← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 84

Sashe 58

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na cutar dake Miriam bazan tab'a barin hakan ba Me ka mata ?..... Jiya kinsha maganinki ? A memakon ya amsa mata tambayarta ta sai ya mata wata tambayar, yana motsa babban an yatsansa a kan kuncinta, ta gya a masa kai, wata ila ya manta ne, amma shi da kansa ya bata maganin, ko kuma de kawai yana san a bar zancen ne. Ka je ka yi wanka, na gama abin kari Sai ya gya a mata kai, sannan ya sumbaci goshinta, ya barta tsaye a wajen ya shiga akinsa, Maryam ta yi murmushi idonta a lumshe. *Da misalin 04:00* Maryam ce tsaye a cikin ironing room in gidan, kayan da ta wanke jiya take gogewa, earpiece ne sa ale a kunnenta tana waya da Anti Fati. Kafin daga bisani su ka yi sallama, ta meda himma wajen yin gugarta ta. Sanda ta gama ta ebe kayan ta yi sama da su, akin Tafida ta fara shiga, ta bu e wardrobe insa, ta samu wurin da babu kaya ta saka masa a wajen. Sannan ta ebi nata ta shiga akinta ta saka nata ma a cikin wardrobe kafin ta fito waje, ta shiga balcony in corridor, ta yi zamanta a kan lilon nan, tana yiwa akun nan magana. Kafin ta bu e wayarta ta shiga Tiktok, tun jiya take ta dubawa, dan tana jiran shigowar sa on Badar, Aikuwa tana shiga wurin message ta ga sa on nata, hannunta har rawa yake ta shiga ta bu e, lambar Badar in ce. Ta kwafe lambar, sannan ta si yi credit daga account inta na banki, dan bata da kati sosai, kafin ta aika mata kira. Allah sarki auna, wallahi na yi kewarki Shine abinda ta fafi bayan ta amsa sallamar Badar in. Tana iya jiyo dariyar Badar in kafin ta ji tace. Madam Tafida, nima ina kewarki Anti Fatice ke fa a min wai an miki satar waya Wallahi, kede rabu da mutane 'yan neman jafa'i, Samsung ina saida aka raba ni da ita Maryam ta yi dariya, dan tsaf ta tuna yanda Badar in ke matu ar san Samsung in tata. To yanzu wacce kika koma ? Iphone! Ke dan Allah?! Wallahi nake fa a miki, Aliyu ne ya dalleni da ita To ya su Mama ? Wallahi su Mama lafiyarsu alau Ke yanzu wacce gareki ?, kinsan ku matan manya, ai naga hannunki ma yanda ya yi fari, nasan fuskar kima ta yi farin Maryam ta yi dariya. A'a ni babu wani fari da na yi, Samsung na koma wallahi Tana iya jiyo shewar Badar in, kuma itama ta fa i ne kawai, ba dan bata san cewa ba ta yi farin ba, itama da kanta ta san cewa ta yi farin, ta kuma sauya. A hayye!, kinga fa matan manyan da nake magana!, ke wai tsayama, injide an auko mana aramin Tafida Maryam ta yi tsaki. Badar bana san iskanci Allah! Badar ta saki dariya. Ai dama na sani, kin koma makaranta ne? Maryam ta gya a kai kamar Badar in na ganinta. Na koma wallahi, kinsan a estate muke, to ta estate in ya sakani, ke fa?! Badar ta kuma yin dariya, tana tuna sanda take yawan damun Maryam in da zancen Tafida, tana ce mata bata so, yanzu de sai gata a matsayin matarsa. Ikon Allah kenan. Na koma, amma ni university ma na fara...... Haka suka yi ta hira, kafin Maryam ta katse hirar domin ganin kamar magariba na shirin yi, gashi bata dafa komai ba. Kitchen ta koma sannan ta shiga kiciniyar shirya abincin dare. TAFIDA POV. Khab ? (Yaushe ?) Muryarsa ta tambaya, yayin da kunnensa na dama ke kare da wayarsa, tsaye yake a ofar balcony in shiga falo, yayin da yake waya da Arjit abokinsa. Teen saptah!! (sati uku!!) Muaryar Arijit in ta bashi amsa da ga cikin wayar, abubuwa da yawa sun zo masa lokaci aya, Bikin holi, Gasar world cup da za'ayi na cricket, sannan bikin abokinsu Mahesh, sannan duka wuraren a india suka, amma a mabanbanta wurare, Bikin holi da ya yiwa Daadi al awari mumbai ne, gasar world cup Ahmadabad (Amdavad), yayinda bikin Mahesh in zai kasance a garin Delhi. insa aya su Maryam sun fara exam, dan bazai iya tafiya babu ita ba, kuma gashin kansa ya dameshi, yana so ya rabu da shi. Kansa ya aga sama sannan ya furzar da iskar dake bakinsa. Kana ji ko Arjit, kawai kuyi magana da su Ranvir (sauran abokansu), ku shirya abinda ya dace, sai na fara zuwa mumbai, sannan zanje Ahmadabad, bayan nan sai na araso delhin, kuma zan yi magana da Mahesh Cikin harshen hindi ya yi maganar, yayin da a ayan b'angaren Arjit yace. Theek hai, tum hara biwi kaha par hai ? (ok!, ina matar ka?) Tafida ya yi murmushi. Tana lafiya, tare zamu taho da ita ai, zaka ganta! Mema kace sunan ta ? Maryam Haan Maryam warai Maryam) Kana ji ko, sai mun yi waya, zuwa anjima ko gobe zan kira Mahesh in, kuma zan kira Amit ma Ok bye Bye! Ya sau e wayar tare da aukowa aramar keypad in da ya siya jiya, ya tura sa o sannan ya meda ta cikin aljihun nasa, ya sa hannu ya tura ofar sannan ya shiga da sallama. Babu kowa a falon, kuma dama yasan ba lalle ya sameta a falon ba, dan kullum i yanzu tana kitchen, sai kawai ya haye sama, yaje ya yi wanka ya sauya kaya. Sannan ya dawo asa, kansa tsaye ya wuce kitchen, jingina ya yi da jikin ofar bayan da ya bu e, da alama bama tasan ya shigo ba, arar hand mixern data kunna shine ya cika kitchen Sanye take da wata doguwar riga ta atamfa, me sau inki, bisa ga dukkan alamu baza ta yi nauyi ba, yau bata saka hijabi ba, amma akwai ankwali a kanta, shi ma kuma ba wani auri me wahala ta masa ba, ka wai ta an turoshi gaba ne, kamar ture kaga tsiya, yaginda jelar gashin kanta ke reto a bayanta. Koda Maryam taga kamar lokaci zai ure, sai kawai ta dafa farar doya, ta mata egg sauce, dan kamar ta na ga itace zata fi mata saurin dafawa, ko da ta gama sai ta ga tana da sauran lokaci, dan haka kawai sai ta juye komai a cikin warmer. Ta shiga ha a cake parfait, tana cikin mixing whipping cream da condensed milk da handa mixer ta ji hannayensa sun kewaye waist inta, kafin amshinsa ya shiga hancinta, kansa ya sau a a kan kafa arta ta dama. Hand mixer ince ta fa a cikin bowl in, sbd sakinta da ta yi a bazata, ta ji kamar iska bata isa huhunta da kyau, komai dake aiki a cikin kanta ya tsaya cak, sakamakon wuyanta da ya sumbata. ip!, wuta ta auke a kan Maryam, ya Allahu ya rahamanu!, ina wannan bawa na ka yake san kai ta?, ta ayyana hakan a zuciyarta. Barka da aiki, Daaso yar Maryam ta ha iye yawu, sannan ta lalubo muryarta a ma oshinta ta amsa masa da. Humm....humm..hummm! Tana jin sautin murmushin sa a kan wuyanta, a hankali ya juyo da ita ta fuskance shi, sannan ya saka hannunsa ya cire dankwalin kanta, ya janye ribbon in ma, gashin ya baje a bayanta, sannan wannan hair pin in ma ya sau o, cirowa hair pin in ya yi, ya sa ala mata shi a gefen gashin. Ya kike ? Sai yanzu ta iya agowa da kanta ta kalleshi, gashin kansa a ji e yake, ya saumo masa kan goshi, amma duk da haka tana ganin idonsa da suka fara sauya kala, dan a hankali wayar take riki ewa zuwa ja. B...Baka d..da lafiya ne Girarsa ta tattare waje guda alamun kokwanto. Me ki ka ga ? Idonka na sauya kala Sai ta ga ya yi murmushi. Mantawa ki ke da mijinki monster ne ?, that's common Wifey Maryam ta ha iye yawu, sannan ta sunkuyar da kanta asa, shaf ta mance da waye shi, wa anan abubuwan da yake mata sune suke mantar da ita komai, ciki kuwa har da nisantar juna da ya ce su yi. Hannunta ya ja ya zaunar da ita a kan kujerar island, shima ya zauna a ta gefenta. Juyawa ya yi ya kalli inda ta aje mixer da kayan da take ha a cake parfait, ya motsa hannunsa a setin kayan, mixer in ta tashi daga cikin bowl in, ya ajeta a cikin sink, sannan ya ebo kayan ya aje su a kan island. Maryam tana kallon abinda yake, shi da kansa ya ha a parfait in, kuma ba tare da ya tab'a koda abu aya da hannunsa ba. A sanda ya kammala ha awa a lokacin aka kira Sallar magariba, shi da kansa ya mi e ya bu e dishwasher ya fito da kayan dake ciki, sannan ya saka wanda suka b'aci, ya kunna ta. an ya fitar aya bayan aya yabi cabinet ya jere su. Har yanzu da wannan power natural in yake amfani, juyowa ya yi inda Maryam ke zaune, ya rike fuskarta da hannayensa. Ba ki da lafiya, kina bu atar hutu, hmmm ? Sai kawai ta gya a masa kai, dan bakinta ba zai iya cewa komai ba, goshinta ya sumabata, sannan ya saki fuskar tata yana ja da baya da baya har ya fice. Maryam ta sau e wani nauyayyen numfashi, ta kai hannu ta janyo ankwalinta ta aura, sannan ta mi e ta fice daga kitchen in._____________ SAI KASKA CE YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Tiktok @SAI_KASKA Arewabooks @18saikaska Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *Wanga babin naki ne Umee* *BABI NA TALATIN DA TAKWAIS (38)* MARYAM POV. ________Sallah taje ta yi sannan ta zauna a akinta tana tunani, tunanin da ita kanta bata san na miye ba, bisa ga dukkan alamu Tafida ya gama zautata. Meriuty!, Mariuty!! Iko sai Allah!, idan da wani me ikon ma to shi ya yi shi, yau kuma Meriuty ta koma ?, ta tab'e baki sannan ta mi e, dama bata cire hijjabin ta ba, dan haka ta nufi ofa. ofar akinsa
Chapter 58 · 0% Book details