← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 84

Sashe 25

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

an b'ata masa rai. Shi kuma abu mawuyacine ke b'ata masa rai, a kwanakin nan ne abun yayi amari, amma kuma yanzu gashi ya tafi, Sannan har cikin ransa yake fatan Allah yasa ya tafi har abada. Sai de kuma shi da kansa yawan cewa yana nan, babu inda ya tafi, Dan akwai wannan super natural in a jikinsa. Ko ka an baya fatan wani abu da zai cutar da Maryam, musamman ma ace daga gareshi ne. Gaskiya Muktar ya fa a, tabbas yayi dace, dan Maryam ayace tamkar da dubu, samun irinta a wannan zamanin sai an tona. Sannu da zuwa Muryarta ta fito cikin sanyinta, kuma yaji sanda zuciyarya ta buga, ya samu kansa cikin irin yanayin da yake tsintar kansa a duk lokacin da ya saurari bugun zuciyar tata cikin tsoro ko nishadi koma murna. Sannu Daaso, gidan Mustapha ki ka je ? Daaso ?, shekaran jiya ya fara kiranta da sunan, wata ila dan nisha i yake kiran sunan, Mustapha kuma ta san sunan mijin Maman Ilham ne, dan haka ya fa a mata ranar da yace mata taje gidan. Eh, nan naje, banma jima ba yanzu na shiga kuma na fito an cije lips dinsa ka an, sannan ya gya a kansa a hankali. Hira ki ma je ku kayi? Ko ka an, nayi meat pie ne, shine na kai mata nace a bawa yara Yanzu ma kansa ya gya a sannan yace. Muje ko? A hankali ta fara takawa zuwa cikin gidan, ya tsaya a wajen yana kallonta, sannan ya rufe gate in, ya shigo gidan shima. Bai sameta a parlo ba dan haka yayi saman shima, wanka kawai yayi dan yayi Sallah a hanya, ya saka wasu jogger set farare, ya rufe kansa da hular hoodie in kayan, ya sau asa, cike da farin cikin zai ci girkin Maryam. Kuma kamar yanda ya zata in ne, ta aje masa komai akan danning, ruwan shansa da abincinsa yaga yau harda juice a wani jug na glass. Bai san sanda murmushi ya sub'uce masa ba, to shi kuwa miye ba zeyiwa wannan innocent soul in ba ?. Kujera ya ja ya zauna, sannan ya bu e plate in da ta aje, ya bu e warmer in farko, wadda yake da tabbacin miyace a ciki, kamshin spices ne suka fara shiga hancinsa, kafin yayi arba da cabege sauce, kalar cabejin daya hadu da attaruhu da tattase sune sukafi aukar hankalinsa. Harda ha iyar yawunsa, sannan ya aje murfin a gefe, ya janyo ayar ya bu e ita kuma farar shinkafa ce a ciki, wadda ta dafata da carrots da kuma green beans. duka ya juye shinkafar a plate in, sannan ya zuba miyar, ya hauci yana ta lumshe ido, da ace yana da yawan magana da wata ila santi zeyi, dan abincin nata ya kai a masa santi. Yana ci yana ha awa da strawberry juice in da ta aje masa, har ya cinye tas, dan dama bata tab'a zuba masa abinci ya rage ba. Tashi yayi ya shiga kitchen in, ya bu e dish washer sannan ya jere mata kayan a ciki. Har ya juya zai fita kamshin wani abu ya bigi hancinsa, ya waiga ya waiga sai hango wasu containers guda biyu kusa da stove, beyi tunanin komai ba ya nufi wajen. Ta farko ya bu e yaci karo da meat pie, hannu yakai ya auki guda aya ya kai bakinsa, ya cinye shi tas, sai kuma ya rufe mata. Ya bu ayar ita kuma cup cakes ne a ciki shikam guda biyu ya iba ya cinye shi duka, a ransa yake fa in, Maryam na so ta maida shi acici. (kujini da an raini Rufewa yayi ya maida mata ya aje sannan ya fito, a parlo ya zauna, ya kunna wata tashar da ake nuna wasan cricket, ya kishingi a yana kallo, harda ture hular hoodie in, ya shiga shafa sumarsa data fara taruwa, sbd al awarin da yayiwa Daadi, hatta wajen fade in ma ya tara gashi. Ko me ya tuna sai ya mi e tsaye ya nufi akinsa ya auko wani abu ya dawo asan, yana daga inda yake ya wala kiran Maryam. Maryam na zaune a aki tana sauraren ira'a qur'ani, taji kamar Tafida na kiranta, kasan cewar kunne aya ta saka. Sai ta cire ear piece in, ta shiga arin danna pause amma sam wayar ta i bata ha in kai, haka take mata kwana biyu, ta an ja gajeren tsaki, sai ta tsayar ta jikin ear piece in, ta mi e hannunta ri e da wayar ta saka hijjabinta ta fita. A parlo ta sameshi, sai ta zauna a asa. No seat here Maryam ta kalli inda yake nuna mata, gefen kujerar da yake zaune a kai ne, kasan cewar kujerar nada tsayi ita kuma sai ta zauna a can arshen kujerar. Kanta a asa kamar kullum idan tana gabasa, gyaran murya yayi, bayan ya gama saurarar abinda ya saba. Kamar yanda na fa a miki, an gama komai da kamai na makarantar ki, so gobe zamuje tare zamu arasa abinda ya rage...... Nasan zaki bu aci wani abun na amfanin makaranta, so ni bansan me kike so ba, dan haka na yanke shawarar kawai na baki ku in ki siyi kome kike so, dan akwai super market nan kusa da block in mu, zaki iya zuwa ki siyi abunda kike da bu arashe yana mika mata ku in da Maryam bata san adadinsu ba, hannunta cikin hijabinta ta karb'a, kuma hannu biyu Nagode sosai, Allah ji an mahaifa Bai amsa a fili ba sai yaci gaba da cewa Kina da waya ne ? A hankali ta gya a masa kai, tana fito da wayar tata daga hijabi ta nuna masa, saida Tafida ya kusa yin dariya, amma yasan idan yayi zata ji babu da i, amma wayar tata ta bashi dariya, like for real matar Tafifa da wannan wayar. Daaso wanna ai ba waya bace Dama tasan za'a rina, taya za'ayi Tafida ya kalli wayarta da kima, yana ri e waya biyu, kuma duk da ba sanin ku in wayoyin ta yi ba tasan masu tsadane. Barinma iPhone insa, dan wayar ta burgeta ita kanta, musamman ma gefen wayar wani abune aka kewaye wayar dashi kamar gold Karb'i wannan, akwai numbers ima akai, idan na shirya zan karb'e su Ya mi a mata Samsung insa, irar S22 ultra, Maryam ta kalli wayar, sai kuma a hankali ta ago ta kalleshi, shima in ita yake kallo, kafin ta kai hannunta ta karb'i wayar, za tai masa godiya ya katseta da fa No Miriam, you don't need to be Miriam ?, ita kuma haka za ta yi ta samun sauyin sunaye ?. Ranar haka ta kusan raba dare tana ta shige da fice a cikin wayar, ita wayar tamafi burgeta akan ku in da bata ma samu TA irga ba. Duk da shima ku in ta ji da insa, domin bata tab:a ri e kudi kamar haka ba, ololuwar yawan ku in da take ri ewa a hannunta shine na registration inta. Amma ita wayar tafi yin gaba da ita, kuma taga babu sim a kai, saide wasu numbers da basu da yawa, kuma a ciki akwai ta Daadi, Neha, Chaacu Imran (Wato kawu Imran), Chaacu Irfan (Kawu Irfan). Choti Gulzar (Sieger Gulzar), Ramesh, Arjit, Mahesh, da dai sauranau, yawancin number in na india ne, hakan ke nuna mata cewar da yan uwansa na india Yake waya. Sai kuma gallery data duba, tarin hotunansa ne birjit, abun har ya bata mamaki, ganin namiji da yawan hoto, ita da take mace ma bata da wasu hotuna na azo a gani, amma nasa kam sai baki take kamawa dan mamaki. Kuma ciki taga na wadda take kyautata zaton itace Neha da kayan sojoji an musi shi da ita, abun mamakin shine kayan sojijin nigeria ne a jikinta, kuma gata ba india, hotuna dai sai wanda ya manta baiyi ba. A ciki ma taga wani nasa wanda ya tara gashi a kansa har yayi parking insa, harda dariyarta, dan style in hoton ya bata dariya. Eshaan Tafiida Ta furta muryarta auke da wani irin nishadi da bata san daga ina yake fitowa ba, a cikin daren gaba aya ta ebe kayan wayarta ta maida kan wayar, amma bata tab'a masa hotonsa ba ko wara aya, dan wata ila ya bu aci kayansa, amma taji da in samun wayar sosai ba ka an ba. HANAM POV. Cikin sati ayan da Uchenna Franklin yayi a ashinta sun ara samun kusanci, duk da bata fatan ya haura harkar kasuwanci kawai, dan ita dan shi tasa aka kawo shi, bayan nan kuma bata fatan wata ala a daban, sbd kamar yanda ta fa a masa ne a wancan lokacin sunada banbanci sosai. Kuma cikin sati ayan ya gama mata aikin da zai mata, sannan taji da in aiki dashi sosai ba kadan ba, dan ya iya inki sosai, kuma bayan sun gama aiki saida ta sake masa tayin karb'ar ku i kamar tun sanda suka fara aikin amma ya i, kamar de da farkon. Yace ita anwarsa ce, ba zai karb'i ku inta ba, yayi mata ne matsayinta na anwarsa. An ce komai yayi farko yanada karshe, gashi har yau Uchenna zai bar fashion house in, ya shigo office inta tana bawa Arya custard dan yau Naani insa bata zo ba, ta mi e da Arya in a hannunts, tana masa murmushin da ma'aikatan wurin suka fa a masa shi ka ai takewa irinsa, amma su dai kam basa samunsa. Har ka gama ? Ta yi maganar tana kallon jakar hannunsa Eh wallahi na gama ha a komai, zan kuma koma bakin aiki na To Mr. Uchenna, Nagode, nagode sosai, thanks a ton you got it......my friend ba o zai yi halinsa Ya fa i yana arin karb'ar Arya daga hannunta ta sakar masa shi, ya karb'eshi. Muje na taka maka to Haka ta raka shi har parking lot, inda ya aje motarsa, ya bata Aryaan sannan yayi musu sallama ya tafi. *Ma farin komai kenan _________________________ _Ah-Ah, su Daaso an shiga next level_ _Na fada ?, aa nayi shiru dai_ _Ina me mika muku dubbin godiyata, Allah ya temaki ko wannen ku -SAI KASKA CE
Chapter 25 · 0% Book details