Sashe 30
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta india ce, sai wani jeans dake jikin nasa, gashin kansa a jike ya sau o kan goshinsa, alamun de wanka ya yi, idonasa manne da wani ba in glass me duhu, kamar kullum fuskarsa babu fara'a babu akasinta, sai ya fito kamar wani jarumin Bollywood. Kamar yanda take kallonsa shima ita in yake kallo, bai jima da dawowa daga filin wasanin ba, sbd Khabir da ya kirashi yace masa ansamu hijaba nan, kuma gashi nan a hanya zai kawo masa su, bayan ya fito daga wankan ne ya kalli idonsa a mudubi yaga wayar idonsa tayi ja. Shi kam ya fara tabbatarwa da maganar su Fulani, da suka ce masa wata ila Maryam itace maganin matsalarsa, dan kusan sati biyu kenan rabon da ba in ruhinsa ya tashi, kuma duk ya danganta hakan ne da shigowar Maryam rayuwarsa. Baya san ya ri a tsorata Maryam shi yasa ya saka glass in, Abinda ya saba ya shiga yi, wato sauraron bugun zuciyarta. A hankali cikin takunsa na kullum ya fara takowa cikin kitchen in, still idonsa a kanta, ita kuma sai ta kawar da idonta a kansa ta ci gaba da jera raspberry in da take jerawa akan cheesecake in data hada. Yaushe ka dawo ? Muryar ta fito ba tare da ta kalleshi ba, tana ci gaba da abin da take, Tafida yaja kujera aya daga tsallekin inda take tsaye ya zauna sannan ya amsa mata da. Ban jima da dawowa ba, sa o za'a kawomin shi yasa na dawo da wuri Ta gya a kanta tana saka raspberry in na arshe. Shi kuma yaci gaba da kallon duk motsin da take, ya kalli hannunta, a hannunta na dama a yatsarta ta tsakiya akwai zobe, wata ila azurfa ce, dan yana kama da azurfar. A tsintsiyar hannunta na hagu kuma akwai wasu jerin abun hannu na ananun beads masu she i, sai wal-wali suke a cikin hansken fitilun dake haskawa a kitchen din. Maryam ta bar jikin island in, ta nufi jikin cabinet in da take aje ananun plates, kasan cewar cabinet in a sama suke yasa sai ta yi tattage, kamar wani abun baki sai tsayinta ya kasa kaiwa, ko hannun cabinet in ta kasa tab'owa bare ta bu Matsa Ta tsinkayo muryarsa a bayanta, kuma cikin umarni, matsawar ta yi ta juyo tana kallonsa, daga inda yake ya aga hannunsa saitin cabinet in, ya motsa hannunsa daidai bu ewar ofar, Maryam ta juyo ta kalleshi ta jiya ta kalli cabinet in data bu e kanta. Me ki ke so ki auka ? Maryam ta ha iye wani abu, sannan ta lalubo muryarta tace. P...plate Saida yayi wani murmushi, sannan ya kuma motsa hannunsa, nan take plate in ya fito daga cikin cabinet in, kuma bai sau a a ko ina ba sai akan cabinet Duka a kan idon Maryam, wadda ta yi sumar tsaye, kamar mafarki take, kode tsafi yake ?, kuma ai yace mata he is monster saide kuma babu yanda za'ayi mutum ya zama dodo. Kamar me tsoron taka asa haka ta tako zuwa jikin island in, hannunta na rawa tunani da yawa na yawo a kanta ta kai hannu ta auki wu Duka abinda take Tafida na lura da ita, so yake yayi dariya, amma kumma sai ya dake, yanzu iyaka wannan kawai ta gani ahse idan ta ganshi a wancan halin suman gaske za ta yi. yar Maryam ta samu ta iya yanka cake in, ta ora akan aramin plate in da ke aje a gabanta, sannan ta ora karamin cokali a kan poate Ta tura plate in gaban Tafida dake zaune a tsallakenta ya kafeta da ido, ya tabbatar da a halin da take ciki yana cewa kett!, zata saka gudu, dan ga yanda bugin zuciyarta ya sauya, tana bugawa da sauri-sauri. Ya kai hannu yana jan plate in gabansa, ya auki aramin cokalin ya guntsiri cake in ya kai bakinsa, kamar kullum girkin Maryam 100% ne koma ya fi hakan, babu wata makusa. Yana ci yana kallon Maryam da ta masa nutsuwa. Ki zauna Maryam ta kasa ganewa umarni yake bata ko kuwa, tade kawar da komai dake kanta ta zauna, amma har yanzu ba a nutse take ba. Kin manta da abinda nace miki rannan ko? Yayi maganar a sigar tambaya, saide be jira amsawarta ba yace. Miriam Ya kira sunan daya ra a mata arfi da yaji, Maryam ta yi arfin halin agowa da idonta ta kalleshi, har yanzu idonsa sanye yake da glass, amma sai ya aje cokalin hannunsa ya kai hannu ya cire glass in, wayar idonsa da ta yi ja ta bayyana a idon Maryam, gaban Maryam ya shiga bugu fiye da azu, ta zazzaro idanuwanta gaba aya tana kallonsa, tunda Maanmu ta kawota duniya bata tab'a ganin abu makamancin wanda take gani yanzu ba, zata kawar da kanta gefe ya dakatar da ita. No dont, keep looking at me Babu yanda za ta yi bata iya musu ba, dan haka taci gaba da kallon nasa, saide zuwa yanzu ta fara hawaye, sai taga yayi murmushi. Ba tsafi nake ba Daaso, ba in ruhi ne a cikin gangar jikina, yana controlling in base on yanda yake so, kuma tun ina aramin yaro na gamu da wannan abun, babu wanda yasan abinda ya haddasar min da wanna abun, su me martaba sunce akwai aya daga cikin our forefathers da ya yi rubutu akan irin wanna abun nawa, kuma sunce wai ta yanda za'a dakatar da hakan shine ta hanyar aura min wata yarinya.... ni ban ma ri e signs in da sukace yarinyar tana da shi ba, shi yasa suka auramin ke, dan sunce wai kece yarinyar, Maryam a duk lokacin da ba in ruhi na zai tashi bana ji bana gani, bana banbance masoyi ko ma iyi, hatta da kaina ma bana ganewa, akwai abinda ban tab'a fa awa kowa ba, amma zan fada miki..... Sai kuma yayi shiru, ganin yanda Maryam ke ta zubar da hawaye, mi ewa ya yi da ga inda yake ya dawo inda ta ke, ya zauna a kujerar dake gefen tata, ya mi a mata hankin daya ciro daga aljihun wandonsa, Maryam ta karb'a tana share hawayen da suka k tsayawa, kuka take da gasken-gaske, amma mara sauti, tausayinsa ya cika mata zuciya, Tafida ya gyara zamansa yana juyowa ya kalleta da kyau. Abinda ke jikina aljanine, kuma yana bani super natural, sannan yana kareni daga cin asiri, a duk sanda za'amin asiri baya cina, saide ya koma kan wanda yamin, kuma turoshi a kayi, idan ina mafarki ina ganin wanda ya turoshi, bansan waye shi ba, kuma bansan me yake nema a wajena ba, amma tabbas nasan shine yake cutar dani, rayuwata bata da wani amfani, dan sam bana iyayiwa ubangijina tasbihi, bana iyayiwa manzona salati, hatta da kalmar larabci aya sometimes gagarata take, kuma kin san wani abun mamaki ? Ya fa i yana kallon Maryam, ita de har yanzu kuka take, amma mara sauti, sai share hawaye take, bata iya ce masa komai ba shima kuma sai yaci gaba.......... ________________ _Nace ba, wai a ina su Baba suka san Uchenna Frankline ?_ _Menene Abun mamakin da Ficar Yara yake SO ya rasa mana ?_ _A har kullum, ina me matu ar godiya a gare ku, ngd sosai da goyon bayanku, me aunar ku ce Salma Ahmad Isah_ _I LOVE YOU WUJIGA-WUJIGA -SAI KASKA CE YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Arewabooks @18saikaska Facebook fage: (Salma Ahmad Isah Sai Kaska) _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *Na sadaukar da wannan babin gare ki Bilkisu H Muhammad* *BABI NA ASHIRIN (20)* ......... A duk sanda zanyi sallah, dana na yi takbiratul ihram sai na ji kamar wani abu ya fita daga jikina, kamar akwai wani gingimemen dutsi a kaina da aka sau e min, kamar da a aure nake sai aka sakeni, kamar kuma ina ashin sarrafawar wani abune, bana tantance yanayin amma sai naji ni wasai, ina jin cewa nine, nine ni a karan kai na, inayin sallahta a nutse, amma daga zarar na yi sallama, wannan nauyin dake kaina da zai dawo, wannan aurin da a kamin zai dawo, zanji kamar ana sarrafani, kamar bani bane, bani bane akaran kai na, rayuwata akwai wahala WIFEY, shi yasa nake ganin lefin su Fulani da suka sakoki a cikin rayuwata, rayuwata bata da al ibla, rayuwa nake ba irin ta sauran mutane ba, na banbanta da sauran mutane, sam bana farin ciki, duk dariya ko murmushin da zan yi yakan tsaya akan lebena ne kawai, baya kaiwa har cikin zuciyata, ko ka an bana farin ciki, saide kuma inasan naga na saka wasu farin ciki, tunda ni bazan samu ba me zai hana na bawa wasu, amma kuma Maryam shigowarki rayuwata ya sauya wasu abubuwan, a da ba in ruhina baya kusanta ta sai raina ya b'aci, amma a wattanin nan da muke ciki sai abun yayi amari, ya dawo yana tashi kullum, saide tun dag a ranar da aka aura mana aure bai ara tashi ba, saide kl nayi wannan.... arashe yana nuna mata wayar idonsa. Kuma kece ka ai kike sakani naji cewa bani ka ai ba ne, ina da wani, duk da ina da an uwa amma kullum cikin ka aice nake jina, abubuwa sunmin yawa akai na, banajin da i jikina kullum, ko ka an wanna ba rayuwata ba ce Sai yaji wani nauyi dake zuciyar sa ya sau a, kamar wani dutse aka ora akan kirjin sa kuma aka sau e haka yake ji, yaji shi free domin ya amayar da abinda ke damunsa tsawon shekaru, bai tab'a zama ya bajewa wani ciwonsa haka ba, ko Neha da yafi kusancin da ita fiye da kowa bai tab'a magana da ita irin haka ba, bai tab'a ba, amma kuma kullum abun na ci masa zuciya, har yana barazanar hanashi numfashi, kuma duk abinda ya fa a mata haka in ne, baya jinsa daidai, baya farin ciki, yanajin kamar rayuwar tasa ba tasa bace, kamar ana sarrafashi ne, yanzu haka sai da yayi kokawa da wani abu sannan ya iya amayar da wannan maganganun. Ke kalleni nan Maryam na goge hawaye ta kalleshi, har idonta