Sashe 12
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baice mata komai ba sai tsaiwarsa da ya gyara yana binta da kallo, kuma ko bata fa a ba yasan me zaisa tazo ta masa magana. Idan bazaka damuba dan Allah lambarka nake so, ina sanka da soyyaya Ba itace ta farkon masa irin wannan abunba, mata da yawa sun masa irin haka, sbd yasani a karan kansa ba sai an fa a ba shi kyakyawa ne, amma kuma bayan wannan kyakyawar fuskar akwai wani duhu, duhun da babu wata a mace da zata iya juyashi zuwa haske, wannan fuskar tasa kawai suka sani, basu san ainahin shi in ba. Eshaan Auwal Tafida bai san cewa akwai mace aya da zata sauya tarin duhun dake cikin rayuwarsa ba, zuwa haske. Kafin ya samu damar bata amsa, kunnensa ya jiyo masa wata magana a bayan wasu motoci, da farko tsaki akayi kafin yaji ance. Aikin banza, wallahi wasu matan basu da kamun kai..... Ko ba'a fa a masa ba yasan cewa abinda yake faruwa tsakaninsu taji, shi yasa take fa in hakan, dan haka ya mosta kunnensa na dama, wanda yake kusa da inda maganar take fitowa, tayanda yana iya jiyo bugin zuciyar me maganar, ga kuma wani ara kamar ta cartoon, muryarce taci gaba da cewa. In banda rashin kamun kai ma me zaisa kazo kana wani cewa namiji kana san sa da soyyaya? Aka kuma jan wani tsakin, a hankali take maganar, dan idan ba me arfin ji irin nasa ba babu me iya jiyowa maganar, kuma bayan ta gama maganar sai ya meda hankali wurin sauraron bugun zuciyarta, a hankali take bugawa, sai yaji sautin yana masa da i, kamar wakar da yake yawan saurare. Yayi nisa wajen sauraren bugun zuciyar tata, har baya iya jin abinda budurwa dake gabansa ke fa i, gani tayi kamar yayi banza da ita, dan haka tayi tsaki ta bar wurin, tana ta mita a ranta na cewar gaskiyane abinda ake fa i akan Tafida kan bashi da kirki, shi kuma ganin ta bashi damar sha ar iska yasa ya shiga cikin motarsa yana ta sauraren wannan bugun zuciyar da baisan mamallakiyarsa ba. *HAKU AU GROUP OF INDUSTIRIES, ABUJA* *Da misalin karfe 10:00 am* Uallabai!, yallabai!, yallabai!! A firgice Alhaji Muhammad Haku au ya ago yana kallon PA insa, wanda ke ta wala masa ira, sai kuma ya kawar da kansa gefe, PA ya samu kujera ya zauna yana kallon ogan nasa. Abba me yake damunka ? Ya tambaya a matsayinsa na a a wajensa ba wai shugaba da na asan sa ba, Alhaji Muhammad Haku au yayi ajiyar zuciya yana jingina da kujerar da yake zauna a kai. Abba ka manta that we are friends, we do'nt use to hide komai wa junan mu Maganar taso ta saka Abban murmushi, sai kawai ya gyara zamansa yana kallon PA in nasa. Haris abinda ke damuna da yawa, ba duk kai zai iya auka ba Try me Abba yayi murmushi Matsalar ata ce Hanam Haris yayi murmushi shima, dama yasan zance gizo baya wuce na i, shi bai taba ganin ar me gidan nasa ba, amma a koda yaushe abban bashida abun fa i ko abun magana akai sai Hanam, hakan yasa shi san ganinta koda sau aya ne. Abba a matsayinka na mahaifin ta, addu'a ya kamata ace kana mata, duk da bansan abinda ya faru da ita ba, kuma ka kasance a kusa da ita domin warara mata gwuwa, ba kazo ka zauna kana tunani ba Haris Allah baya barin wani dan wani yaji da Ban gane ba Ina nufin akwai mutuwa, akwai jinya dole wata rana zan zo na rabu da ita, hakan yasa nake san nayi mata aure kowa ma ya huta, amma kuma sam ta i yarda da auren A'a abba bai kamata kace haka ba, kamar yanda na fa a maka kayi mata addu'a just pray for her arashe yana murmushi, shima Abban murmushin yayi, Allah ya sani cewa yana matu ar san Haris, da ace Hanam zata amince da ya saka ya aureta. Abinda bai sani ba shine, wasu addarorin suna faruwa kamar yanda muka so. To meke faruwa ? Sai kuma ya dawo serious, ya mi a masa file in daya shigo da shi. file ne daga office in manager Alhaji Muhammad Haku au ya kar6a, ya bu e file in yana gya a kai. Zaka iya tafiya Ok sir Ya fa i yana arin fita, a bakin ofa yaci karo da Kamal, babban a a wajen shugaban nasu, wani banzan kallo Kamal in ya watsa masa, dan Allah ya sani cewar ya tsani UCHENNA, dan a kullum mahaifinsu yana fifitashi akansa. Uchenna kam ko kallon Kamal in beyi ba, ya rab'ashi ya wuce. Ko ina ya wuce sai an kirashi, dan babu wanda bai san shi a kamfanin ba, dan Uchenna akwai raha, barkwanci da kuma haba-haba da mutane. Office insa ya shiga ya zauna, tareda ora aya akan aya, ya janyo wayarsa ya kira aninsa a waya, suka shiga waya, kuma bai kashe ba saida suka jima suna wayar. Sai wajejen arfe tara na dare ya tashi daga aiki, ya fito daga cikin ginin kamfanin nasu ya isa parking lot in kamfanin, ya bu e motarsa irar Honda Accord, ya shiga ya tayar sannan ya wuce gidansa dake Cosgrove Estate Wuse. Yana shiga cikin kyakywan gidan nasa wuta ya fara kunnawa, sannan ya ya haura sama ya shiga akinsa yayi wanka sannan yayi sallahr isha'i da bai samu yayi ba, ya sau asa ya Shiga kitchen domin ya samawa kansa abinda zaici. Duk da kyau da tsaftar gidan shi ka ai yake rayuwa a ciki, babu kowa nasa tare da shi, shi aya yake rayuwarsa. *Hadejia Emirates* Mai martaba Abdullahi Abubakar Masu ya tsaya tsirawa matarsa ido, wadda ta gama shaida masa da ta samo yarinyar da ake bu atar Tafida ya aureta, bawai be yarda da ita bane, saide yana san ya san taya akayi ta samo yarinyar. Suna zaune ne a babban falonsa wanda yake cikin turakarsa, kuma babu me ikon shigowa wajen idan bashi ba ko matansa, sai kuma amintattunsa da suke zuwa su gyara wurin. Fulani, taya kika samo yarinyar? Maganar tasa ta fito cikin asaita kuma a hankali. Bayan abinda ya faru jiya..... Na saka an kiramin an Masani, kuma ya ara fa amin alamomin yarinyar kamar yanda ya shaida mana a wancan lokacin, kuma na ira jakadiya babba mun ara tattauna maganar da ita...... Kuma bayan ta dawo daga gidan kamu ne tazo take shaida min da taga yarinyar kuma tayimin bincike akan yarinyar..... Sannan babu alama aya da yarinyar ta rage wadda ake nema Me mai martaba ya sau e wani gwauron numfashi Na ro eka ranka ya da e....dan Allah ka aura masa yarinyar nan, na gaji da ganin ana cikin wannan halin, ina so naga ana nima ya warke, na ganshi cikin farin ciki, naga ya tara iyali.... Sai kuma ta kasa arasawa, sbd kukan daya ci arfinta, me martaba ya rungumeta a jikinsa cikin sigar lallashi Amma kinyi bin cike sosai akan yafinyar ?, dan bana so muje mu kawo wadda bata dace ba cikin ahalin mu, garin gyaran gira a rasa ido Fulani taja hanci Eh na ara sawa an min bincike akanta, yarinyar tanada tarbiyya sosai, kuma daga gareta babu wani aibi, mahaifin ta ne ba mutumin kirki ba Me martaba ya gyara ri on da ya mata a cikin jikinsa sannan ya furta abinda ya zama sannadiyar sauyawar addarorin Tafida da wannan yarinyar da suke magana akai. Yarinyar ce zata zauna da anmu ba mahaifin ta ba, dan haka na auka miki al awarin a gobe goben nan za'a aura auren Tafida da wannan yarinya, kamar yanda za'a aura auren Amina da Adam, wannan al awari na miki A daidai wannan lokaci, a wani ban garen na masarautar Tafida ne yake tafiya cikin nitsuwa izza da asaita, wayoyinsa ne guda biyu ri e a hannunsa na dama, hannunsa na hagu kuma key in motarsa ne yana tafe yana an ka a key Bayace ga dalili ba, amma wannan bugun zuciyar daya saurare ya kawar da abubuwa da yawa a cikin kansa, ya mantar dashi sign in zuwan ba in ruhinsa, ya mantar dashi komai, sautin ne kawai ke bashi nisha i, kamar ka awar igiyar teku, yayinda yake tsaye a gab'ar tekun, iskar da tekun ke busowa me ciki da da i da ni'ima tana busawa akan fatarsa. Haka yake jin bugun zuciyar tata, kuma kamar wata wa a me da i daga bakin babban mawa insa, yaso ace ya dawwama yana sauraron bugun zuciyar nan, dan bayan daya shiga motarsa bai fito ba, kuma baiga yarinyar ba. Kawai de ya zauna yana jin bugun zuciyar tata ne, kuma jifa-jifa yake ji tanayiwa wani aramin yaro magana, alamun ba ita ka ai bace a wajen, kusan minti goma sha, sannan sai wata murya ta kira sunanta 'MARYAM' a lokacin ne kuma ta tashi ta bar wurin. Kuma bai dena sauraron bugun zuciyar tata ba har suka fita daga wajen. Sunanta da kuma muryarta dama bugun zuciyar tata baki aya sunyi gaba da zuciyarsa, har cikin ransa yake fatan sake ganinta...... -SAI KASKA CE- YADDA ADDARA TA SO -By Sai Kaska My wattpad page @Sai_Kaska *Proud of my first novel* TAUTARI WRITTER'S ASSOCIATION *BABI NA TARA (9)* .....Idansa ne ya kai kan Galadima wanda yake tafe Dogarai na take masa baya, kallo aya ya masa ya she ar, banda shi Galadima in da bai ko kalli Tafidan ba, dan wata iriyar tsanarsa yake kamar idan aka bashi wu a yau akace ya kasheshi zai iya, bayasan Tafida ko ka Babban abun haushin ma Tafid shine ya san sirrinsa da babu wanda ya sani kaf duniya, ciki kuwa harda Fulani Sadiya, haka suka zo suka wuce opposite, amma babu wanda yakula wani. Tafida na shiga turakar Fulani, a parlo na uku ya samu Nadra tana kallo, gaishe da shi tayi sannan ta bishi da orafin in tsayawa ya gaisa da awarta da beyi ba, daga nan tai mishi tayin abinci, kuma bai iba amma sai yace bari yaje yayi wanka. Bayan yaje yayi wankan ya sauya kaya zuwa farar T-shirt da ba in jogger pants, ya saka ba en slide sandales a