← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 84

Sashe 20

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

awata wurin dashi, shima dai nan in kamar can ta hasaso yanda zeyi kyau da addare, aiko zata zo ta duba shi da daddaren. Wani stairs ta gani wanda zai kaita can saman rufin gidan, a hankali ta juya zuwa wajen, tana takawa har ta kai saman gidan, nanma ha uwarsa ba'a magana, kuma saman ma akwai jerin kujerun zama ga grass carpet ga iska me da i dake ka awa a wurin, ta shiga duba gidajen dake kusa da nasu dama wanda ke nesa da nasu, ita kam yau ta rasa abunyi dan murna. Tunawa da tayi ta bar girki yasa ta koma asan ta shiga kitchen in bayan ta leka wani lungu da tagan shi a bayan kitchen in, taga b'ulla gaban gidan ne. Taliyar tata ta sau e ta ha ata da kayan ha in da ta mata sannan ta komo kitchen din ta zauna ta saka taliyar a gaba tana kallo, sai kuma tayi bisimilla sannan ta kai bakinta, wasu lokutan burika na cika a gaske ba mafarki ba, yau gashi tana cin taliyar da take burin ci. Allah abun godiya. TAFIDA POV. Har ya kai ST NICHOLAS HOSPITAL, bai dena tunanin addu'ar da tayi masa ba, anya kuwa idan yaci gaba da zama da ita bai cuceta ba ?, anya kuwa ba zai zama me san kai ba ?, da haka ya fito daga motarsa har ya shiga floor na farko kuma kamar kullum yana gaisawa da mutane, a ofar elevator ya ha u da Khabir. Ango, Ango Itace kalmar da khabir in ya fara fa i suna gaisawa, Tafida yayi murmushi, amma baice komai ba, suka shiga elevator in zuwa hawa na 5 dan a nan office insu su dukan yake. Khabir sai tambayarsa yake akan auren nasa amma Tafida ya i cewa komai sai da suka shiga har office in Tafidan sannan ya bashi amsa. Khabir, yanzu bani da abin cewa akan auren nan, ka bari akwai wata waya da nake jira, daga baya sai muyi magana Kamar Khabir in zai ce wani abu, sai kuma yayi shiru. Allah kyauta, bari naje Tafida ya gya a masa kai, wayarsa ce ta fara ringing tun kafin ya zauna, zaman yayi kamar yanda yayi niyya, ya cire hular dake kansa sannan ya daga kiran, suka gaisa da Muktar sannan dalilin kiran ya taso. Me ka samo ? Muryar tasa ta fito cikin wannan ajin nasa da kasaita, yanayi yana tura sumarsa baya, muryar Muktar ta fito daga cikin wayar yayinda yake fa Komai ma na samo, sunanta Maryam Tijjani Muhammad, haifaffiyar hadejia unguwar garko, tanada yan uwa hu u, babbar yayarta itace Fati matar Habib, nasan ka sanshi ai gidansa ma kusa da gidan ka ne Idanun Tafida a lumshe ya gyada kai, kuma shima Muktar in kamar da yasan ya gya a masa kan sai yaci gaba. Tanada anne uku, Hassan da Hussain sai autansu Muhsin...... Wato Tafida abun mamakin shine annen nata an biyu a secondary school suke, kuma sune suke ciyar da gidan nasu, and a shekaru bazasu wuce 18 ba Da sauri Tafida ya bu e idonsa Me ?, but ina babansu ?, ko ya rasu ? Ya jerowa Muktar tambayoyin, cikin wata iriyar murya da bazaka iya gano halin da yake ciki ba. Wallahi yana nan da ransa, da drivern tilera ne, ya ri i ku i a da, amma kuma yana bin mata kasan shi kuma arfe ba'a ha ashi da kazanta, sai me motar ma ya kwace kayarsa, daga nan kuma sai ya talauce, sai yake ganin kamar wai matarsa mahaifiyar su kenan itace me farar afa, sai ya fara mata cin mutinci baya kula da ita da yaranta, wani yayanta ne wai Usman, Shine yake kula da ita har yaran suka taso sannan suka fara aiki a wani gareji, kuma har yanzu sune suke kula da gidan, and baban kuma har yanzu bai dena halin banzansa ba, ni wani labari da naji ma ance ku in auren Maryam in da aka bashi zaije yayi aure dashi, abun de abun tausayi umhm ina jinka Tafida ya fa i hannunsa akan bakinsa Shi wanna kawun nasu yayan maman tasu shine yake aukar nauyin karatun Maryam in, dan poly take ma, ta gama level one zata fara level two, kuma kasan wani abu ?, wallahi yarinyar akwai kamun kai, ga tarbiyya bata da matsala ko ka an, ko saurayi ba ta da shi sai wani wai shi sanata, kuma shima ba kulashi take ba, dan yanda naji labari ma ance wai daga karshe ce masa tayi ita yanzu bata da ra'ayin aure, gaskiya kayi dace Ya sauke hannunsa daga kan bakinsa. Gaskiya kam nayi dace, nayi dace da su Fulani suka aura min ita, dan nasan idan ba ita bace ba lalle na karb'eta ba, saide kuma ita batayi dacen ba, su Fulani sun hargitsa rayuwarta da suka aura mata ni, amma babu komai, zan nema mata gun karatu a nan polytechnic din alaro, sai taci gaba kawai kaje poly din ka karbo min takardunta ka aiko min pls Tafida yanzu baza kayi ha uri da auren nan ba? Yaya zanyi Muktar ?, nesanta kaina da zanyi da ita shine babban gatan da zan mata, idan har naci gaba da kusantar ta zan iya cutar da ita, and if that happens bazan tab'a yafewa kaina ba, bana san na zama silar rasa innocent soul kamarta Yana iya jiyo ajiyar zuciyar da Muktar yayi. Kuma hakane, Allah ya mana me kyau kawai Ina asibiti idan ka karb'o takardun just let me know Inshallah Daga haka kuma wayar ta are, ya ira drivern sa ya aike shi siyyaya, sannan ya fara aikin da yake jiransa. UCHENNA POV. Dariya yayi bayan Abba ya gama ro onsa akan wai yana so yayi aiki a ashin arsa, to shi a duniya me Abba zaice ya yayi,kuma ya masa musu, shi kuma Abba ganin yana dariya yasa yace. Kaga zan saka ta baka albashi fiye da wanda ake baka a nan.... Haba mana Abba, nifa bance komai ba, ni yanda kake ro onane yake bani dariya, abba babu abinda zaka nema nayi maka na i, komai kake so wallahi ni me maka ne Ran Abba yayi tas, a kullum idan ya kalli Uchenna wani alfaharine ke cika zuciyarsa, yana jin inama ace dansa ne, dan ya fiye masa Kamal sau dubu. Haris..... Sai kuma yayi shiru. Na'am Abbana God bless you Abba God has already bless me, tunda ya bani kai a matsayin uba Abba ya mi e daga kan executive chair in da yake kai, ya zagaya zuwa tsallaken teburin nasa ya zauna a kujerar fake facing ta Uchenna. I am so proud of you Haris, Uchenna Franklin Uchenna na murmushin da baya rabuwa da fuskarsa ya kamo hannayen abba. Abba i am the one that will be proud of you, because you changed my life, Abba ka bani abinda babu wanda ya bani, ka bani kyakyawar rayuwa, Allah ya raya mana kai, Hanam anwatace, zanje nayi mata aiki kyauta, inki baiwata ce, laifine dan na baje basirar inkina domin anwata? Abba ya shafa kansa, kalamansa sun are, dan babu abinda zai iya cewa. Yaushe zan fara zuwa ? Gobe Allah ya kaimu Yana san yaje ya ga wannan anwar tasa da a kullum abba bashi da magana da ta wuce tata. TAFIDA POV. Tare suka dawo gidan shida drivern sa, amma bai shiga gidan ba sai da suka zagaya ta baya yasa drivern ya jibge kayan da sukayi shopping, kuma tun daga kitchen in yaga sauyin gidan, dan ko ina a gyare yake tsaf, dama shi baya bawa kitchen in muhimanci idan ba girki zeyi ba, wasu kayanma ba tab'a amfani da su yayi ba. Saida ya dawo ta kofar gidan ya sallami drivern sannan ya nufi gidan. Curtains in falon wanda ke jikin katangar glass in nan a sau e suke, dan haka bai samu damar ganin komai ba. Abu na farko da idonsa ya fara gane masa a parlon bayan ya bu e sogar shine, Maryam kwance a kan kujerar parlorn, tayi ai, amma kuma lullub'e cikin hijabi, daga ganinta ba bacci take ba, duk da idonta a rufe yake,Sbd ga wani guntun murmushi a leb'enta, sai kawai ya motsa kunnensa. Abu na farko daya fara saurara shine wannan sautin, wannan sautin daya sauya duniyarsa a kwanakin nan, ya shiga cikin irin yanayin da ya saba shiga idan yana sauraren bugun zuciyar tata, kamar igiyar ruwa na ka awa, kamar iska me da i wadda take busowa daga bishiyoyin garden in gidan sa. A tare da bugun zuciyar tata kuma sai ya tsinkayo wani abu, haka kamar magana, sai ya kara takowa cikin parlon, har ya kawo jikin kujerar da take kwance, sai a lokacin ya samu damar sauraren abinda itama take saurare. Wato ear piece ta saka tana sauraren novels na ji. Yaji tausayinta ya ara cika zuciyarsa, nisha inta take hankali kwance, ba tareda tasan halin da rayuwarta ke ciki ba. Kuma bisa ga dukkan alamu littafin na mata da i, a hasaso ya indonsa yanda zata tsorata idan ya tahseta, daga jiya zuwa yau ya fuskanci cewa tana da tsoro, kuma shi yafi jin dadin sauraron bugun zuciyar tata idan tana a tsorace. Yau maryam yini tayi cikin nisha i, dan ko ina ta kalla a gidan wani da i ne ke lullub'eta, tanajin inama zata dawwama a haka, gidan ya mata fiye da zatonta, kyakyawan kitchen, kyakyawan aki, ga kyakyawan garden. Komai ma na gidan me kyau ne, haka ta yini ita ka ai a gidan, amma kuma ka aicin bai dameta ba, dan akwai TV, ga kuma kitchen. Haka ta shiga tayi abincin rana ma sannan tayi nadare dan harda shi ta dafa, bata sani ba wata ila zai ci. Har tayi sallar la'asar amma babu alamar dawowar Ficar yara, to wai ita inama ya tafi ne ?, yace mata de aiki za shi, to wani aiki yake?, tayiwa kanta tambayar lokacin da take ban aki tana wanka, sai kuma kwakwalwarta ta nuno mata hoto aya daga cikin hotunansa da ta gani azu, hotonsa sanye da lap cort, da kuma wani award da ta gani akan wata chest drawer. Wato likita ne, bayan ta gama wankan ta
Chapter 20 · 0% Book details