Sashe 71
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
murmushi tunowa da shi da ta yi, shine da kansa ya kawota gida, sannan yace mata zai je ya karb'o musu visa insu. Yana lafiya Kira na yi na sanar miki dama, kinsan Gebriel ya mutu.... Duk da akwai hasken rana a wajen, Amma sai da Hanam taga kamar wata walkiya ce ta haskota daga sama, bakinta a sake kuma yana rawa ta furta. A garin ya ya ? Guba suka sha shi da matarsa, wai dan sbd sun haihuwa, yanzu fa shine labarin dake tayawo a new york baki Hanam ta dam arfen balcony, dan arin fa uwa da take, ba wai tausayinsa take ba, ba kuma haushi ta ji dan ya mutu ba, kawai de zafin rasa rai ne ya dake ta, haka kuma koda ta ru i kanta cewa shi ba baban Arya bane ta sani cewa shi in ne baban nasa, amma, ba musulmi banr, bata san wata kalar addu'a zata masa ba. Sai kawai ta kashe wayar, dan wata ila hakan ne mafita. *RNo.202,Taj Skyline Hotel, Ahmedabad, India* *09:30am* ESHAAN POV. Zaune yake a kan wata sofa, hannunsa ri e da littafin Aakhoki Gustakhi, wanda Saree ya rubuta, littafin yake karantawa, yayin da yake jiran fitowar Maryam da ga ban aki, so yake ta yi sauro ta fito su tafi, dan yau za'ayi final, kuma wasa ne tsakanin India da Australia. Sannan yana sa ran a gobe zasu wuce Delhi, dan jibi ne aurin auren Mahesh abokinsu. Tunaninsa ya katse tare da karatun da yake, a sanda Maryam ta fito daga ban akin sanye cikin chickankari, rigar orange color ce, kuma ta sau o mata har kan guwa, yayinda wandon ya kasance fari, kuma wandon yana da fa i, ta yafa farin mayafin kayan a kanta, ta rataya shi zuwa bayan kafa arta. afarta sanye cikin fararen boots, kamar kullum fuskarta babu kwalliya, amma shi a hakan da take tafi masa kyau, dan yafi san ya ganta a yanda take, haka in nan nata, dan hausawa sunce wai dai-dai in wani, karkattaccen wani. Litafin ya rufe tare da aje shi a kan coffe table, ya mi e yana shafa sumarsa. Kin shirya? A hankali ta gya a masa kai. *Narendra Modi stadium, Ahmedabad, India* *12:00pm* Hayaniyar masoya da kuma magoya bayace ke tashi, sai kuma masu bayyana yanda wasan ke kasancewa, gaba aya stadium din cike take ma il da mutane, daga tsakiyar fili kuma an wasan india da na australia ne ke fafatawa, dan yanzu haka ana zagayen arashe ne. Daga cikin kujerun an kallo, akwai ta Eshaan da Maryam, wan an da suka zuba ido suna so suga yanda wasan zai kaya, a farkon fara zuwansu wajen babu abunda Maryam take ganewa a wasan. Amma a hankali a hankali ta fahimci kan wasan, kuma kamar Eshaan itama tana fatan ace india ce ta lashe wasan, dan yanda ta ga indiyawa nasan wasan cricket idan suka fad'i wata ila Ahmadabad ta kama da wuta. Wajen ya yi wani irin shiruu, kamar mutuwa ta ratsa, kamar da ba wajen ne ake ta hayaniya ba, sun yi shirun ne saka makon Rohit Sharma babban an wasa india, da ya ri e bat a hannunsa ya au matsayarsa yana jiran Jones an wasan austrelia ya cillo wallo. Jones ya an ja da baya ka an, kafin ya tako a guje, kuma yana zuwa tsakiyar filin ya cilla wallon, wani irin duka da Roshi Sharma yayiwa wallon saida ta fita daga ginin stadium Kamar magoya bayan india jura suke, sai suka saka ihu, ana tafi ana fito, india taci wasa, bakin Eshaan kamar ya rabe biyu dan tsabar murna, Maryam ma ta taya su murna sosai. Da a wajen su abun farin ciki ne sosai, dan indiawa na martaba wasan cricket. *Cairo Internacional airport* *05:40pm* HARNAM(Harees and Hanma) POV. A tare suka fito daga cikin terminal, yayin da Haris ke ri e da jakukunansu, gaba aya hanam ta agu taje taga Arya, so take taga yanda ya sauya, dan tana da tabbacin ya sauya sosai. Haris ne ya tsare muasu taxi, sannan suka shiga, kai tsaye Acasa Mia suka nufa. Ta ta haddace address in gidan, dan haka taxi na sauke su ita ta fara shiga gidan. Aryaan?! Shine abinda ta fara fa i, a sanda idanuwanta suka gane mata shi suna wasa shi da Al-amin,Salwa da Khalil a garden in gaban gidan. Da gudu ta yi inda suke ta sure shi tana rungume shi, kafin ta dago shi daga jikinta tana kissing face insa, ta yi kewarsa sosai, fiye da yanda baki zai iya furtawa. Jikinsa tabi da kallo tana ganin yanda ya sauya, bakinsa taf cike da ha wara, girma ya ara bayyana a tare da shi. Arya Ammi ta yi kewarka Ammi ? Cikin gwarancinsa ya furta hakan, Hanam ta yi dariya tana sake rungume shi. Eh Ammi, Amminka ta yi kewarka Papi ma ya yi kewarka Ta juya ta kalli Uchenna dake bayansu, hannu ya kai ya karb'i Arya daga hannunta yana rungume shi shima, sai a sannan ta dawo kan anenta data ga a wajen, aya bayan aya tabi ta rungume su suna gaisawa da ita. *09:30pm* Bani ayan Muryar Masarrat ta fa i, a sanda suke tsaye a kitchen ita da Hanam. Hanam ta auko plate cike da cabbege ta mi a mata. Saida Masarrata ta juye cabbege in, sannan ta rufe pot in, ta jiyo ta kalli Hanma. Ana biddi ahki ma'ak bi maudu'u daruri (Ina so nayi magana da ke akan wani abu me muhimanci). Hanam bata ce komai ba sai ci gaha da kallonta da ta yi alamu ina ji. Waye mahifin Arya ?, dan inada tabbacin cewa Harees ba shine mahaifinsa ba Bisa ga manakinta sai taga Hanam in na murmushi. Dama sai da ta ayyana hakan a ranta, tasan cewa dole zata tambaya. Sai kawai ta ago da hannayenta ta sunkiyar da kanta tana kallonsu, yayin da ta ha esu waje guda tana wasa da su. A sanda naje New york wani aiki, na ha u da wani, kuma shine yayimin fya e, har na samu cikin Arya Kalaman basu da yawa, amma kuma sun yiwa Masarrat nauyi a ka, gani take kamar ko wani unci da ya faru a rayuwar Hanam itace sila, kamar duk wata damuwa da Hanam in ta shiga duk ita ta ja. Nan da nan ta fara hawaye, Hanam ta arasa kusa da ita sannan ta rungumeta tana shafa bayanta. A'a Ammi, ba kuka za ki yi ba, komai ya wuce yanzu, dan Allah ki dena saka damuwa a ranki Kafin ta saketa, Masarrat ta kai hannu ta share hawayenta, sannan ta dafa kafa ar ta. Allah ya miki albarka, muje muci abinci, zuwa gobe zaki zaga dangi Hanam na murmushi ta auki wani bowl ta fita, a falo ta same su duka suna hira. Yauwwa abinci yakammala, wallahi yunwa muke ji, ya yi kyau yarinyata, Allah ya miki Albarka Dr. Taiyyab Abu Al-aminya fa i, Hanam ta yi dariya, dan mutumin yana da kirki, kamar Abbanta, Abbanta ?, a ranta ta yi masa addu'a kamar yanda ta saba a duk sanda zai shigo cikin tunaninta. A hankali ta juya ta kallesu su duka, Abuya kamar yanda ta ji su Al-amin na fa a masa, Harees, Arya, Al-amin, Salwa da Khalil dukan ninsu suna cikin farin ciki. A da ita ka ai take rayuwa, daga ita sai Abba, bayan Abba sai Arya ya zo, daga shi kuma sai ga Harees, wanda zuwansa ya zama sanadiyyar shiryawarta da mahaifiyarta, bayan kuma ta shirya da mahaifiyar tata sai ta samu anne harda mahaifi. A cikin ranta ta godewa Allah, a sanda ta tuna abinda Abba yake fa a mata a kullum. Bayan wuya sai da i Bannute a baka ne, bayan wuya sai da i, dan a yanzu tajita a matsayin cikakkiyar ar adam, ta samu komai, babu abinda take nema, kewar Abba ka ai ta dameta. *No.803, Tolstoy Rd, New Delhi, India* *05:00pm* MARYAM POV. Zaune take daga kan wata sofa, ta yi tagumi tana bin an matan wajen da kallo aya bayan aya, yaren hindi suke wanda ita sam bata fahimta, ko magana za ta yi da su saide ta musu da turanci, su kuma su amsa mata da turancin nan nasu dake bata dariya. Tun safe take tare da an matan, wa anda suka kasance awayen amarya Komal, kamar yanda Eshaan ya fa a mata sunanta. Dan jiya suka sau a a delhi, kuma ya fa a mata cewa yau za'a aura auren abokin nasa, shi yasa suka taho tun safe, ya dan ata a hannun amaryar shi kuma tun bayan nan bata ara ganinsa ba. Sai biryanin da ya aiko mata dan yasan ita ba komai take iya ci ba, sai laddu in da sukai ta bata. Hayaniyar awayen amaryar ta cika mata kunne, dan yanzu haka amarya suke shiryawa. Sai kawai ta auki wayarta ta bu e ta shiga message, kusan jarin mesages uku tana turawa Eshaan amma ba ya replying. Dan haka kawai sai ta fito daga wajen ta aika masa kira, amma de kamar azu bai aga ba. Mts, ina ya shiga ne? Babu me amsa mata dan haka kawai sai ta meda wayar cikin jakarta ta ci gaba da kallon an matan, kyawawa wanda babu aya da zaka iya cillarwa a cikinsu, domin babu baya a cikin. Wow...., a ina kika si yi wannan saree Maryam ta juyo ta kalli budurwar, sannan kuma ta kalli jikinta, nan take tunanin ta ya dawo mata da abinda ya faru a azu. Tana zaune a bakin gado tana cin abinci, Eshaan ya shigo akin hotel in da suka sau a, hannunsa ri e da wani kwali, yacemata saree ne a ciki, kuma nata ne, so yake ta saka. Ta fa a masa cewar ita fa bata iya aura saree ba, shi kuma yace taje ta saka blouse da skirt in tazo sai ya aura mata.Yanda aka aura saree in nema bata san tunawa, dan yau d'an guntun hankalin da take ji Tafida ya bar mata shi seda ya zube, notukan kanta suka karasa kuncewa. Kin gane saree in Krishan?, shine fa wannan wanda na taya a Metropolitan Mall, amma na fasa sbd tsadar da ya min Maryam ta kuma