Sashe 22
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
biyu, kallonsu kawai yayi suka watse, duk da ita i Iqran bata tsoransa, dan jinin sojane ke yawo a jikinta, mahaifiyarta soja ce, Hanam ta bishi da kallo har yazo ya zauna kusa da ita. Juyowa tayi ta kalleshi, ita bata tab'a masa kallon kullira ba ma sai yau, Ba ine amma kyakyawa, dan Uche bashi da muni sam, ga tsafta kamar ba Cristian ba, komai tsaf-tsaf, itama in saide ta fa a masa farin fata, amma ba kyau ba. What ? Au haka ma zaki ce ?, to shikenan let's go straight to the point, ina sanki Hanam, shine abinda nazo na fa a miki, kuma ina fatan zaki karb'eni Wani irin kallo na baka da hankali ta masa sannan ta mi e tsaye. So you think we are joking ? Shima sai ya mi e tsaye, ta aga kanta ta kalli fuskarsa dan Uche akwai tsayi ba laifi. What do you mean Haman ? I mean nida kai bazamu tab'a zama aya ba, hanyoyunmu mabanbanta ne, ba addininmu aya ba, muna da banbanci Uche, tun ba yau ba nasan cewa sona kake, amma kayi ha uri soyyaya tsakaninmu abune mara yiwuwa, dan bazamu tab'a zama aya ba Tana kaiwa nan ta tafi ta barshi a wajen. *** Har yanzu bai manta ranar ba, dan daga ranar bai sake ganinta ba sai yau, to yama za'ayi ya manata ranar, nan take wani abu da ya da e da mantawa da shi ya dawo masa, wani hoto da yaso yayi deleting insa daga kwakwalwarsa ya dawo, yan da mahaiyarsa ke kuka a ranar Na tsaneka Uche, Allah ya tsine maka Sai kuma tsinuwar ta shiga dawo masa tunaninsa, yanda yake tsine masa a mabanbanta lokuta. Kai tsinanne ne Allah sai ya tsine maka Ba zaka tab'a ganin daidai ba a rayuwarka tsinuwata ce za tayi ta bin ka Hello!! Firgigit ya dawo daga tunanin, kamar wanda lantarki ta kama. Are you okay ? Muryarta ce ta tambaya, shekaru kusan bakwai kenan, amma kammaninta na nan yanda suke, bata sauya komai ba sai girman da ta ara, to amma me yasa bai gane cewa Abba shine mahaifin ta ba ?, ko ta sunansa ya kamata ace ya gano hakan ?, shi yanzu ta tuna da shima ma ?, ba lalle ace ta tuna dashi ba, wata ilama tayi aure abinta. Shi kuma tun bayan ita bai kara san ko wace yarinya ba, duk da an mata da yawa sun sha kawo kansu gareshi amma baya kulawa, Hanam kawai ya so, kuma baya jin zai sake san wata bayan ta. Yeah i am okay Muryar tasa ta fito cikin wani irin sauti wanda bazaka fahimci komai a cikinsa ba. Mr. Uchenna Franklin right ? A hankali ya gya a mata kai, Hanam ta shiga nazarinsa, tabbas ta gane shi, shine Uche wanda sukayi makaranta tare, wanda giyar yarinta tasa yazo yace yana santa, dan ita a ganinta kawai wannan yarinta ce ba komai ba, duk da ya sauya ya ara girma kammaninsa sun an sauya ka an, amma ta gane shi. Saide kuma ba wannan ne abun da yasa take nazarinsa ba, tana nazarinsa ne sbd muryarsa ta yanzu, kamar ta tab'a jin muryar a wani wuri, saide ta kawar da tunanin. Ok tam da fatan Abba ya yi maka bayani ? Eh ya yi min bayani, yaushe zamu fara dinkin ? Zuwa gobe, yau zan sa a kaika ka zagaya fashion house in kafin ka fara aiki To.... kafin ya fa i wani abun, yaji wani dan karamin hannu ya ri afarsa ta asa, a hankali ya sunkuya ya kalleshi, Damm! wani bangaren na glashi ya fado a zuciyarsa, ganin wani yaro me tsantsar kama da matar dake zaune a gabansa, babu ta yanda za'ayi ka kalli yaron kace ba jininta bane. Yaron kamashi yayi yana jan kafarsa, a hankali ya kai hannu ya auko yaron ya ora akan cinyarsa. Yaron ki ne ? Ya fa i yana masa wasa Eh, yaro nane Shine na farko ko na uku? anyi wani gajeren murmushi, har yanzu Uche bai sauya ba. Shine na biyar Miye sunansa ? Muhammad aryaan, arya Wow what a wonderful name Arya ya kama gemun uchenna yana ja Kai! kai! bari, wannan me tsada ne, hala babanka baya dashi, shi yasa kake tab'a min nawa Ya fa i yana kama dan karami hannunsa. A karo na farko zuciyar Hanam ta motsa akan maganar mahaifin Aryaan, kowa kallon shege yake masa, babu wani wanda ya tab'a magana akan mahaifinsa kamar haka, wata ila shima Uchen dan be sani bane. Yana kallon reaction inta, kuma nan take ya fuskanci cewa akwai matsala game da yaron, kode mahaifinsa ya rasu, ko kuma dai akwai wata a asa. Baaaabaaaaa Daga Hanam har Uchenna kallon Aryaan suke da tsantsar mamaki, Hanam bata tab'aji yayi magana haka ba, saide gwaranci amma baya magana haka, ko Mama bai iya cewa ba amma gashi yana kiran wani Baba, Baba ?. Baba ?, kode ina kama da babanka ne ? Kalisa zata zo ta zaga da kai, thanks for concern Hanam ta fa i dan ta dakatar da bugawar da zuciyarta ke shirin yi, sai Uche yayi murmushi, ya mi e ya zagaya inda take ya bata Aryaan in, sannan ya shafa sumar kansa me taushi. God bless you my boy daga haka kuma fice, Hanam tayi wata iriyar ajiyar zuciya tana dafe kirjinta. Ya'ani inta manak zau'u, bit alla'a ala hada garib wa tu ullu Baba, badal ma tafda'a ma'a ismi ana (Gaskiya kaikam baka da kirki, kawai sai ka kalli mutum ka kirashi Baba, memakon ka fara da kiran sunan). Kamar wani Babba idan yayi abu haka take masa fa a, harda wata harara, sai kuma ya bata dariya ganin yanda yayi lamoo yana kallonta, shima tanayin dariyar ya bangale nasa wawulon bakin, Hanam ta aje shi akan table in kayan aikinta sannan tayi pecking kansa tana shafa sumar kan nasa. Abu ummu inti galiz (Baban mama baka jin magana) A hankali ta rungumeshi. MARYAM POV Bata ankara ba har famfon sink in ya cika robar dake hannunta har yana zuba, saurin kai hannu tayi tana kashe kan famfon, a hankakali ta juya ta kalli kitchen island in, wanda ta cika shi da kayan kitchen in, dan so take ta sauyawa komai ma'aji, amma gaba aya ta kasa, tunani ne fal ranta, tayama zata iyayin wani waran aiki ?. Tatuna abinda yace mata jiya, dan second daya...... biyu....... LA na ukun ne wayarsa dake kan coffee table tayi ringing, kusan tare suka kalli screen in wayar, 'NEHA' shine abinda aka rubuta, a gaban sunan kuma akwai heart emoji, gaban Maryam yaci gaba da buga a lokacin, wayar ya auka ya mi e, har ya kai kan stairs sai ya juyo ya kalleta a inda ya barta. An kawo kayan abinci, suna kitchen kije ki duba ki gani, idan akwai abinda babu sai ki fa amin Cikin karfin hali Maryam ta gya a masa kai. Tana jin ya ja kofar akinsa itama ta mi e harda gudu ta shiga kitchen ta auki abuncin ta data dafa na dare, ta koma aki ta kulle. Sai kuma ta tsun duma duniyar tunanin caku un zatukansa, wanda babu abu aya data tsinta a ciki, gaba aya zantukan nasa sun aure mata kai, wai me yake nufi da shi annoba ne ?, me yasa zai kira kansa da monster?, kuma beast?, dama mutum yakan zama dodo ?, kode yayi hakan ne dan ta nisance shi ?, to amma Fulani ta fa a mata makamancin hakan. Kode dan yana so ya auro wannan Neha in ne yasa yace mata haka ?, kai bama haka bane, koma de miye shi yasani, amma kuma a can asan zuciyarta a tsorace take, dan Maryam gwanar tsoroce, saide tunanin zata koma makaranta, dana kayan abincin daya ara cika store in da shi sai ya kore wannan tunanin, tunda de har yace ta nisance shi, kuma yace ta ri a kulle kofa ai shikenan. Amma kuma duk da haka abincin data auka bata samu ta ci ba, bacci ma da yar tayi, daga ta anji motsi zata farka, da haka har gari ya waye, kuma taji sanda ya fita masallaci, sai a lokacin ta sau o kasa ta mayar da abincin kitchen Sannan ta shiga store in aje kayan amfani na gidan, ta auko broom da squeegee da mop ta koma saman, ta share ko ina a akinta ta goge, ta wanke toilet ma, haka balcony, ta bu e curtains in tana kallon yanda hasken rana ke baza duniya. Ga tsirarin mutane na kai kawo, sannan ta dawo cikin akin, kuma bata fita ba saida taji ya dawo daga masallaci, sannan ta fito, ta share corridor in nan tayi moping sannan ta saka squeegee in nan ta goge glass in balcony A wajen taga abincin akun nan ta zuba mata harda ruwa, sannan ta auko watering can, tayiwa flowers in dake wajen bayi, kana ta sau asa, parlon ma ta gyarashi sosai harda wajen daning, dama store da ironing room, sannan ta shiga kitchen, kuma shi har yanzu bata gyara shi ba sbd so take sai ta gama shirya kayan cikinsa kafin ta gyara shi. Da wannan tunanin ta araso island in, ta auko wasu gajerun kwalabe na glass wanda tasan cewa na species ne, ta ri a juye kayan species in har saida ta gama, sannan ta janyo wata cabinet guda haka ta jerusu. Sai kuma ta dawo kan glass cups da smoothie jars da kuma mugs, suma ta jeresu a loka guda, tanayin aikin zuciyarta na washewa da farin ciki, plate da bowls ma nasu wajen da ban, sai kaysn stainless steel cooking utensil set, ta aje su kusa da stove, oil containers din data zuba mai a cikima ta aje su kusa da set din. Knife set ma a wajen ta aje shi, sai frying pan, work, set in tukunya duka ta aje su a waje guda cikin wata cabinet, blender, greater da juicers suma tai musu ma'aji, kayan shayima su bournvita da su lipton ta sauya musu mazubi zuwa wasu containers na glass. Sai da ta tabbatar da komai a killace yake sannan ta shiga share kitchen in, kayan fridge in ta barsu