← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 84

Sashe 83

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

in zaren da Roshni ta saba aura masa ri e a hannunsa. Kai Eshaan, baka jin magana ko?!! Muryar Roshni ta fa i tana zama kusa da shi, tare da karb'ar ba in zaren hannunsa. Ta ago afarsa ta dama sanna ta shiga aura masa zaren. Kana ji na ko?!, kada ka sake cire zaran nan Ta saki afar tasa tana shafa sumar kansa. _Maa, me yasa kowa yake saka ba in zare a afar dama? Roshni ta janyo shi jikinta. Kowa ma a india yana aura ba in zare a afarsa ta dama, 'yan addinin hindu sun ce kariyace da ga abun bautarsu, mu kuma musulmai, muna sakawa ne sbd kariya, domin addi'o'i da ayoyi ne a jiki, kamar yanda ayatul kursi ke bada kariya ga gida muma haka ba in zaren ke bamu kariya, sbd haka kada ka ara cirewa kaji ? Ya gya a mata kai. Roshni ta kai hannunta tana tura sumar kansa baya. Yeh mera bacca hai!(That's my boy!) Ya yi dariya yana kwanciya a jikinta. Tashi kaje ka yi wasa, maza,maza,maza!, hhhhhhhh _. Ta arashe tana masa cakulkuli. Hhhhhh, Maa, Chor mujeh, (Ki bar ni)hhhhhh! Shi da Auwal ne tsaye a akin wani mara lafiya, kullum idan Auwal in ya dawo gida se ya bashi labarin wani yato da suka karb'a a asibitinsu. Auwal in yace masa yaro ne arami, ya gamu da ciwon Cancer, shi ne yau Auwal in ya auko shi yace su zo su duba yaron. Hannun Eshaan i sanye cikin na Auwal, yana kallon yaron cike da tausyawa. Appa yana jin ciwo ko? Auwal ya sunkuyo da kansa ya kalle shi. Sosai ma kuwa Amma ai ze warke ko? Inshaallah Idan ma be warke ba idan na zama likita zan masa magani Auwal ya sunkuya ya auke shi a hannunsa, suka ci gaba da kallon yaron. Na sani My Boy, na san cewa idan ka girma zaka temaki kowa, ka saka kowa farin ciki Shine tsaye a gaban teburi me auke da cake, wanda aka rubuta 'HAPPY BIRTHDAY ESHAAN', duka danginsa na india dana nigeria sune tsaye a bayansa suna taya shi murna. Shi da Neha ne suke guje-guje a lambun gidan Daadi. Yayin da shi ke ri e da ball, Neha ib kuma na binsa da gudu tana fa Bhai ka bani, ka bani mana! Shi kuma ya ci gaba da gudu yana dariya. Shine zaune a gaban Me martaba da Fulani Kahdija, Chiroma, Turaki da Mairama, ranar da aka ce masa Maansa da Appansa sun rasu, a lokacin da Fulani tace. Ni zan kula da shi, dan Allah a bar min shi.... Shi da abokansa na jami'a ne suka buga wasan cricet a filin criket na jami'ar su. Yayin da shi ya daki ball in, ta tashi sama, kuma ta tsallke layin da ake bu ata. Abokan nasa suka iyo kansa da gudu suna kiran sunansa. Shine tsaye a cikin aliban da suka yi graduation, sanye yake da acadamic gown, hannunsa ri e da certificate insa. Shine yake gaisawa da wani babban likita, a ranar da aka karrammashi sakamakon bajinta da ya nuna a aikinsa na likita. Shi da Muktar ne suke zaune a chikin wani restaurant suna hira har da dariya. Shine dur ushe a gaban su Me martaba ranar da suka fa a masa cewar sun aura masa aure da Maryam. Shi da Maryam ne tsaye a gaban indian gate, yana ta mata bayani a kan tarihin ofar, sai ya lura da kamar hankalinta ba ya kansa, dan yaka ya tab'a ta. Miriam! Hmm! Lafiya? Sai ta girgiza masa kai, hannunta ya kama, sannan ya motsa kunnensa yana sauraron bugun zuciyarta, Maryam ta kalli hannunsa sannan ta kalli nata, ta ago ta kalleshi. Ina tare da ke, komai zai yi dai-dai....... Ka fa i sunan Allah Muryarta ta farkar da shi, ba shiri ya bu e idonsa. La haula wala uwata illah billahil aliyul azim!, La'ila ha'illa huwa, wahadahu la sharika lahu, hasbinnalahu la'ilaha'illalah! Wani abu sabo, wani abu da ya manta rabonsa da ya furta. Fitar muryar ta sa ta fito tare da bajewar ba in haya in da ya mamaye shi, ba in zaren afarsa ya shiga kawo haske, wani irin farin haske da ya mamaye gaba ayan kogon. Hasken da ya yi tafiya ya isa zuwa ga Manikandan da Subhurmanyam ya aga su sama. *** *** *** A hankali Maryam ta shiga ifta idonta. Kafin ta bu e shi gaba aya abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata daki-daki. Kafin ta bi wurin da take da kallo, cikin akinta ne, dai-dai inda Subhu ya auketa, kamar mafarki take, kamar idonta ta ifta sannan ta bu e, haka take ganin faruwar komai. Kuma kamar yanzu ta shiga ban aki ta fito. Sai dai ra in da wuyanta yake mata da wanda goshinta ke mata ya tabbatar mata da gaske ne, duk abinda ya faru gaske ne. A firgice ta mi e zaune, dubanta ya kai kan Eshaan dake yashe a gefenta, kamar ma ba ya numfashi, kamar ba shi da rai!!. Baban Ilham dan Allah ka temaka mana, Esh...Eshaan ne ba shi da lafiya, ka kira emergencyn Alaro pls Muryar Maryam ta fa a a sanda ofar gidan su Ilham ta bu e, Baban Ilham ya bayyana a gabanta. Ta tashi Eshaan amma ko motsi baya yi, hatta da numfashinsa ma babu. Hakan yasa ta fito da ga gidan, kanta ko ankwali babu. Ki nutsu Maryam, ina Eshaan in yake ? Ta kasa magana sbd kuka, ta fita hayyacinta baki aya, ta kasa banbance ba i da fari, ta gaza gane meke shirin faruwa da su, wace iriyar addara ce haka?. Side in gidan kawai ta nuna masa da hannu. Maman Ilham, ki kula da ita, bari naje na duba Eshaan Maman Ilham da ke tsaye a bayansa ta gya a masa kai, a lokacin dare ya yi. Baban Ilham zai fita Maryan ta bi bayansa da gudu. Maman Ilham na ri ita sai de ina, hankalinta ya yi gaba. A kan idonta a ka fita da Eshaan in a ambulance, sannan ita ma aka wuce asibitin alaro in da ita, dan goshinta da ke zubar jini har zuwa lokacin. ________________ _To arsheb Subhu ya zo, amma kuma kamar akwai ura har yanzu, dab Fidar yara fa baya numfashi, toh!, ku biyo ni de_ _Godiya nake masoya SAI KASKA CE YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Tiktok @SAI_KASKA Arewabooks @18saikaska Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *BABI NA HAMSIN DA BIYAR (55)* *Alaro city Hospital* *12:30am* Maryam ce zaune a kan kujerar dake kusa da gadon marasa lafiya. azu bayan sun kawo Eshaan asibiti, likitoci suka shiga duba shi. Yayin da itama aka shiga dubatan, amma hankalinta na kan Eshaan in, shi yasa bayan an gama mata tretment ta bazama ta fito ta tsaya tare da Baban Ilham. Suna wurin har likitocin suka fito, suka sanar musu cewa doguwar suma ya shiga, amma su sun duba basu ga abinda ya janyo masa doguwar sumar ba. Sai da Baban Ilham ya tambayeta abinda ya faru da su, amma bata ba shi amsa ba, dan a ganin ta babu wanda zai yarda da abinda zata fa Shima kuma be ara tambayar tata ba ya barta, abinci ma da Maman Ilham ta kawo musu bata ci ba, kuma rabonta da abinci tun daren shekaran jiya, amma bata jin yunwa, batajin wani abu me kama da ita. Babu abinda ke gabanta sai ganin tashin Tafida, ya kalleta da shu ayen idanuwasa ko kuma ja idan ya riki e, ya kirata da 'Miriam' ko 'Daaso' ko yace mata 'Wifey'. Amma sam hakan ya gagara, gashi kwance a gabanta tana ganinsa, kamar me bacci, kamar idan ta kira sunansa ze amsa. A hankali ta kwantar da kanta a kafa arsa, sannan ta ara ri e hannunta dake cikin nata. Kai jarumi ne, jarumin da ya tsaya a gaban she anu, ya fuskance su, ya yi ya i da tsoransa har ya yi galaba a kansu, me yasa yanzu ma bazaka yi ya i da wannan tsoron ba? Ta tambaya tana ago da kanta, ta kalli fuskarsa ta cikin hasken dake akin. Me yasa ba zaka ya i abinda ya hanaka tashi ba ? Muryarta ta kuma amsawa a cikin dubun daren, da kuma shurun akin. ara kwantar da kanfa ta yi a kafa arsa, tana karanto dum addu'ar da Allah yasa ta gifto a ranta. Kamar da ga sama ta ji motsawar yatsunsa cikin nata, da sauri ta ago da kanta tana kallon fuskarsa, hannun nasa ya ara motsawa. Bakin Maryam ya tale da dariya, tana ci gaba a kallonsa. Da kyau, nasan zaka iya, Allah zai temakeka... Bata ko rufe bakinta ba idonsa ya motsa, kafin a hankali ya shiga bu e shi, ya sau e su tar a kan Maryam. arin mi ewa zaune ta ga yana yi, dan haka ta shiga arin taya shi zaman, har ta samu ya jingina da jikin gadon, se jera masa sannu take, yayin da shi kuma ya ci gaba da kallonta, yana ganin yanda take ta fara'a. Zama ta yi a gefen gadon tana kallonsa fuskarta auke da murmushi. Kaga ko... Hannunta da ya ja ta fa o jikinsa yasa ta yi shiru, se kawai ta kwantar da kanta a kafa arsa tana kewaye shi da hannayenta. Allah ya bamu iko Daaso, Allah ya temaka mana ara matse hannayenta ta yi tana murmushi. Kafin ya sake ta yana kallon fuskarta, zuwa yanxu ta fara hawaye, dan haka ya motsa hannunsa na dama a setin bedside drawer yana so tisssu yasau a a hannsa,amma ko motsawa tissuen be yi ba. Ya juyo ya kalleta yayin da ita kuma take dariya, hannayenta ta saka ta tallafi fuskarsa. Komi ya are Eshaan, babu abinda ya rage, sharrinsu ya bisu, babu ba in ruhi babu jan ido, babu fi a, babu gurnani haka kuma babu super natural, yanzu kai ne, asalinka, gangar jikinka, ka sarrafata yanda kakeso ara rungumeta ya yi a jikinsa yana furta. Alhamdulillah, Allah na gode maka Ka fin Maryam ta ago da kanta tana kallon fuskarsa, still tana kwance a jikinsa, shima
Chapter 83 · 0% Book details