Sashe 74
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigo gari ai Maryam ta kalli inda suke, bakinta ya bu e cikin dariya, ta yi missing gida, ta yi bala'in kewar komai na ha ejia. Farin cikinta be ara ninkuwa ba sai sanda taga sun wuce ofar fada sun nufi Garko. A ofar lungunsu ya yi parkinga. Se da Maryam ta riga shi fita daga motar, bakinta fal murna, ta tsaya a wajen tana ta bin unguwar tasu da kallo. A sannan Tafida ya zagayo inda take tsaye bayan ya fito mata da jakarta dake booth. Matasan dake zaune a kan bencina suna ganinsa suka ta so suka rufe shi suna ta mi o gaisuwa. Tafida be iya shariya ga matasa ba, seda ya tsaya suka gaisa har ya musu ihsani, sannan suka barshi ya tafi, Maryam kam har ta yi gaba, saida ya ha a da sauri sannan ya cin mata. ofar gida taga auta da abokasa suna wasa, tamanta da wani Tafida dake binta a baya ta ruga da gudu inda suke tana fa Auta! Shima jin Muryar yayar tasa yasa ya mi e da sauri, yana ganinta ya ruga inda take shima yana dariya, suna ha ewa suka rungume juna, Maryam ta aga shi masa tana juyi da shi, tuni batun zuwan Maryam ya kara e unguwa. ota da an mata duka aka lo o ana ganin Maryam da Tafida. Sai da Maryam da auta suka gama yarintar tasu sannan ta ja hannunsa suka shiga cikin gidan. Maanmu wata sabuwar Ps5 ce ta fito... Hussain be ko arashe ba, Maanmu da wata mata dake zaune a kan tabarma suka saka dariya, harda Hassan da ya fito daga ban aki. Ya kalli kwanon dambun da ke gabansa sannan ya kallesu. Ni fa ba santi nake ba, labarine kawai nake san baku Matar da ke zaune kusa da Maanmu tace. Babu wanda yace kana santi ai, kawai de labarin naka ne abun dariya Sai kawai shima ya yi dariya yana kai loma. Wato anti Hanne ai a gidan nan babu girkin da za kuyi ya saka ni santi, Yaya ce kawai take yin girkin da ke sakani santi Kamar daga sama suka ji sallamar Maryan da Muhsin. Gaba ayansu suka sakawa bakin ofar ido, ko amsa sallamar an rasa wanda ze yi. Ita ince kuwa ta shigo, sede wannan Maryam in tana da banbanci da waccan, wannan Maryam in tana da jiki, kuma tafi waccan fari, amma maganar da ta yi yasa suka fahimci cewa ita in ce. Wai baku ji muna sallama ba ne ? arashe tana zama kusa da Maanmu tare da rungumeta, Anti Hanne ta mi e tsaye tana fa Ko wannan itace Yayan? Ihun da su Hussain suka saka shi ya tabbatar mata da maganarta. Gaba d'aya suka zauna a gaban Maanmu suna ta yi Maryam sannu da zuwa. Kuma ina Yaya ? Maryam ta kalli Hussain, tana so ta tuno waye Yaya, nan take walwarta ta hasko mata Tafida dake tsaye a bakin ofa ri e da jakarta. Ita aukin ganin an uwanta ma ya mantar da ita shi. Ta dafe goshinta. Oh!, yana waje, kaje ka shigo da shi Auta bani hijabina gashi can Muhsin ya mi e sannan ya auko mata hijabin, Maanmu ta karb'a ta saka, sai bin Maryam take da kallo yanda ta ga tasauyamata, duk da dama Anti fati tana fad'a mata yanda Maryam d'in tace suna zaman lafiya da mijinta, amma ganin 'yarta ta ya k'ara tabbatat mata da waccan magana. Sirikin mu ne zai shigo ? Maryam ta juya ta kalli matar da kallo aya zaka mata ka fahimci cewa bafulatana ce. Eh Hanne, mijin Maryam ne Ah to nima bari na je na saka hijabi Cike da kokwanto Maryam ta bita da kallo har ta shige akinta na da. Ta juyo ta kalli Maanmu. Maanmu waye ce wanna ? Husain ka auko wannan dardumar ta akina ka shimfi awa Tafida Maanmu ta fa i memakon ta amsa mata, ita fa kanta ya kulle, ta kasa ganewa. Sallamarsa ta ji daga waje shida Hassan, Hassan in ne ya fara shigowa sannan shi, kansa a asa har ya zauna a kan dardumar da Hussain ya shimfi a masa, suna gaisawa da Maanmu Hassan yace da Maryam. Yaya a ina zan aje miki jakar ? Ta kalli jakar da ke hannunsa se taga jaka aya, bayan ita tasan da jaka biyu ta taho. Ka kaimin akin na Ai yanzu baki da aki a gidan nan, sai dai na Maanmu Maganar Hussain ta ara kulle mata kai, amma ba komai zata tambayesu tunda Maanmu ta i amsa mata, sai kawai tace. Kai min akin Maanmun to A lokacin Hanne ta fito daga akin Maryam na da, ta ja kujera ta zauna itama suna gaisawa da Tafida. Duk yanda ya kai da gujewa kada Maanmu ta masa godiya sai da ta masa, shi kuma sbd baya san yawan godiyar yasa koda su Hussain suka turo masa lambarsu be bawa Maryam d'in ba, dan bayama so ta san da abinda yama 'yan uwanta. Har ruwa aka kawo masa amma yace tafiya ze yi, sai da ya tashi ya fita sannan Maanmu ta kalli Maryam. Kije ki taka masa mana Ita gaba aya rudanin dake kanta ya hanata cewa komai, a kunyace ta mi e ta fita. Can ta hangoshi har ya kusa fita daga lungun, ta bi bayansa, sanda ta isa wurin har ya shiga mota. Ita ma seat in gaba ta bu e ta shiga. Akwai jakata Ya juyo ya kalleta. Na sani ai, amma ai wannan kayan sakawar ki ne Eh kayan sakawar, dama su nake fa Keda ba'a nan zaki kwana ba, anjima zan zo na auke ki Bata san sada ta furta Huh? Eh mana, baki da wurin kwana a gidan Maanmu, baki san an bawa wata akin ki a gidan ba? Zuwa yanzu kam abun ya gama kulle mata kai, kenan har Tafida ma ya san da zaman waccan matar amma ita bata sani ba ?, to me yake faruwa haka?. Kije ku gana da an uwanki, nima zanje na ga nawa Ita de ba haka ta so ba, tana san ta kwana a gida yau, a cikin 'yan uwanta. Dan ta yi kewar kowa a cikin su. Ta juya jiki a sanyaye zata fita, caraf ta ji ya ri e hannunta, ta juyo ta kalleshi, a kan lips insa ya furta. I love you Bata ce Komai ba, dan kanta cike yake da ru ani. Ya saki hannunta ta bu e motar ta fita, sai yanzu take kallon yanda jama'a suke binta kallo, gaba aya ma ota an le o ana san a ga waf. Ko da ta shiga cikin gidansu se ta ga su Hussain na irga ku Ta zauna a inda ta tashi azu tana fa Wannan ribar shagon wayar ce? A'a mijinki ne ya bayar yace a bawa Maanmu da Anti Hanne anyi murmushi, ita de kam ta agu ta san wacece wannan Anti Hannen, gashi kuma tana zaune a wajen, babu damar ta tambayi su Hussain. Hassan auko min jakar nan Hassan ya mi e ya shiga akin Maanmu ya fito mata da jakar, se yanzu Maryam take arewa gidan kallo, har sabon fenti suka sake, an gyara gidan sosai. Bayan Hassan ya kawo mata jakar ta bu e ta shiga raba musu kayan tsarabar da ta kawo musu, kowa se murna yake har da Abti Hannen da bata tsara kawo gujirin da ita ba itama ta samu, harda ma otansu. TAFIDA POV. Kai tsaye fada ya wuce, sai da ya yi parking motarsa a babban parking lot in katafariyar fadar, sannan ya bu e motarsa ya fito. Kamar yanda aka saba, dogarai da hadima dama bayi sai kirari ake masa da mi o gaisuwa. Tafida an Tafida, ruwan kogi tafi sannu sannu wanda ya yi wargi zai halaka, giwa ta gama da masu arfi ta wuce...... Haka wani dogari me kaifin murya ya ci gaba da ranga owa Tafida kirari har ya shige soron farko. Ya ci gaba da taka sorayen fadar har ya isa inda yake san isa, wato b'angaren Fulani Khadija.Sai da aka masa iso da ita sannan ya samu ya ganta. Yana zaune a falo na uku ta fito cikin wannan tafiyar tata ta asaita. Tun da ta fito take binsa da kallo, ya sauya mata sauyi ba an ka an ba. Ita a yanda me martaba me bata labarin ya sauya ma sai ta ga ya fi, ya yi iba ya ara haske, kai da ganinsa kasan cewa hankalinsa ya kwanta. Zama ta yi a kan kujera tana amsa gaisuwar da yake mata. Ina Nadra? Sai da wasu sakkani suka wuce kafin ta amsa da. Taje wani bikin awayenta Ya gya a kansa. Ina Maryam ? Na kaita gidansu, inshaallah zata zo ku gaisa Itama kan nata ta gya Bari na saka a kawo maka abinci Muryarta ta fa i cikin shirun da falon ya auka. A'a ranki ya da e, sauri nake, dan a can gidana zamu sau a, zan shiga na duba jikin Galadima sannan na wuce, kuma dama mun yi magana da me martaba kan sai gobe zamu gaisa Babu matsala, Allah kai mu goben, zaka iya tafiya Ya mi e yana mata sallama sannan ya fice. Fulani Khadija ta aga kanta tana godewa Allah, zuciyarta cike take fal da farin ciki da kuma murna, murnar ta sau e nauyin marayan Allahn da aka ora mata, murnar ganin tilon an da zata iya kira da nata na cikin farin ciki bayan wani abu da ta yi a rayuwarsa. Tafida ya yi sallama a falon Fulani Sadiya, jakadiyar da ta masa iso ce a kan gaba, yayinda shi kuma ke biye da ita. A gaba aya zamansa a fadar wannan shine karonsa na biyu da ya shiga b'angarenta, na farkoma da Fulani Khadija suka fara zuwa sanda ta haifi Amina, bayan nan bai sake shiga ba. Bin mutanen dake falon ya yi da kallo kafin ya samu waje ya zauna. Fulani Sadiya, Maimun, Amina da Nabil. aua bayan ayan suka gaida shi, kafin shi ya gaida Fulani. Ya Galadima da jiki ? Ya tambaya yayinda suke gaisawa, Fulani Sadiya ta jinjina kai. Jiki da dama, sai godiyar Allah To Allah bashi lafiya, ni zan