Sashe 75
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wuce rashe yana mi ewa. Ya kuma musu sallama sannan wuce. Gidansa ya koma, yaje ya yi wanka sannan ya ara fita ya tafi asibitinsa. *Unguwar Garko* *Da 08:15pm* Suna zaune a kan babbar tabarma, abinci suke ci suna hira, Hassan, Hussain da Muhsin suna ci a kwano aya, yayin da Maanmu da Anti Hanne da kuma Maryam suke ci a kwano aya. Zuwa yanzu Maryam ta saki jiki da matar dan tana da kirki, kuma wani abu aya ne ya gifta a tunaninta kan matar, da alama Abbansu ne ya yi aure, dan ko girkin daren ma ita ta yi. Yanzu da bana nan waye yake shara da wanke-wanke ? Da da bakyanan Ko ni ko Hussain, amma bayan zuwan Anti Hanne kullum ita take yi Cewar Hassan. Maryam ta kalli fuskar matar ta cikin hasken wutar dake tsakar gidan. Hassan cover nake so me kyau Hassan ya kai loma yana mi a mata hannu. Muga wayar taki Da hannunta aya ta zaro wayar a cikin jakarta sannan ta mi a masa. Inalillahi wa inna ilaihi daji'un Hussain kalli wayarta ka gani! arashe yana mi awa Hussain Kai miye ya samu wayar tawa ? Babu abinda ya sameta, kawai de ku inta muke lissafawa Ai nake gaya maka matar nan ta faso gari, kai baka ga hasken da ta yi ba? Harda iba ma ta Maryam ta girgiza kanta tana tauna abincin bakinta. Maryam Iya Ummi ta dawo fa Maryam ta tsame hannunta daga cikin trayn da suke cin abinci tana kallon Maanmu. Tana gari yanzu haka ? Maanmu ta gya a mata kai. Tana nan, karkiga abinda ta ri a yi akan wai anyi auren ki bata gari Iya ummi itace babbar awar Maryam tun tasowa, dan hatta da makaranta basu tab'a rabawa ba, da sukayi candy ne ita Maryam ta ta shiga Binyamuini, ita kuma Iya Ummin ta tafi Gashuwa. Ko sanda akayi bikin Maryam in bata gari. Yaya akwai irin cover wayar taki Me kwaliya fa nake so Kar ki damu gob e zan kawo miki Ah-ah su Yaya a india Cewar Hussain bayan yaga hoton da ke kan wallpaper wayar tata. India ?, mu gani Muhsin ya fa i yana dawowa kusa da Hussain, daga haka kuma se hirar ta koma a kan India, Maryam na ta basu labarai akan wuraren da suka je, ta na yi tana nuna musu hotuna. Salamu Alaikum! Muryar Tijjani ta ranga a sallama daga bakin ofa, da gudu Muhsin ya mi e ya yi kansa, Tijjani ya ri eshi yana dariya. Kasan minene a nan ? Tijjani ya tambayi Muhsin yana nuna masa ledar da ke hannunsa. Yalo ? A'a agwalima ce Muhsin ya karb'a yana masa godiya, Tijjani ya arasa shigowa cikin gidan, Hassan, Hussain, Maanmu da Anti Hanne duka suka masa sannu da zuwa, ya amsa yana zama a kan tabarmar shima, Anti Hanne ta mi e ta kawo masa abinci. Gaba aya mamakinsu ya hana Maryam cewa komai, Abbansu ya sauya, amma yaushe hakan duk ta faru ita bata sani ba?, abun akwai aure kai. Ah-ah ashe mutanen lagos ne a gidan Sai yanzu Maryam ta ankara da bata gaida shi ba. Abba ina wuni Tijjani ya amsa da fara'a kamar ba shi ba, daga haka kuma se ya shiga neman yafiyarta, har da saka mata albarka sannan ya rufe da nasiha. Abun ya bala'in aurewa Maryam kai, ashe akwai rana irin wannan da zata zo ?, koda a mafarki bata tab'a zaton ta. ________________ _Allahu akbat kabira!, kai duniya ina zaki da mu?, jama'a kuga yanda Tijjani ya sauya, hmmmm_ _Ni de ina san na san wacece wannan Anti Hannen, dan da alama kamar sauyin Tijjani ta silar ta ne,to a har kullum ina me matu ar godiya a gareku_ SAI KASKA CE YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Tiktok @SAI_KASKA Arewabooks @18saikaska Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *wannan babin naki ne Oum Nureen* *BABI NA ARBA'IN DA TARA (49)* MARYAM POV. Tafe suke ita da su Hussain a lungun unguwar tasu, Bayan Tafida ya kirata yace gashi nan a wajr ta fito su tafe, shine su Husaain in suka ce zasu taka mata. Hussain wai yaushe aka samu sauyi a gidan nan har haka ? Ta tambayi abinda ya ma ale a ranta tun bayan sau arta a garin. Hummm, ai Yaya tun bayan auren ki komai ya sauya, kin ga da sadakin ki Abba yaje ya auro Anti Hanne a auye, ya kawota gida, ita kuma Anti Hanne tun bayan zuwanta gida sai Allah ya ha a tata da Maanmu, biyyaya babu kalar wadda batawa Maanmu, duk abinda Maanmu zata ce mata shi take, amma fa a wajen Abba bata masa da sau i, dan ita ta saka Abba ya bu e wani shagon provition, ya dawo shi ne yake kawowa abinci a gida, duka awainiyar gidan ta dawo kansa. Ya setu ya dawo dai-dai, abun de sai alhmd Wallahi yaya auren ki alkairi ya zama ga gidanmu Maryam ta yi murmushi, tabbas aurenta da Tafida alkairi ne ga rayuwarta. Amma Hussain me yasa to ni ba'a sanad da duka wannan ba ?, kuma fa muna waya da Anti fati, ko da wasa bata tab'a sabar da ni ba Maanmu ce tace kada wanda ya fa a miki, wai dan kada a tayar miki da hankali Allah sarki Maanmu, Maanmu uwa ta gari. To mu zamu juya daga nan, sai gobe, ai zaki zo ko ? Cewar Hassan a sanda suka fito bakin titi har suna hange motar Tafida dake tsallake. Inshaallah zan zo, sai goben auta arashe tana dafa kan Muhsin. Daga haka suka mata sallama gaba ayan su suka juya, ita kuma ta nufi motar Tafida. Yana gidan gaba, ya jingina kansa da kujera, kayan jikinsa ma ya sauya. Ita kuwa wanka kawai ta yi, amma bata sauya kaya ba, dan kayan nata ya tafi da su. Hello!, bacci kake ne ? Ta furta a sanda ta shiga cikin motar , A hankali Tafid ya bu e idonsa ya kalleta, asa'ilin da take rufe ofar motar, wayar idonsa ta koma ja, zuwa yanzu Maryam ta saba da wannan abun, dan sam baya bata tsoro. Sun glasses insa ya janyo sannan ya saka. Mts!, ba bacci nake ba Muryar sa ta fito kamar me jin baccin, kuma kamar wanda yake a wahale. Baka da lafiya ne ? Ya girgiza mata kai yanawa motar key. Lafiyata alau, kawai yunwa nake ji Ta zaro ido cikin fa Baka ci abinci ba wai ? Ya gya a mata kai, ai dole yaji yunwa, sanda zasu taho daga abuja ma beci abinci ba, cewa ya yi idan ze yi dogon tu i baya cin abinci. Tafiya suka fara, babu wanda yace da wani ala, koda suka zo round about in fada se taga ya yanke hanya, tunaninta fada zasu je. Mamaki be kamata ba sai da taga sun au hanyar Kano road, bata de ce komai ba, a kusa da sabuwar tasha taga yatsaya wajen wani me seda gasashiyar kaza da doya. Ya fita, ta yaje wajen mutumin, ita batasan cewa mutane irinsa na cin irin wa anan kayan ba. Bayan ya siya ya dawo motar, ya mi e titin express in nan, sannan ya yi kwana ya dawo hanyar shiga gari, sai kuma taga sun au hanyar Maje road, kuma a Maje road in ma ya tsaya ya shiga Wani store in dake kan hanya. A nan kuma bata san me ya siyo ba se ganinsa ta yi da ledoji ni i-ni i, yabu e gidan baya ya saka a ciki, sannan ya shiga ya tayar da motar suka ci gaba da ta fiya. Hanyar Shagari G.R.A taga ya nufa, hakan ke nuna mata cewa gidansa zasu je, gidan da a da sai de ta wuce ta ofar sa, wani lokacin har gaisawa suke da masu gadin gidan. Yau se gata zata shige shi a matsayin matar me gidan. Kafin su kai gidan har bacci ya fara auketa, dan bata ma san sanda suka isa gidan ba. arar bu ofar motarsa ne ya farkar da ita daga gyangya in da ya soma aukarta, ya zagaya ya bu e mata motar ta fito, sannan ya kuma zagayawa ya ebo ledojin dake baya. Kawo na taya ka Ya girgiza mata kai. Ke da kike bacci Au ashe ya ganta, se bata sake cewa komai ba har suka shiga cikin gidan, duk da dare ne hakan be hanata ganin kyan gidan ba. Shine a kan gaba ita kuma na biye da shi, har akin da taga ya shiga, a cikin akin ne kuma taga jakar kayanta. Kai tsaye wurin jakar ta wuce, ta bu e ta ta auko wasu pyjams riga da wando masu kyau, ta shiga bayi ta saka kayan sannan ta fito. Sanda ta fito ta iske shi zaune a kan sofa yana cin abinci. Bata ce masa komai ba ta wuce ta auko hijabinta,sannan ta dawo kan gadon ta kwanta, kamar daga sama ta ji muryar sa. Ba za ki ci abincin ba ? Ta juyo ta kalleshi amma shi ba ita yake kallo ba kamar yanda ya saba. Kuma har yanzu idonsa sanye cikin ba in glashin nan. Naci abinci a gida Shi ma be ara cewa komai ba, har ya gama cin abincin nasa, ya aje sauran kayan da ya siyo, ya mi e ya shiga akinsa na gidan, kayansa yaje ya sauya sannan ya dawo akin da ya bar Maryam. A kan gadon ya kwanta yana kallon fuskarta ta cikin hasken dake akin, hannunsa ya motsa a setin swithch, take wutar akin ta mutu. Tsoron da ya saba kama Maryam shi ya kamata, dan haka ta matsa kusa da Tafida ta shige jikinsa, shi kuma ya kai hannunsa ya ri eta, ya mata peck a ka. Ka yi addu'ar bacci ? Addu'a ?, ita bata san cewa shi ba kamar kowa yake ba ?. Tana jin kansa da ya girgiza mata. Kamar yanda ta saba idan suka kwana tare se ta yi addu'ar sannan ta tofa masa. *Cosgrove Estate wuse,st 3, house NO 334* *08:40pm* HARIS POV. Seda ya tabbatar da ya gama