Sashe 4
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
YADDA ADDARA TA SO By Sai Kaska * proud of my first novel * *BABI NA BIYU (2)* * HANAM FASHION HOUSE, GWARINFA ABUJA, NIGERIA * A hankali cikin natsuwarta take tafe sanye take cikin wani farin wide leg pant, sai wata bakar shirt, wadda ta ora mata farar suit a sama, hannunta rike da jakarta wada ta kasance itama fara, gashin kanta cikin stail din braid (wato kalba) guda aya, wadda ta sauko da ita kan kafa arta ta dama, ta saka robber band a karshen kalbar sbd kada ta warware, dan tsabar santsin gashin kan nata,daga karshen gashin nata tai masa kala da brown yayinda saman kuma yake ba i, ta dora ba in mayafi asaman kan nata, kamar yanda babu fara'a a fuskarta haka babu kwalliya. Daga bayan ta kuma naani in data auka domin kula mata da anta a office dinta ce biye da ta, yayinda take auke da dan nata cikin baby carrier, idan ka kalli uwar ka kalli an, baka bu atar arin bayani akan anta ne, sbd tsabar kamar da suke, banbancin su shine shi kalar kwayar idonsu ce, sai kuma farin da an nata ya fita. Daga ita har an nata kana ganinsu kasan cewa half cast ne, duk da ita hasken fatarta kamar na indiyawa yake, dan nata kuma kamar an larabawa. Ko ina ta wuce a office in sai an gaisheta har ta kai office inta, yayinda naani in kuma ta wuce da yaron zuwa akin data tanada domin renon yaron nata. Executive chair in dake office in taja ta zauna, sannan ta aje jakarta a kan table in dake gaban kujerar tata, ta janyo ipad dinta ta bu e domin ta fara duba wasu sabbabin design din dinkuna. ***** Motarta kirar hybrid take tukawa akan titi, bayan ta tashi daga aiki, yayinda anta sanyin idaniyarta ke zaune a seat in me zaman banza, cikin car seat dinsa. Jifa-jifa take juyowa tayi masa wasa, a gaba ayan rayuwarya bata da wani abu me mihimmanci bayan wannan dan nata da kuma mahaifin ta, su ka ai tasan tanada su, batajin tana san kanta kamar yanda take sansu. Yau ta kama ranar zagayowar haihuwarta, bayan mahaifin ta da baya gari babu wanda ya kirata ya tayata murna, kuma dama hakance ta saba faruwa da ita a duk shekara, wattanin baya ita ka ai ko ita da mahaifinta suka shagalin murnar zagayowar ranar haihuwartata, gashi kuma yau mahaifin nata baya gari, dan haka ta yanke shawarar yin shagalin daga ita sai anta. Dan haka ta parker motar tata a gaban chedi plaza shopping mall, ta ciro dan nata daga cikin car seat din dayake ciki, ta daukeshi a hannu ta nufi cikin mall in. Bayan dan wani lokaci ta fito daga mall din hannunta rike da leda me dauke da tambarin mall din, wanda aka sako mata dan karamin cake din data siya a ciki ( bento cake), ta dawo ta zaunar da yaron a seat dinsa ita kuma ta zagaya ta shiga driver seat taci gaba da tuki. A gaban ma araren gidan nasu ta tsayar da motar ta danna horn cikin salonta, wanda bayan ita da me gidan kansa babu wanda yake irin wannan horn in, hakan tasa me gadin nasu bu ewa gate in cikin sauri, dan ya gane cewa itace, sbd me gidan baya gari. Shigowa tayi da motar tata, tayi parking a parking lot, ta fito daga motar ta auki yaronta ha i da jakarsa da kuma tata sai ta ledar cake in data siyo. A babban parlon gidan nasu ta samu kowa na gidan, tun daga iyayen yaran har yaran, bata ko kalli inda suke ba ta haye tagwayen benin dake parlon domin shiga akinta mtswww!, aikin banza, wallahi na tsani ganin yarinyar nan, idan na ganta ji nake kamar na bita na shake mata wuya ita da wannan shegen an nata Cak ta tsaya daga tafiyar da take, ta juyo a hankali ta kalli babban yayanta kamal dake wannan batu, a hankali ta aje jakukunan hannunta a kasan tiles in dake saman stairs in, dan har ta kai arahe, sau owa ta farayi tana tunkarar cikin parlon ya kamal gata nan fa zuwa anwarsa na'ima ta fa i tana kallonta, mahaifiyarsu hajiya mero ce ta buga uban tsaki sai me kuma idan ta zo ?, ko dukansa za tayi ? Gabansa tazo ta tsaya, shima ganin hakan yasa ya mi e tsaye, harma da kowa na parlon kamal kake ko wa ?, kada ka ara jifan ana da kalmar nan ta shege!, ana yanada uwa kuma yanada uba, kuma duka nice, dan haka ana ba shege bane, ka ri a kula da kalamanka, idan har a kaina zasu tsaya ba zan tanka maka ba, amma idan har suka etara layi zuwa kan ana" tayi wani murmushi me ciwo zan koya maka hankali kaida wannan uwar taka da bata gabana, bana shiga sabgar kowa, dan haka bana bu atar kowa a tawa sabgar, ana anane, babu wani wanda keda iko dashi, ka fita sabgarsa ke !, dan tsabar baki da mutinci akan wannan sheg...... Bai samu damar karasawa ba, sakamakon marin data sakar masa a kumatumsa na hagu, ya dafe wajen idanunsa waje yana kallonta, bama shi ka ai ba, kowa dake parlon saida ya kama baki yana kallonsu su duka, cikin mamaki, a da idan sun maga abu bata kula su sam, amma gashi yanzu harda mari ke hanam dan baki da hankali shine zaki mari ya kamal ? Kanwar kamal in rahina wadda suke uwa daya ta fa na mareshi in, ko akwai me rama masa ?....... Kai kuma Ta fa i tana juyowa kan kamal in dake dafe da kunci yana kallonta da tsananin mamaki na fa a maka cewa ka fita sabgar ana, dani kake fa a ba dashi ba, kuma ana ba shege bane, nice ubansa mark my words Tana kaiwa nan ta bar wajen a fusace, ta bar kowa da baki a sake yana kallonta, dama sun saba mata cin kashi, babu kalar ba ar maganar da basa fa a mata, tanayin ha uri ta shanye, amma yau sun kaita bango. Zaune suke a ha en dakin an nata, wanda bai cika girma sosai ba, saide cike yake da kayan wasa kala-kala, yaron na zaune cikin floor seat, yana wasa da rattle insa (kacar-kacar), sanye yake cikin onesie (over rall)baka. Yayinda hanam ke zaune a gefensa cikin Wata linen tunic dress, rigar dama ta zaman gidace, bento cake in nan ta dauko ta bu eshi daga cikin take away in da aka saka shi 'HAPPY BIRTHDAY' shinr abinda aka rubuta a jikin cake Aryaan, yau mummy take birthday, let's cut the cake Ta fa i tana kallon yaron, kamar wani babba haka take magana dashi, dan hatta dariyarta da mutane suka dena gani cikin wannan shekarar toshi tana masa, karamar wuka ta dauka ta yanka cake in tana wakar happy birthday, cake in ta yanko ta kaiwa yaron baki, yaron ya bu e ya karba yana ci, itama ta yanko ta saka a nata bakin, tana masa wasa ta dauki tisseu ta goge hannunta sannan tana kallon yaron ta fara cewa abu ummuh an nas bi ulu innak ibn gair shar'i, bas ummak bita'arif innak shar'i, li'anna hiya yalli wulidtak, wa rabaitak, wa aitak killil hub, ya ibn hayyi duniya yalli nahni fiyya annas ma bihibbul kil, bihibbu nafsun wa bas, bas saddi ni ana kitir bihibbaka, wa ana ba'arif innaka bta'arif hasshi sah? (Baban mamansa mutane suna cewa wai kai shegene, amma mamanka tasan cewa kai ba shege bane, sbd mamanka ita ta haifeka, ta reneka, kuma ta baka kowace iriyar soyyayarta, ana wannan duniyar da muke ciki ba kowa ke san wani ba, kansu kawai suke so, amma ka yarda dani dan ni ina sanka sosai kuma nasan kaima kasan hakan ko?) "Abu ummu ta'al ila huna (baban mamansa zo nan)" Tayi maganar tana daukansa ta rungume shi a kirjinta tana pecking kansa ni bazan taba guduwa na barka ba, kamar yanda tawa mahaifiyar ta gudu ta barni MARYAM POV Zaune suke gaba dayansu akan babbar tabarma, ita da maanmu da muhsin suna cin jallof in taliya da waken da Maryam in tai musu da daddare, yayinda hussain da hassan suma suke cin nasu daban, hussain sai zabga santi yake, dan idan batun girki ne to Maryam ba daga baya ba Kinsan allah yaya, ni ji nake na kamar akawai kifi a ciki Maryam da maanmu suka masa dariya, banda muhsin dake shirgawa cikinsa abinci, da kuma hassan da dama shi can miskili ne au dariya na baku ? eh mana, muhsin auko pillow nai masa waigi, dan naga iris ya rage ya fa i..... Sallamar mahaifin suce ta tsayar da hirar, ya shigo cikin gidan yana musu kallon aya, wanda hasken fitilar da suka kunna ya bashi damar ganin fuskokinsu, sigarinsi yake busawa kamar kullum, Maryam, hussain da muhsin suka masa sannu da zuwa, yayinda maanmu da hassan ko takansa basu bi ba, kuma kamar yanda ya saba babu wanda ya kula a cikinsu, idan da sabo sun saba, amma kuma kullum basa fasa gaidashi ina abincina ? Hassan ya zaburo zaice, ya basu ku in abincin ne ?, hussain ya ri e hannunsa yana girgiza masa kai, hassan yaji kamar ya saka ihu dan tsabar takaici, hussain ya juya ya kalli Maryam. yaya ki zubawa abba abinci Maryam ta mi e ta nufi rumfar da suke girki, maanmu taji wani malolon takaci ya tsaye mata a ma oshi, kamar yanda ya saba ma ale mata a duk sanda zata kalli tijjani a matsayin mijinta. Sam bata san ta ri a sa'insa dashi a gaban ansa, dan sam bata san su renashi kamar yanda hassan ya rainashi, shi kullum babu ruwansa da ya suka tashi?, yaya suke?, shin suna cikin halin bukata? ko aa, babu ruwansa da cinsu, shansu, sitirarsu, kula da lafiyarsu, duka bai damuba. Maryam ta dawo hannunta rike da wani aramin food flask ta tsugunna ta mika masa, a wula ance ya kar6a sannan ya juya ya fice daga gidan, da alama yau bazai kwana a gidan ba. Maanmu taji wata kwallar ba in ciki na shirin sauko mata, amma sai ta dake, ta hana