← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 84

Sashe 60

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba ta fice. Har saida ta ule masa sannan ya lura da lunch box in nata, ya yi murmushi sannan a hankali ya furta. Uwar tsoro! Lunch box in ya auka sannan ya fita, dan ya san ajinsu. Kamar kullum yauma sanye yake cikin manyan kaya, wata green in shaddace a jikinsa, kansa babu hula, dan yanzu ya tara gashi da yawa, kuma idan ya saka hular bata zama, shi yasa ya dena sakawa. Ko da ya shiga class in nasu sai yaga babu malami a ciki, ya shiga dube-dube, can ya hangota a karshen benci, ta kifa kanta a kan desk, kamar kuka take kuma kamar me bacci. Be yi wa kowa magana ba ya shiga cikin ajin, idon 'yan matan ajin kamar ya fa asa dan ganin Tafida a ajinsu, shi kuma bai kula kowa ba. Zara da Aisha ne suka juyar da kansu gefe, basa so su ha a ido da shi, dan basu sani ba ko Maryam ta fa a masa abin da suka yi. Miriam! Kamar a mafarki Maryam ta ji muryarsa tsaye a kanta, kai ina taya za'ayi ma yazo wajen, sai dai kuma tunawa da ta yi a mota ta barashi, bataga tafiyarsa ba, yasa ta ago da sauri, shi in ne kuwa tsaye a gefen desk inta. Ya Allahu ya Allah, wai shi be san halin da take ciki bane?, me yasa yake mata haka?, wallahi idan akaci gaba da haka zai iya zautata.... Lunch box in ya mi a mata sannan yace. Kin manta wannan Ta yi sauri ta karb'a, tana bin 'yan class in da kallo, gaba aya ido ya dawo kansu, kallonsu ake daga ita har shi, wasu na mamakin ala ar da ta ha asu, wannan de baya kama da ita ta ya za'ayi ace yayanta ne, sai dai ko saurayi, kusan irin wannan tunan ne a kan kowa dake ajin. Maryam ta ha iye wani abu sannan ta juyo ta kalleshi, yana nan tsaye be tafi ba. Kuka ki ke ? Da sauri ta girgiza masa kai. Me yasa ki ka kifa kanki a kan table ? Kode ta fa a masa cewa abinda yake mata ne yake sata take nitsewa a cikin lake chad ?,a'a ko zata fa a masa ba'a nan ba, nan ba wajen maganar su ba ne, ita da zai temaka mata ma ya tafi, da sai tafi jin da in ranta. Babu komai, haddata ce bana so ta....ta zube Ita kanta sai da ta sarawa kanta da wannan aryarta ta, zubewar hadda kuma ta nawa ?, ai tun da leb'ensa ya sau a cikin nata haddar ta zube, saide ta sake sabon lale. Ya cije leb'ensa yana kallon ta, dariya ce take san kama shi, amma ba zai yi dariya a nan ba, dariyarsa ta makusantanasa ce kawai, ba wa al'uma duka ba, shi yasan kome take, ba hadda take san ri ewa ba, jinyar gangar jikinta take sbd ya yi kissing inta. Ok ki kula, Allah ya temaka, Allah ya bada sa'a Da fatar bakinta kawai ta amsa ameen in, shima kuma yana kaiwa nan ya fice ya bar matan ajin da bin bayansa da kallo, Maryam ta kallesu takaici na san kamata. Tafida na fita suna dawowa da kallonsu kanta, suka iyo kanta zasu tambayeta amma Zara ta dakatar su ta hanyar fa Ba sai kun tambaya ba, mijinta ne Maryam ta kifa kanta a kan desk, sbd kallon da suke mata. *R NO 147,JJ hospital, byculla, Mumbai, India* kan gadon marasa lafiya, Galadima ne kwance, yayin da rabin jikinsa yake a rufe, ya ara ramewa ya yi ba i, kansa ya langwab'e daga gefe, bakinsa sai zubar yawu ya ke, yanzu maganama ba ya iya yi, hannayensa da afafunsa kam sam basa aiki, ko zama baya iyawa sai an zaunar da shi. Da ga kan wata kujera kuma Fulani Sadiya ce, wadda idan ba kasanta sosai ba a da, to baza ka ce ita bace a yanzu, ta rame ta zama wata iriya, tsabar tashin hankali, an da ta saka buri da rai a kansa, shine yake kwance yau a cikin wannan hali, sai an kwantar sai an tayar. Bama wannan bane abun damuwar, da suka zo asinitin saida a ka masa general test, kuma a nan ne a ka asanar musu da cewa yana shaye-shaye. Sai a yanzu ta gane cewa duk abinda takewa Tafida kan anta yake komowa, babu aya dake samunsa duka. Ta yi kukan ba inciki dana nadama fiye da irgenta, gashi ta yi magana da boka kan a san yanda za'ayi a warware asirin, amma bokan sai ya tunasar mata da cewa itafa tace kada ayi wanda zai tab'a karyewa, kuma shi ya mata. ofar shigowa aka turo, me martaba ya shigo, ta aga kai ta kalleshi sannan ta sau e, takowa ya yi zuwa kan kujerar da take zaune. Ya me jikin ? Ya tambaya yana kallon Galadiman da ke kwance a kan gado, Fulani ta kalleshi itama. Jiki da godiya Tafida ya kirani, ya fa a min cewar nan da wani satin zai shigo india, kuma zai zo ya duba shi Wata wallace ta kufce mata, wallar nadama da kuma ba in ciki, duk halin da anta ke ciki itace sila, yanzu shi Tafidan da take komai dominsa shine ma wanda zai zo ya duba shi, bayan ko ga miciji basa yi. A ranta ta shiga jero istingifarin da ya zame mata jiki akwanakin nan, so take ta nemi yafiyar Allah, wata ila ya yafe mata kura-kuran da tavyi, amma tabbas tasan cewa ita me lefi ce gareshi, shin anya ma kuwa zai yafe mata ?. _________________ _Fulani Sadiya is asking, shin za'a yafe mata ?, kun san shi Allah gafurun rahimun ne, sanan kuma ba'a shiga tsakanin Allahbda bawansa, to a har kullum de, Allah yasa mufi k'arfin zukatan mu, Allah ya tsare mu da aikata da na sani_ _Wai nace ba, kowa fa ya shirya jakarsa tsaf, dan bana naga k'aunar nan india zata kaimu, k'asar masoya ba, to ku ci gaba da zuba ido, dan jin yanda ta fiya india zata kaya, A har kullum, nice ta ku SALMA AHMAD ISAH(Wato SAI KASKA), na gode mukubda goyon baya._ SAI KASKA CE YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Tiktok @SAI_KASKA Arewabooks @18saikaska Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *Wannan naki nw Deejamah* *BABI NA TALATIN DA TARA (39)* *Hanam fashion house, Gwarinfa, abuja* HARIS POV. Me ya faru ? Ya tambaya yana kallon Hanam data kirashi tace yazo. Sai kawai ta girgiza masa kai, sannan ta auko wani aramin envelope ta mi a masa. Kasan SSGF ai ? Ya karb'i envelope in yana kallonta sannan ya kalli envelope Mall in Falaq ? Ta jingina da jikin kujera tana gya a masa kai. Eh ita, kaje ka kai mata wannan pls Har zai ce wani abu, amma sai kawai ya yi shiru, ya mi e zai fita, ofar da aka turo yasa shi dakatawa. A razane Hanam ta mi e tsaye, ganin wanda ya shigo, bakinta a bu e take kallon su ayen idanunsa, wanda ya kafa mata su yana kallonta, a take wurin ya fara sauyawa a idonta. Office in ya riki e ya koma mata ofar gidanta na USA, yanda yake kallonta a yanzu haka ya kalleta a time anan shu ayen idanuwan irin wanda Arya ya gada daga wurinsa. Da yar fatar vakinta ta furta sunan da ta ri e ta yi haddarsa a cikin kanta. Gabriel!! *Flash back......* A shekarun baya Hanam fashion sun samu takardar kwantiragi da ga kamfanin The House of Sofia couture dake New York USA, suna bu atar da C.E.On Hanam Fashion house da ta zo ta yi aiki dasu na shekaru biyu. Sun yi yarjejeniya a kan hakan, sannan suka tsara komai. Har zuwa lokacin da Hanam in ta shirya ta tafi can USA Sun fara aiki cikin nasara, domin komai na tafiya dai-dai, kuma sunajin da in aiki da Hanam Wata ranar monday, wadda Hanam ta kira da ba ar rana. Ranar da ta mata mugun tabo a dayuwarta, ranar da ta zama sanadiyyar shigowar wani haske rayuwarta, ranar da ta zana silar rushewar rayuwarta. Zaune suke ita da abokan aikinta a office insu, a lokacin kusan 10:00pm, sun gama ha a kayansa za su fita. Guys, me zai hana muje bar yau Cewar Camilla A'a ni bana shan giya Hanam ta fa i tana bu e musu ofa. Ai ba sai kin sha ba, kawai muje mu anyi rawa Cewar Tomas, ba haka Hanam taso ba amma taga suna san hakan, dan haka ta furta abinda ya rikito da duniyarta daga sama zuwa asa, kalaman biyu ne, amma fasirinsu ne yasa komai na rayuwarta hargitsewa. Ok muje! *3679 st, Queens, New York Doha Bar lounge* Wurin cike yake da 'yan mata da samari, banda ki a me arfi babu abinda ya ke tashi a wajen, wasu na zaune suna shan barasa, wasu kuma na rawa. Haka su Hanam suka shigo wajen, gaba aya sai wajen ya bata yami, ita bata tab'a zuwa irin wajen nan ba. Daga can inda babu mutane suka zauna, Camilla ta yi musu oder na giya, tasa a kawowa Hanam ruwa kawai dan shi tace tana bu ata. Gabriel kalli can! Kyakyawan baturen me blue eyes da farar fata irin tasu ta turawa ya juyo ya kalli inda abokin nasa ya ke nuna masa. Wacce da ga ciki ? Ya tambaya yana rarraba idanunsa a kan matan biyu dake wurin. Balarabiyar mana Ya saki wani kasaitaccen murmushi a sanda ya ha a ido da ita. Tana da kyau, bari naje na gwada sa'ata Yana mi ewa abokan nasa suka saka ihu suna masa tafi. Hannunsa ri e da wine glass wanda ke auke da giya ya arasa wajen da suke zaune. Sannun ku de 'yan mata Camilla ce tace. Gabriel sannu Baki washe ta furta hakan, dan duk wanda ke zuwa doha bar yasan Gabriel, musamman 'yan mata da ke matowa a kansa. Menene sunanki kyakyawa ? Hanam bata ko kalleshi ba, tun azu da suka hada ido ta ji tsanarsa ta daki irjinta, ta tsani mashayi. Maganafa
Chapter 60 · 0% Book details