Sashe 72
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallon an matan, sannan ta ara kallon saree in, jar kala ne, an masa ado da wasu golden stones, kuma yadin sa silk ne, hakan ke ara nuna mata tsadarsa, duk da ba wani sanin kan saree d'in tayi ba. Ba ni na siya ba, mijina ne ya siyo min Aiko mijiniki yana sanki, saree in ki kud'insa aya da na amarya Maryam ta kalli sareen da ke jikin amaryar sannan ra kalli nata, kusan kallarau aya ma, dan hatta da kalar blouse d'in iri aya ce, kawai de yanda aka jera stones d'in jiki ne ya banbanta. ...Kai ga tawagar ango sun iso... wata matashiyar budurwa da Maryam ta ji suna kira da Rakshi ta fa i baki washe. awayen amarya suka shiga gyarta, dan dama jama'a sun jima da fara taruwa, ita Maryam ba wannan ne ha dameta ba, duk da tasan cewa ba al-adarsu aya ba, dole de ango idan zai zo wajen ya taho da abokansa, kenanan Eshaan na tare da su?. Ba ta yi tunanin komai ba ta mi e, ta auki wayarta da wani golden mayafi ta yafa a kanta, dan bazata iya yawo kanta a bu e ba haka. Ta cikin tarin firmitsin jama'ar da suka taru a gidan tabi har zuwa bakin ofa inda take jiyowa ki e-ki Waje ta ja ta tsaya tana kallon ikon Allah, ango da abokansa dama 'yan uwansa sun iso gidan, sai ti ar rawa ake ana watsa ku i. Ga masu ki a suna aikinsu. Cikin abokan ango ta hango Eshaan,sai daj shi ba rawar yake ba, tafi kawai yake yana fito. Cikin tarin jama'ar wajen ya hangota a gefe, ba zai ce yasan daliliba, amma se yaga babu kowa a wajen, duk wannan hayaniyar da ke tashi a wajen babu ita. Babu kowa sai itan da yake gani, sanye cikin red silk saree, me ratsin golden, wuyanta hannayenta da kanta dauke da jawellies, babu wata kwalliya da yawa a fuskarta. Amma kuma ta yi kyau, domin ta yafa wani golden in viel a kanta. A hankali afafuwansa suka shiga takawa setin inda take, kallonsa take yayin da shima yake kallonta. Ina ka shiga Sundar ? Muryar Maryan ta tambaya da arfi ta cikin ki a da hayaniyar da ke tashi a wurin. Eshaan ya lumshe ido sannan ya bu e yana ci gaba da kallonta. Kinyi kyau Wifey Sai ya fa i hakan me makon ya amsa mata tambayar da ta masa. Me ?, azuma fa sai da ya fa amata hakan, me yasa yanzu ze sake ?. Mu shiga ciki, za'a fara gudanar da aurun auren Muryar sa ta fa i, ta cikin hayaniya da ki an dake tashi a wajen, hannunta ya kama ya shiga janta har zuwa cikin farajiyar gidan inda za'a gudanar da aurin auren. A kijerun gaba suka zauna, har yanzu idonsa a kanta ya kasa janyesu, hannunsa ya kai ya gyara nata zaman veil A lokacin kuma ango da an uwansa suka araso wajen, har yaje ya zauna a wajen da aka tana da domin shi, Suwami ya shiga jero addu'o'i. Kafin aka kawo amarya, itama ta zauna a kusa da ango, aka ci gaba da yin addu'o'i, sannan aka bawa ango red Tikka (wannan jan garin da matan auren an addinin hindu ke sakawa a tsakiyar gashinsu, alamun suna da aure). Ango Mahesh ya sakawa Amarya Komal tikka a tsakiyar gashinta daga gaba, sannna aka ma o mangalsutra, (sar ar aure). Ango ya sakawa amarya, sannan suka mi e, mahaifin amarya ya zo ya aure mayafin amarya dana kafa ar ango, sannan suka shiga zagaya wuta. A lokacin kuma aka shiga rabawa jama'a fure suna watsawa amarya da ango, yayina da shima Swami ya mi e yana karanto addu'ar aure. Mangalan fagbani bishnu mangalan madradda shar, mangalin gundari fakshar mangala yatarobari...... Har zuwa arshe. Eshaan da Maryam suka mi e a sanda suma aka mi a musu fure suka shiga watsawa amarya da ango. Maryam na watsa kamar kowa sai ji ta yi ita kuma ana watso mata, ta juya ta kalli Eshaan, yayin da kowa ke watsawa amarya da ango shi kuma ita yake watsawa. Ta saba ganin irin wannan auren a Tv, yau gashi a gaban idonta tana ganin yanda ake aura shi. SAI KASKA CE YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Tiktok @SAI_KASKA Arewabooks @18saikaska Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *Wannan naki ne Rahma Musa Hussaini* *BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI (47)* {ESHAM} *R 78, TC Maurya Hotel, New Delhi, India* *11:15pm* Dama Mahesh ba musulmi ba ne? Muryar Maryam ta tambaya, yayin da take shirya kayan sakarwarsu a cikin jaka. Eshaan da ke zaune a kan gado yana danna system ya juyo ya kalleta. Eh, an addinin hindu ne, ai ina jin kaf abokamu daga ni sai Arjit ne musulmai Ta gya a kanta tana zipping in jakar, sannan ta ajeta a asa kusa da wardrobe. Ta shiga ban aki ta auro alwala, ta fito ta saka hijabinta, sannan ta kwanta a,kan gadon, tana kallon Eshaan dake gefen gadon har yanzu yana danna system. Yanzu gobe gida zamu koma ? Sai ta ga ya dakata da danna systen in, kafin ya juyo yana kallonta ta cikin an guntun hasken da ya rage a akin. Indian ta isheki ne ? Sai ta gyara kwanciyarta tana girgiza masa kai. Naga mun gama komai ne, to me zamu jira ?, ko akwai inda zamu sake tafiya ? Sai ya girgiza kansa yana rufe laptop in, sannan ya ajeta a kan bedside drawer. Ya kwanta yana jan bargon, kansa na kallon sama yace. Mun gama zuwa ko ina, kawai de ina ga ya kamata a ce mun an yi yawo a delhi arashe ya na juyowa ya kalleta, itama shi take kallo. Ina zamu je to?.... Ta tambaya a sanda yake kashe sauran fitulun da suka rage a akin, Maryam ta rintse idonta tana anme pillown da take kwance a kai, har yanzu bata dena tsoron duhu ba, kullum zai kashe wuta sai ta tsorata. Hannunsa ta ji yana lalubar nata, kafin ya ha e tazarar dake tsakaninsu ya janyota jikisa, kanta ya sau a a kan kafa arsa, hannayensa biyu duka suka kewaye waist inta. Maryam ta ara du unewa a cikin jikinsa, a hankali ya lalubo kunnenta sannan yace. Akwai wurare da yawa da zamu iya zuwa a Delhi, Qutub Minar, India gate, safdarjung tomb, Humayun's tomb, lodhi art district suna da yawa sosai, ina so ki yi yawo sosai a india Maryam ta ara matse jikinta dake cikin nasa, har wa yau ta kasa sabawa da wannan yanayin. Yanzu de ki kwanta ki huta, dan a gobe zamuje mu zaga gari, kuma a goben jirgin mu zai koma nigeria, kinsan idan mun koma lagos kwana biyu za mu yi mu tafi ha ejia *Chida Event Center, Jabi, Abuja, Nigeria* *07:40pm* HANAM POV. Babban akin taron a cike yake ma il da jama maza da mata, daga can wajen zaman amaryam da ango kuwa Kamal Muhammd Haku au ne da amaryarsa Kalisa Usman. Daga b'angaren zaman dangin ango kuma gaba aya an uwansa ne maza da mata sai hira ake ana cin abinci, kallo aya zaka musu ka fahimci cewa suna cikin tsantsar farin ciki. A cikin su kuma akwai Hanma. Wanda itama ke sanye cikin irin nasu kayan, kuma harda ita ake hirar. Ya Hanam wai ki zo inji Ya Harees! Nabila ta fa a mata da arfi, kasan cewar hayaniya da ki an dake tashi a wajen. Ta juya ta kalleta sannan ta mi e tsaye. Hanam wai Ina Aryaan ne ? Ta juyo ta kalli Hafsi, sannan kuma ta shiga hange-hange ko zata hango shi, ita rabonta da shi tun da safe. Allah ya temaketa ta hango shi zaune a kan wani table. anenta maza ne gaba aya a kan table in, hatta kayan da ke jikinsa ma irin na su ne. Ta nuna wajen da hannunta. Gashi can a wajen su Hafiz Bari naje na karb'o shi, ai basu ka ai suke san sa ba Hanam ta yi dariya tana tafiya, sai kuma ta tsaya ta juyo ta dawo wajen tana fa Nabila yana ina ? Ni dai a waje na ganshi, ki duba cikin motarsa Sai ta gya a kanta, sannan ta fita daga wajen da yar sbd tarin mutanen dake wurin. A parking lot taga motarsa dan haka ta je ta bu e zata shiga gaba, amma sai taga baya gaban, yana baya, ta rufe ofar gaban ta bu e ta bayan sannan ta shiga. Kuma tana shiga ya janyota jikinsa ya rungume. Wai bakwa tausayi na ne?, kun barni daga ke har Arya Hanam ta sa ala hannayenta ta wuyasa a sanda ya saketa. Kamar baka ci abinci ba ma Sai ya gya amata kai. Tun safe banci komai ba, kinsan mu ne abokan ango, duk gwagwarmayar da akayi da mu akayi ta Awwww, Alah sarki rex (king), sannu Ya kai hannunsa yana janyo wata leda dake gidan gaba na motar, ya aje mata ledar a kan cinyarta bayan ya auko. Ga abincin nan, a bani na ci anyi dariya tana bu e kayan dake cikin ledar. Sannan a lokaci guda ta ago ta kalleshi cikin hasken futulun waje dake shigowa cikin motar, farar shaddace sanye a jikinsa, kansa harda hula, kuma ta ga kayan da ke jikinsa irinsa ne a jikin ango, dan yanzu sun iki, aminta suke shi da Kamal kamar wa an da suka ta so tun yarinta. Ni fa na yi tunanin Mama zata zo Uchenna ya jingina da jikin kijerar motar yana cire hular kansa, sannan ya shafa kansa. Wai Zakiyya ce za ta yi graduate, shi yasa bazata zo ba Hanam ta bu e wata roba tana saka spoon a ciki. Ai mu ma kuwa ya kamata a ce munje, ka je wurin Baba yau ? Ta kai masa lomar farko tana masa tambayar, ya ha iye abicin da ya gama taunawa sannan yace. Da safe kawai naje, amma ban koma ba, wata ila kafin mu koma gida sai muje Kaida wa ? Ni da ke Ya amsa mata yana karb'ar abincin da take