Sashe 6
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dan nima jibi zan raka anti fati gidan auren 'yan uwan mijinta ai shikenan Badar ta fa i tana duba mata sabbabin vedios in girkin data samo mata a tiktok. TAFIDA POV. zaune yake a mazaunin me zaman banza, yayinda abokinsa muktar yake tu a motar, dan dama shine yaje ya auke shi a airport bayan ya sau a a kano, idanunsa sanye da wani sun glasses, ya boye kalar wayar idansa data koma ja tunda safe, duk da muktar yasan halin dayake ciki amma baya san ya agawa kowa hankali. ora hannunsa akan bakinsa yana nazari, nazarin abinda zai iya faruwa a hadejia, yanzu ya shiga cikin wani irin hali da ba in ruhin dake cikinsa yake tashi akai-akai, a da sai yayi wata da wattani bai tashi ba, amma a kwanakin nan abun ya ta'azzara. muktar ya d'an kalleshi da gefen ido tunanin me kake ? a hankali ya sauke hannun daya ora akan bakinsa ya juya yana kallon window, sai ya lura da har sun shigo ofar garin hadejia ta farko babu komai... aa Tafida, akwai wani abun hakane, kamar yanda muktar in ya fa a akwai wani abun, jikinsa ne ke bashi cewar akwai wani abu dazai faru, to amma taya zai fa a masa cewa jikinsa na bashi cewar wani abu zai iya faruwa. Bai amsa shi ba, sai hannu dayakai ya cire sun glasses in dake idonsa, a lokacin suka karaso dai-dai round about in na malam zangi, babban round about in hadejia. Tun daga ganin lambar motar matasa suka gane cewa TAFIDA ya shigo gari, tun bayan daya dawo daga india, aka na a shi akan sarautar mahaifin sa ta TAFIDA, yayi hawan doki matasan garin dama an mata suka ganshi, shikenan suka samu abun magana, kaf an matan garin ha ejia babu wadda bata san Tafida ba, samari na matukar sansa, hakan tasa a duk lokacin da za'ayi hawan sallah ko na kilisi dakarun Tafida sunfi na kowa yawa, sbd rabi da kwatan matasan had'ejia suna sansa, Allah ya masa wannan farin jinin, ga kuma tarin an matan da zaka gani a wajen idan har yayi hawa, kowa zaka tambaya zai baka labarin Tafida a ha ejia. Juyowa yayi ya kalli muktar da jajayen kwayoyin idonsa, muktar in ma ya jiyo ya kalleshi, saida gabansa ya fa i yayinda yayi arba da kalar idon nasa, duk da ya saba ganinsa da idan kwayar idon nasa ta sauya, amma na yau yafi ja, jan har yayi yawa. Tafida kayi addu'a yayi murmushi me ciwo yana kawar da kai itace abun da ako yaushe nake sanyi, amma kuma daga zarar na shiga irin wannan halin bana iya yinta, bakina nakeji yamin nauyi, hatta da harafi aya na larabci bana iya furtashi muktar ya girgiza kai cike da tausayin abokin nasa, wata iriyar rayuwa yake me cike da ban tausayi. Hannunsa ya mika baya, ba tareda ya ta6a bottle in ruwan dake kan kujerar baya ba, bottle in ta taso da kanta zuwa cikin hannunsa, ya dawo da hannun nasa gaba ri e da bottle in ya bu e ya kafa kai yana sha, zuwa yanzu sun shigo cikin kofar garin had'ejia, kuma sun hau titin fada, so yake ya samu yayi ya i da she anin ruhin nasa kafin su karasa fada. Bottle in ya aje a gaban motar, ya dafe kansa da hannuwansa, da muktar yaga haka sai ya shiga tofa masa addu'a duk wadda tazo bakinsa, bayan an wani lokaci ya ji e sharkaf da gumi, har ya ji a rigar yadin dake jikinsa. A hankali ya ago ya jingina da jikin kujera, yanajinsa ya dawo dai-dai, shed'anin ruhin nasa ya tafi, wayar idansa ta dawo ainihin blue inta. Da haka suka karasa katafariyar fadar garin hadeji, hadejia ginsau birnin doki, ta an abubakar sarki babba. Inji ja'e ha ejia. A gate in farko wanda aka tanada domin aje motoci muktar yayi parking, suka fito a tade, muktarb ya auka masa jakar dayazo da ita, gaba aya harabar fadar a cike take fal da jama'a, sbd bikin da za'a gudanar na yar sarki gimbiya amina,isarsa ba jimawa labari ya kara e fada akan Tafida ya shigo garin. Kofa ta biyu suka zo wucewa dogarai da hadimai sai kwasar gaisuwa suke, duk da shi Tafidan baya san hakan sam, shi baya d'aukan kansa daban da kowa, gani yake shi dai-dai yake da kowa, amma haka a'idar take, dan haka babu yanda zaiyyi face ya amsa, su kuma suna gaisheda shine sbd suna sansa, dan yafi yarima an uwansa halin arzik'i. Daga wannan gate na biyu suka shiga soro na farko a fadar wanda ya kasance soron masu gadi da tsaron fada a da, amma yanzu babu kowa a wajen sai masu wucewa, daga soron farko sai na biyu wanda shi kuma ya kasance soron malamai a zamanin da, wanda shima a yanzu babu kowa, sai kuma soro na uku wanda shi kuma ya kasance na oramai, sai soro na hu u wanda yake d'auke da wata babbar karaga ta sarkin hadejia, daga kasan kujerar wani lallausan yashine zube, sannan kujera a samansa, a duk lokacin da sarki ya sauko daga sallar jumu'a yakan tsaya a wajen ya zauna ayi fadanci sannan a tashi, daga shi kuma sai soron bayi, wanda kuma a yanzu yake auke da tsofaffun bayi na da, wanda har yanzu akwai sauransu, gaba aya saida Tafida yabisu ya gaisar sunata saka masa albarka sannan ya wuce, daga nan kuma wani tamfatsetsen filine, wanda ya kunshi hanyoyi hud'u, daya wadda zata sadaka da 6angaren matan sarki da kuma turakar sarkin, aya kuma wadda zata kaika ai nahin majallisun sarki, sai kuma wadda zata kaika 6an garen bayi da kuyangu na fadar, Sai ta murin dominan sarki. Nan in ma a cike yake da jama'a haka suka yanki hanyar da zata sadasu da 6an garen matan sarki, wata uwar doguwar tafiya suka yanka kafin suka iso ainahin inda bangarorin matan sarkin suke guda uku, wanda yafi kowanne girma suka nufa, kowanen gini akwai beni, amma kuma kuma irinsu aya sai na tsakiyarsu daya yafi girma. Aminttaciyarta suka samu tana fitowa daga ofar shiga, ta gaishe su tareda fa i bari tai musu iso, muktar sai ya tsaya yana fa na gama nawa aikin, na kawoka gida lafiya, dan haka sai anjima idan ka samu fitowa Tafida ya juyo yana kallonsa, sai kuma ya ta6e baki cikin aga kafa a, dan muktar ba balo bane, shi an gidane, ya karbi jakar tasa sannan ya saka kai cikin kofar parlon, tuntuni an masa iso wajenta, dan haka ya saka kafarsa cikin parlon kai tsaye daga parlon farko ta wuce na biyu, a nan yayi birki, kamshin turaren wutane ya fara ziyartar hancinsa, kafin a hankali ya fara bin parlon da kallo, baiga kowa ba sai himilin tarin kayan abinci akan coffee table, wanda yake da tabbacin nasa ne, yayi murmushi yana juya kai kafin a hankali ya araso cikin parlon saida ya shiga ya zauna, sannan ya lura da ashe bai rufe kofar ba, dan haka yayi nuniga kofar ya motsa hannunsa nan take kofar ta rufe kanta tareda motsawar hannun nasa. A lokacin ne kuma ta shigo cikin parlon, bakinta auke da sallama, ya aga kai ya kalleta yana mata murmushin me tsada, wanda ba a ko yaushe yake irinsa ba, dan har hakwaransa na bayyana, itama murmushin take har ta araso ta zauna a kujera kusa dashi, cike da girmamawa ya gaishe ta, sannan suka an ta6a hira ka an, dan ita izzar mulki ta mayar da ita muskila, shi kuma jinin mulki dake yawo a jikinsa yasa baya zantuka barkatai, abici ta fara gabatar masa sannan ta tashi ta bashi waje yaci abinci. Fulani khadija kenan, matar sarkin hadejia alh Abdullahi abubakar masu (c.o.n) shugaban hukumar sarakunan jahar jigawa, itace matarsa ta farko,bayan ita yanada wasu matan har guda biyu, fulani sadiya itace me bi mata sai kuma fulani usaibatu, fulani khadija sau aya ta ta6a haihuwa, itama kuma bayan sun shafe shekaru samada ashirin ita da me martaba da aure, tukunna ta samu, inda ta haifi arta mace me suna Nadra. Ita kuma fulani sadiya yaranta hu u a gidan, habibu shine na farko, kuma shine babba a cikin an me martaba, wanda yake ri e da sarautar galadima a yanzu, hakan tasa ake kiransa da sunan, ko kuma ace yarima, sai maimun wadda tayi aure suna zaune da mijinta a buja, sai amina da za'ayi aurenta yanzu, sai autansu nabil wanda ya kasance karamine bai wuce 10 yrs ba. Fulani usaibatu kuwa yaranta biyu, abbas da kuma amra, suke nan iyalan gidan me martaba alh Abdullahi abubakar masu (c.o.n). Abincin ya bu e ya iba ka an domin baya jin yunwa, idan kuma yace bazai ci ba fulani bazataji da i ba. Nadra ce tayi sallama tana shigowa cikin parlon, wani uban tsalle ta saki ha i da ihu yayinda tayi arba da Tafida zaune a parlo yanacin abinci. Bata san da Labarin zuwan sa ba, yanzu haka tana garden ne taji wasu bayi suna hirar wai Tafida yazo, shine tace bari tazo ta ganewa idonta, kansa tayi da gudu ta rungumeshi, ya aje plate in dake hannunsa shima ya ri eta yana murmushi me kama da dariya hamma yaushe ka zo ? ta fa i tana sakinsa tareda zama a gefensa jiya na zo Tayi dariya, inda sabo ta saba da wannan halin na Tafida, ya iya mannawa mutum magana, idanta ne sau a akan ar hadejian dake kwance a gefen fuskarsa, kusa da kunnensa gefen sajensa, ar hadejia tsago ukune sirara da haifaffun haidejia kanyi a gefen fuskarsu, kusa da sajensu wajejen kunnensu, hakan tasa aka sanya mata 'yar hadejia laa hamma kalli 'yar hadejan ka, ta kusa bacewa, dama nice, allah ba karamin cutar mutane suke ba da suke musu wannaan ar hadejan Tafida ya kai abincin bakinsa yana murmushi, kowani a dake fadar inhar ya ha a jini da fadar walau mace ko na miji to sai ka sameshi da wannan zane, kuma bama fada kawai ba har mutanen gari. Hannunsa ya kai ya tura sumar kansa baya, bawai dan ta sauko masa kan goshi bane, saide dan hakan ta zama abi'arsa a duk lokacin