Yayuna maza da mata babu wanda ya yarda shi haka, durkusawa nayi na gaida Baba ya
i amsa min, sai da Ya Hafiz ya ce mishi.

"Baba tana gaishe ka!" "Ba zan amsa mata ba, akan me zan amsa mata bayan ta fito ba da izininka ba, tasan irin masifar da take shirin kawo min idan da yau mutuwa nayi da Allah zai saka Mala'iku su d'aga ni su ce ga abinda Yarka take yi!" Nan dai Ya Hafiz yayi ta rarrashinsa da kalmai masu dad'i, sannan ya kara da cewa.

"Matukar kina son na kaunace ki Lubabatu ki bi Mijinki sau da kafa, don baki san irin asarar da kika janyo mishi ba ne ke da Hindatu itama zan kira Mijinta na ja mishi kunne tunda ku Yahudawa baku san yadda zaku bi aurenku sau da kafa ba.

Kuma zan kira Addu'a da Umar da Tahir na ja musu kunne kada wani ya kara tura miki kosisi tunda ba zaman aure zaki yi ba."
Yadda Baban Bauchi yake shiga yake fita sai ka rantse da Allah wani abu na aikata, wannan shine burin Ya Hafiz duk ranar da zan zo matu
ar bai mishi ba koda kuwa ya amince tow sai na fuskanci tashin hankali a cikin gidanmu.

Ni kuwa kamar wacce ake watsawa ruwan zafi haka nake jin maganar su kamar danyen guba, nasan Iyaye suna kaunar Yaransu akan kansu amma ni nawa Iyayen sun za
i abinda za a fada a kansu sama da rayuwata, yadda ya gama fadar ya daka min tsawa akan na roki Ya Hafiz, har a lokacin idanuna wani irin zafi suke min, kaina a sunkuye na ce mishi.

"Ya Hafiz ka yafe min." Muryana tana rawa, "Wallahi na yafe miki,matukar ni zan d'aga miki kafa ki shiga aljanna wallahi na d'aga miki ki shiga Allah na yarda da Lubnah Allah ka yarda da Lubnah!" Wannan yar draman da yayi a gaban Babanmu sai ga Baba yana irin farin ciki domin shi dai yaga yadda Ya Hafiz yake kaunata, Ya Hafiz ya ce mishi.

"Baban Bauchi ka amsa gaisuwar Princess don Allah!" Cikin murmushi irin na manya ya ce mishi.

"Na rasa ganewa Hafiz yadda kake kaunar Lubnah baka hango laifinta.

" " Mace ta gari ce, tana da kirki da mutunci.

Ba iya soyayya ya bani ita ba, Allah ya yarda da ita ne ya bani ita.

" Yadda Ya Hafiz yake fa
an kalaman yabo yasa Baba ya kuma juyowa yayi min nasiha, da nuna min yadda Ya Hafiz yake kaunata kaf duniya babu namijin da zai min irin wannan soyayyar da yake min na rike mijina domin kaf duniya babu me min irin son da yake min.........
*08130269641*
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: *ALA
AR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu
BIYAR
Tabbas Ya Hafiz yana kaunata, amma kuma me yasa yake min haka?

Me yasa sai mun gama kome da shi yake juya min laifin?
Chapter 8 · 0% Book details