← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 84

Sashe 2

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

28/11/2023 By sai kaska *proud of my first novel* *BABI NA DAYA (1)* *GABATARWA* Wannan littafin shine littafina na farko dana fara rubutawa,labarin YADDA ADDARA TA SO labarine wanda ya kunshi kirkira (fiction), ina kira ga duk wanda zai karanta wannan littafi, da yayi hakuri idan har yaci karo da wata hallaya ko abi'a wadda tayi kama da tasa. Na rubuta labarin ne akan rayuwar mutane hudu, TAFIDA, MARYAM, UCHENNA da kuma HANAM, bance na kware akan rubutu ba, wannan ne karo na farko dana fara, amma ina fatan zai kayatar ya kuma nishadantar, ha ibda ilmantarwa. *A wasu lokutan kaddara na faruwa a yadda ta so ba ayyada an adam yaso ba, a wa ansu lokutan kuma takan farune a yadda muka so, kuma mukan sowa kanmu abbu ya kasance ba alkairi bane a garemu, sannan mukan i abu ya kasance shine mafi alkari garemu, kamar de kullum Allah na nasa bawama na nasa, amma na Allah shine gaskiya, kuma YADDA ADDARA TA SO, hakane xai kasance, ku biyo ni cikin wannan littafin, domin jin YADDA ADDARA TA SO da TAFIDA, MARYAM, UCHENNA DA HANAM* Ina mika ginjina zuwaga ba. Manyan marubutan da nake alfahari dasu a koyaushe, ababen kwaikwayo na ( my role models) *sadi sakhna *khadija candy *aysha shafi'ee Haka kuma jinjina zuwaga ahalina baki daya * Alh Ahmad Isah Mahmud (mahaifina) * Hauwa'u Abubakar Haruna ( mahaifiyata) * Hafsat Ahmad Isah * Fatima Ahmad Isah *Amina Ahmad Isah *ST NICHOLAS HOSPITAL,LAGOS NIGERIA* wai ina dr. ESHAAN din ? wani likita da ake kira da dr. ola ya tambayi nurses din dake bakin aiki, yayinda ya fito daga dakin da aka kwantar da wani mara lafiya da aka kawo musu asibitin, nurse chinaza ce tace. sir Saturday, dr. baya zuwa ranar weekend ai nasan da hakan, amma dolene yazo, aikine na ceton rai, dan haka ku kirashi yazo da gaggawa ok dr joke ta fa i tana juyawa, hanyar office dinsu ta nufa dan wayarta tana can ah-ah joke to where ? joke ta tsaya tana kallon dr. khabir babban abokin dr. eshaan Offce namu zanje na auko wayana, zan kira TAFIDA ne wani abun ne ya faru ? ta gyada kai eh an kawo wani pertinent ne kuma ana bukatarsa ok jeki kawai bari na kira shi ta juya zuwa inda ta fito, shi kuma khabir ya fito da wayarsa daga cikin aljihun lap coat din dake jikinsa ya nemo lambar TAFIDA a jerin contact din dake wayarsa ya aika masa da kira. *ALARO CITY LEKKI, LAGOS, NIGERIA* Alaro city wani haddaden estate ne wanda za'a iya kira da gari, rukunin gidajene masu kyau, tsarin ginin gidajen kamar a kasar turai, kuma a kowani block tsarin gudajensu iri daya ne, sunada masallaci da church, super market, filin wassani,bpolytechnic, asibiti, makaranta duka a ciki. **** Sanye yake da Jersey irinta cricket, green color a bayan rigar an rubuta 'TAFEEDAH', wandon Jersey din ne a jikinsa wanda ya sauka har kasa shima kuma green ne, anyi layin fari a gefen wandon, guwar kafarsa sanye cikin abun kariya da an cricket ke sakawa a kafarsu ( batting pad), hannunsa sanye da safar hannu irin ta yan cricket, kansa sanye da helmet na cricket, hannunsa rik'e da cricket bat (sandar cricket). au matsayarsa, yana jiran joakim da zai cillo masa wallon, aiko yana cillowa ya takarkara ya daki kwallon da duka karfin da allah ya hallita masa shi, wallon ta tashi sama, kowa ya daga kai yana jiran yaga inda zata sauka, bata tashi sauka ba sai a ketaran layin da aka shata, aiko an team dinsu suka saka ihu sukayi kansa suna kiran sunan sa, dama sun sani idan har wasa da TAFIDAH ne basu da haufi, yana murmushi ya cire helmet din dake kansa, ai nahin surar fuskarsa ta bayyana. Dogone sosai, kuma fari, fari ba irin na Africans ba, fari irin na asalin Indians, ga sumar kansa irin ta asalinsa wato india, ta kwanta a kansa lif, cikin askin high fade, ga kuma razor part a gefe, ga wani bakin kwataccen gashi daya sauko tun daga sajensa ya had'e da wanda yake habarsa ya kuma zagaye bakinsa, kammanin fuskarsa sune suke tabbatar da asalinsa na ba'indiye. Kwatanta irin kyan da yake dashima b'ata lokacine, irinsa ake kira da end of discussion, wani irin kyau gareshi me ban mamaki, me kuma daukar hankalin me kallonsa, kwayar idonsa tafi komai jan hankali a fuskartasa, wadda ta kasan ce light blue color ce. Tsaye yake a inda ya aje cricket kit bag dinsa, yana saka kayan cricket din nasa a ciki, helmet itace a bu na karshe da yasaka a cikin jakar, sannan yayi zipping jakar. Hannu ya kai ya bide karamin aljihun jakar inda ya aje wayarsa da kuma p-cap in daya yazo da ita, p-cap in wadda aka rubuta TAFIDAH a samanta ya saka a kansa sannan ya bu e wayar tasa, missed calls ya gani daga Khabir, hakan ke nuna masa cewa akwai wani abun dake faruwa a asibiti, wayar ya saka a aljihun wandon dake jikinsa, sannan ya sab'a jakar a bayansa. Sannan ya kama hanyar fita daga wajen wassanin, cikin da takunsa na kasaita da izza da kuma aji, wanda yake nuna cewa shid'in jinin sarauta ne, duk da bayasan hakan, amma sarautar a jininsa take, ko ina yabi idan da mutane sai sun aga masa hannu shima kuma ya aga, dan ba wani sosai ya cika magana ba, amma kuma yanada kirki, kuma kowa ya sanshi a wajen. Kasan cewar filin wassanin da gidansa babu nisa hakan yasa yake zuwa a kafa, ko ina a estate din shimfide yake da kwalta, dan haka ya bi titin da zai sada shi da gidansa, ko ina ya wuce idan da an mata sai sun yasa, dan Tafida irin mutanannane wanda ba kowace budurwa bace zata ganshi ta kauda kai ba, Allah ya masa farin jinin an mata, tafiyarsa ma kawai abar kallo ce. Da haka ya karaso kofar gidan nasa wanda yake sak iri daya da sauran gidajen dake block insu, daga jikin gate din kuma akwai wani siririn allo da aka rubuta DR. ESHAAN AUWAL TAFIDA, B3 NO 122 Hannunsa na dama ya ago wanda yake sanye da digital watch, daga saman agogon kuma a kwai wani stamped bracelet, me dauke da rubutun 'TAFIDAH'. Aagogon ya dan daddana nan take gate din ya zuge zuwa gefe, kai ya saka cikin kyakyawan gidan nasa, yana shiga gate in ya kulle, ginin benine mai hawa daya, daga gefen ginin kuma glass ne tun daga sama har kasa, tun daga waje idan ka kalli saman gidan zakaga kujerun dake laye a saman rufin gidan, a parking lot din gidan kuma motoci uku ne, Audi RSQ 8-R, Honda elevate da kuma marsidis benz. ofar entrance din ya bude ya shiga ciki, babban falone a farkon kofar, wanda yake dauke da set din ima- iman kujeru, wata kofar glass ce ke facing din kofar shigowar, wadda zata sada mutum da garden din gidan, wanda kuma yake a backyard din gidan, stairs din da zai kai mutum sama kuma yana cikin falon, daga kasa idan ka daga kanka zaka iya hango ofofin dakunan gidan, domin corridor din dake kunshe da dakunan a ba katanga bace, glass ne aka saka kuma shima gajere, ofofu hudune a parlon, wadda suka kunshi kitchen, dakin guga, gym, sai store amma ba na kayan abinci ba, na aje kayan amfanin gida. Stairs ya fara takawa wanda zai kaishi zuwa dakinsa, wanda yafi kowani aki cikin dakuna uku dake gidan girma, komai na cikin dakin dark an light blue ne, sai kuma fari tun daga kan bad sheet, blanket, pillows, curtains, carpet harda set din kujerun dake dakin da dai sauransu. Cricket kit bag din bayansa ya sauke ya ajeta a inda ya saba ajewa, ya cire wayarsa daga aljihu ya dora akan gado, ya karasa inda dayar wayar tasa take chargy ya zare chargyn ganin ta cika ya ajeta itama a inda ya aje dayar. Ya dawo gaban dressing mirror ya cire agogon dake aure a haannunsa ya aje a kan table din, ya cire p-cap din dake kansa ya ratayeta a jikin hat stand din dake kusa da dressing mirror din,Sannan ya shiga wanka. Bayan wani lokaci ya fito daure da towel, yana goge jikinsa da wani towel din, a gaban dressing mirror din ya tsaya ya jona hand dryer ya shiga busar da sumar kansa, saida ruwan dake jikin sumar ya tsane sannan ya dauko hair straightener dinsa ya shiga taje gashin nasa, sannan ya dauko man daya saba shafawa sumar tasa ya shafa nan take ta soma kyalli, ya gyaggyara zaman gashin dake takiyar kan nasa, dan a gefe da gefen kan nasa da kuma baya babu sumar sosai, an asketa sbd askin high fade din da yayi. Jikin faffa ar lokarsa ya koma, wadda ta kusa cinye fadin katangar da take jiki, ya bude kofa daya, saida yayi taku daya biyu kafin ya isa shiga cikin wardrobe di, dan lokar ar bangoce, kuma kamar closet, manyan kaya ya zabo wani plane yadi golden color, ya saka a jikinsa ya fito daga wajen hannunsa rike da hula tangaran, yana gyara karin hular. Saida yazo gaban mirror ya saka hular a kansa sannan ya feshi jikinsa da turare, ya dawo wajen shelve din dayake aje takalmansa ya dauko wani bakin moccasin ya saka a kafarsa, sannan ya juyo ya dauki wayoyin nasa a inda ya ajesu, ya dauki keyn daya daga cikin motocinsa ya fito, benz insa ya shiga ya wuce ST NICHOLAS HOSPITAL. A babbar rumfar da a samanta aka rubuta Dr. ESHAAN AUWAL TAFIDA yayi parking, ya fito yana ta gaisawa da ma'aikatan dayake haduwa da su, har ya kai office insa, kuma tun kafin ya shiga cikin office in nasa yaci karo da khabir, hannu ya bashi sukayi musabihi suna gaisawa sannan yace ai na kiraka baka d'auka ba, kuma dama nasan kana filin cricket saida muka gama wasan naga kiran naka ai, shine na shirya na taho yayi maganar cikin yaran hausa, wadda ba zaka taba tunanin yasan hausarbama ballantana ya iyata, ga kuma suturar dake jikinsa, wadda take kara dangantashi da hausawan me ke faruwa ? ya fa i
Chapter 2 · 0% Book details