← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 84

Sashe 16

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

magana ta Maanmu wasu manyan mata da aka aiko daga fada wanda suka shiryata cikin alkyabba suka fita da ita daga gidan, suka sakata a cikin mota suka kawota fadar ha ejia, tunda take a rayuwarta bata tab'a shigowa cikin fada ba, dan bataga dalilin da zaisa ta shiga fadar ba, kuma suna kawota ne kaitsaye akayi turakar Fulani da ita, duk da tanajin fadar babu hayaniya sosai alamun an wancan bikin suna gidan dinner, kuma tunda aka kawota bangaren da take ciki kai tsaye wannan akin da take ciki aka kawota, daga ita sai jakar kayanta guda aya, kuma yawancin kayan ciki Anti Fati da Badar ne suka bata shi, dan gaba aya nata cewa sukayi bazata tafi da suba, hijabanta kawai suka bar mata. Tunda tayi sallar isha har yanzu hawaye bai yanke a idonta ba. Jin kamar ana motsa kofar akin ne yasa gabanta yayi wata wawuyar yankewa ya fa i, ta tsirawa kofar ido sai taga Fulani ta shigo, a sirrance ta sau e a jiyar zuciya, Fulani na mata murmushi ta araso har cikin akin tana zama a kusa da ita, Maryam ta zabura zata sau a kasa Fulani tayi saurin ri ota tana girgiza mata kai. Haba!, haba! Maryam ai yanzu kin zama ar gida Maryam ta share hawaye tana zama amma a arare ta zauna sai kama jikinta take, zama kusa da matar sarki ai abun azimun ne. Maryam, inasan nayi miki magana a matsayina na uwa wadda take fatan samawa anta lafiya, ba a matsayin Fulani Khadija matar sarki ba Sai Maryam taji abun banbarkwai, itafa dama tasan cewa dole dai wanna auren na manufa akayi, in ba haka ba taya za'ayi a zab'ota ita aya kaf cikin tarin an masu ku i da mulki na garin nan ace sai ita, ita ka ai, Fulani ta kamo hannayen Maryam. Maryam, Tafida ya taso ne cikin wata hautsinnaniyar rayuwa, tun yana yaro ya rasa iyayensa, Raruwarsa gaba aya lillub'e take da wani ba in duhu, Kuma a yanda aka sanar mana babu me iya kawar da wannan duhun na rayuwarsa sai ke Sai kuma tayi shiru, hawayen da Maryam taga a idonta shi yafi ru ata fiye da maganganun da ta fa Ina me ro onki Maryam, dan Allah ki temaki ana, ki ceto shi daga cikin wannan kogin d a yake ciki, Nasan zakimin kallon me san kai, amma ina ro onki dan Allah.... Maryam ta shiga girgiza mata kai, ita bakinta ma ya kulle, ta kasa cewa komai, maganganun sunwa walwata nauyi. Ta masa fahimtar maganganun nata gaba daya, da kyar ta iya lalubo muryarta. Ni ban isa na warkar da kowa ba, Allah shine me waraka, kuma shine me warkar da kowa _ya ne ?, my people, garifa ya kama da wuta, kamar wani abu yana auri a nan, labari ya dauki zafi _To ki biyoni domin jin karashen labarin, a har kullum nice taku Salma Ahmad Isah, wato SAI, Ina mi a godiyata zuwa gare ku -SAI KASKA CE- YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Arewabooks @18saikaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *BABI NA GOMA SHA BIYU (12)* *Washe gari* *Malam Aminu international airport* *Da misalin 10:00am* Tafida ya fito daga wani shagon snakes, inda ya saba kaiwa ajiyar key kafin Muktar yazo ya karb'a, wasu lokutan ma tare suke tahowa idan ya aje shi sai ya juya da motar, to yau sun taho da wata shi yasa bai biyo shi ba, tun jiyama da sukayi sallama bai ara ganinsa ba, kawai de da zasu taho ya kirashi akan zai bayar a aje masa keyn inyaso sai yaje ya karb'i motar. Inda yasan ya bar Maryam ya dawo, zaune take akan daya daga cikin wasu kujerun dake wajen, ga jakukunansu a kusa da ita, sai yanxu ya samu damar are mata kallo, dan yau da safe da yaje fada sarki ya fara zuwa ya gaisar,sannan yayi masa sallama sai ya fita yaje ya yiwa Fulani sallamar itama, kuma itace tace masa yaje ya jira Maryam in a mota, yana zaune a motar suka araso ita da Nadra. Kuma har ta shiga motar bai kalleta ba, gaisuwar da ta masa ma da yar ya samu ya amsa, kuma bai kalleta da kyau ba sai yanzu. Bata cika fari ba, amma kuma farar ce, bata da wani kyau na tashin hankali, saide bata da muni kyanta daidai ita, kuma bata da jiki duk da abayar dake jikinta tanada fa i, amma hakan bai hanshi ganin sirirantar ta ba, wani abu dayafi komai kyau game da ita shine idanunta, farare tar, duk da sun anyi ja, alamun tayi kuka, wani irin innocent face gareta, kuma akwai nutsuwa da kamewa a tareda ita, Kuma daga ganinta kasan cewa akwai arancin shekaru a tareda ita, sai yaji tausayinta ya ara kamashi. "Muje ko ? A hankali Maryam ta ago ta kalleshi, gabanta yayi wata iriyar muguwar fa uwa, taji kamar tana nitsewa a cikin wani abu, kamar yanda shima bai kalleta ba itama bata kalleshi ba sai yanzu, ta saba jin hirar Tafida a bakin mutane da yawa bata san ashe haka Tafidan yake ba, lalle kuwa Tafida, ai wannan bai dace da wannan sunan na Tafida ba, wannan sunansa Eshaan, dan shine yafi dacewa da shi, ashe duk abunda Badar ke fa a mata gaskiyane. Kuma tana kallon fuskar tasa sai maganganun da sukayi da Fulani yau da safe suka fa o a cikin walwarta. Maryam, nasan da cewa Allah shine me temakon kowa da komai, amma ke kece sanadiyyar temakon Tafida, akwai wani abu dake damun rayuwarsa da bayasan karatun alqur'ani ko addu'a, nasan cewa ke me ilimice dan haka ki ri i addu'a, ga wannan qur'an in ki lazimci karantashi a kullum, na tabbatar da Allah zai temakeku, ya kuma baku zaman lafiya, Allah ya miki albarka azun sai ta kar6i qur'an in ta kuma mata godiya, bayan fitar Fulani wata ta shigo wadda ta bayyana mata kanta a matsayin Nadra, ta bata wata brown abaya, kuma itace bayan tayi wanka ta saka dan har yanzu ma itace a jikinta, saida suka fitone taga tarin wasu akwaituna guda shida, Fulani ta sheda mata da kayan aurenta ne da aka mata, a lokacin ma saida tayi hawaye, kuma wasu bayine da Nadra suka rakata har motar da akace Tafida na ciki, suka saka kayan a baya, sannan ita ta shiga motar. Kuma tun bayan gaishe shi da tayi bata ara cewa komai ba, shima kuma baice inba, sannan batayi gigin kallonsa ba har suka iso kano, amma kuma gaba aya a takure take a cikin motar. Kuma bayan sun zo ne ya saka aka shiga musu da kayansu ciki yace ta zauna ta jirashi yaje ya dawo shine har yanzu yake tsaye a gabanta. Kamar yanda a mota sukayi tafiyar kurame yanzuma haka ita sukeyi, zaune take a gefensa, cikin wani irin kusanci, kusancin ma har yafi na azu, gaba aya sai taji wani iri, ta takur fiye da azu. A hankali ta an waigo ta kalli fuskarsa, ba ita yake kalloba idonsa na kan wayarsa yana dannawa, ga wani sun glasses wanda yake idonsa tun tahowarsu daga ha ejia, wani abun mamaki ta gani a gefen fuskarsa, ar ha ejia ta gani a kusa da sajensa, gefen kunnensa, abun ba aramin mamaki ya bata ba. Ashe shima yanada ita kamar yanda itama take da?, ai ita tunaninta su basayin irin wannan abubuwan. Da sauri ta juya ta kalli window domin itace a window seat, wani abu da bata tab'a kawoshi koda a mafarkinta ba, shine hawa jirgi, yau sai gata a cikin jirgi, tana iya hango gajimaren dake asa, abun gwanin ban sha'awa. Hankalinta gaba aya ta maida akan kallon windown, dan yafiye mata alkairi, dan da taci gaba da kallonsa gwara ta kalli windown. Tunda ta juyo ta kallishi, Tafida ya ankara da ita amma bai ko nuna mata ba, sai kuma wata hira da wasu an mata dake tsallakensu ta dauki hankalinsa. Yanzu dan Allah hafsa idan na samu wannan guy in ban more ba? Sai kawai ya motsa kunnensa ta yanda zai samu damar jin abinda suke fa i da kyau, sai kuma ya tsinto abinda beyi zato ba, wannan bugun zuciyar, bugun zuciyar da yake kwana yake tashi da shi akwana kin nan, wannan bugun zuciyar da yake kwantar masa da hankali ya saka masa nutsuwa. A hankali ya juya ga inda sautin ke fita, ita ince zaune a gefensa gaba aya ta maida hankalinta kan kallon window, iko sai Allah, ashe itace ?, tabbas itace domin sunanta Maryam, amma sam beyi tunanin sake ha uwa da ita bama, balle har ya sake sauraren bugun zuciyar tata. Hello handsome! Maganar aya daga cikin an matan dake tsallaken nasu ta katse masa hanzari, a hankali ya zuyo ya kalleta da idonsa dake cikin sun glasses. ya akayi ? Mamaki ya kamata dan ba tayi zaton yanajin hausa ba, ita kallon indian take masa, zuciyar Maryam ta matse a irjinta, itafa shi yasa bata san kyakyawan namiji, yanzu an mata zasuyi caa akansa. Gara taso mummuna duk kuwa muninsa, inde har yana sanya kuma itama tana sansa hakan ya wadatar. Ammm.....da...dan Allah lambar wayarka zaka bani Amsar da ta fito daga bakinsa ba aramin basu mamaki tayi ba, bama su ka ai ba, harda Maryam dake zaune a gefensa. I am sorry maam, but i am married, kinga matata ma arashe yana an kaucewa dan su samu damar ganin Maryam in dake rakub'e a gefensa. Oh sorry Never mind Maryam ta ha iye wani abu, ahse har zai iya nunata a waje yace ita matarsa ce ?, kode yayi hakan ne dan an matan su yaleshi ?, itafa tunda ta ora idanta akansa wani abu yaxo ya tokare mata ma oshi. Tana hango umbun tazarar dake tsakanin ta dashi, sam ko ka an basu dace ba, basu dace da juna ba, a da tana neman dalilin da yasa aka aura masa ita, amma bayan maganar da sukayi da Fulani jiya ta samu amsar tambayarta, an aura masa itane sbd itace maganin wani ciwo a rayuwarsa ba dan yana santa ko yana ra'ayinta ba, amma me yasa ?,
Chapter 16 · 0% Book details