← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 84

Sashe 24

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sana Hanam sun tab'a yin aji aya a secondary. A'a haris, bata tab'a aure ba Uche yayi wata b'oyayyar ajiyar zuciya, amma duk da haka saida Abba ya ji, Abba yayi murmushi Haris Na'am Abba Next week zanje haku au, kuma tare nake so muje Haku au shine mahaifar Alhaji Muhammad. Zuwa lokacin na gama aiki a nan, ba matsala zamu iya zuwa Eh nasan zuwa lokacin ka gamawa Hanam aikinta, kawai na fa a maka ne dan ka shirya To Abbana, Allah ya kaimu Ameen an albarka na Kuma daga haka wayar ta are, Uche ya aje mug in hannunsa akan wani table, sannan ya dawo ya auki measuring tape, ya shiga auna wani yadi, zuciyarsa fal tunane-tunane iri-iri. Kuka yaji, kuma yasan cewa babu me kukan bayan Arya, dan akin da ake renonsa kusa da office in sa ne, Allah ya sani tun daga ranar da yaron ya ri afarsa ya shiga ransa, dan haka da sauri ya aje yadin da measuring tape in duka ya fice da sauri ya fa akin. Ya iske Naani in nasa ta na rarrashinsa shi kuma sai kuka yake, gaba aya ya rikita Naani in nasa. Kinga kawo shi Ya fa i yana mi a mata hannu, mi a masa shi tayi, shi kuma ya karb'eshi ya fice daga akin. Office in nasa ya koma da shi, ya shiga rarrashinsa, amma ya i shiru, sai kawai Uche ya auki wani zanin atamfa daya yanka ya goyeshi, yana jijjiga shi. Tunda Aryaan yazo duniya ba'a tab'a masa goyo irin wannan ba, dan Hanam bata goyonsa saide ta sakashi a baby carrier, nan da nan yayi bacci. Hanam taji kukan Arya hakan yasa itama ta fito domin taga abinda yake faruwa, sai Naani in ta fa a mata cewar ai wannan na ayan office in yazo ya karb'eshi, dan haka Hanam ta fita, ta shiga office in Uche. Samunsa tayi yana kai kawo da Aryaan in a bayansa, kuma gashi ya goye shi, wani abu ya motsa a kirjinta, wanda rabonsa da ya motsa tun shekaru biyu baya, sai ta kawar da tunanin, dan a ganinta abun ba meyiwuwa bane, ita sai abun ma yaso ya bata dariya, namiji da goyo, kuma ya iya goyon ko dan igbo ne oho. Yanzu Uche da atamfar dubbunan ku in ka goyi yaro ? Ta fa i tana shigowa ciki, shi sam ma bai kalleta ba. Me zai hana idan de boy ze yi shiru, idan yana kuka bazan iya aiki cikin kwanciyar hankali ba Hanam taji wanna abun yaci gaba da motsawa, kuma wannan irin wanda tavjine lokacin da ta haifi Arya Naga ya yi bacci kawo shi, kar ya hanaka aiki Ba dole yayi bacci ba, yaji goyo, nasan yanzu haka ba goyonsa kike ba Ya fa i yana arin since zanin goyon. Na miye zan wani zo ina goyonsa, ai baby carrier in shine dai-dai shi Ta fa i a lokacin da ya mi a mata shi, daga haka kuma ta fice daga wajen, Uchenna yabisu da kallo su duka, yana murmushi ya dawo yaci gaba da aikinsa. *ALARO CITY, BLOCK 3, HOUSE NO 122* *Da misalin karfe 06:00pm* Maryam ce tsaye a cikin kitchen in gidan, meat pie take ha awa, dan yau da safe Tafida ya fa a mata cewar an gama komai na makarantar ta dan haka gobe za suje tare a arasa sauran abubuwan. Yanayin murnar da take ciki sam bame kwatantuwa bane, lokacin da aka aura musu aure kowa fa i yake cewa tayi sa'a duk bataga sa'ar da tayi ba sai yanzu, a yanda ta fahimta shima sam baisan da auren ba, amma kuma haka ya ha ura ya karb'i auren nasu hannu biyu. Kuma babu abunda ya rageta da shi, komai yana mata, bata da wani abunyi sai godewa Allah da kuma shi Tafidan, data fusakanci baya san tana gode masa sai ta samo wata hanya ta gode masa da ban, Ta lura da yanada san cin abinci, kuma yana san abincin da take girkawa dan haka sai ta ke gode masa ta hanyar abinci. Kullum da safe sai ta tsantsara masa girki na gani na fa a, da yamma ma haka, dama na rana baya ci a gidan, duk girkin da take dashi a wayarta shi take masa, kuma dama ita gwanace wajen girki, kuma ta lura da yana jin da in girkin nata. Sbd zata fara zuwa makaranta yasa yau ta yanke shawarar musi meat pie da cake, sbd koda zata makara da safe wata rana, Sai su samu su rage hanya. Kuma shekaran jiya yace mata taje su gaisa da matar ma ocinsu, kuma taje in dan harma ta an jima a gidan dan matar tana da kirki, duk da ta girme mata a shekaru, dan zata iya fin Anti Fati ma. So take tayi ta gama soya meat pie in kafin magariba tayi, dan cake kam tuni ta riga ta gama shi, shima meat pie in ka an ne ya rage. Kuma kafin magaribar ta gama soya shi tas, ta juye a wasu containers masu kyau, ta zuba cake biyar meat pie shida a wani aramin kwano me murfi, wanda zata mi awa Maman Ilham, kamar yanda matar tace mata shine sunan arya ta farko. Ta zuba gaba aya kayan data b'ata a dish washer, dan bata wani wanke-wanke, komai cikin sau i take yinsa, ta goge duk inda ta b'ata, sannan ta ebi warmers in data zuba abincin data girki, ta fita daga kitchen Ta jerewa Tafida nasa akan danning table, sannan tayi sama. Sallar magariba ta gabatar, sannan ta ara sau owa asa ta auki wayarta dake chargy a parlo, ta auki wannan kwanon data zubawa Maman Ilham meat pie in, ta janyo ofar parlon ta fito compound in gidan. Sai da ta kalli parking lot in gidan, motocin Tafida ne guda biyu kawai, dan ya fita da guda aya, ta bu aramar ofar gare in ta fito. Bata damu da ta kulle gidan ba, dan a ganinta babu wanda zai iya shiga gidan bare har yayi sata, ta tsaya tana kallon kyakyawar unguwar tasu, yanda take da kyau da daddare, bata tab'a fitowa da daddare ba sai yau, dan last time data fito har ta shiga gidan Maman Ilham in da rana ne, kuma shine fitarta na farko, sai kuma yau a gaba aya zamanta a unguwar wurin kwana shida, saide ta ganta ta saman balcony. A hankali ta shiga takawa har zuwa ofar gidan dake jikin nasu, wanda yake shima sak nasun yake, ita ranar data shiga gidan ma tayi zaton zata ga komai na ciki irin nasu ne, amma sai taga hatta da ginin cikinma irin nasun ne amma banda kayan cikin. Kanta tsaye ta tura aramar ofar ta shiga, dan ta lura da gaba aya gidajen unguwar basubda masu gadi. Sai da ta wasa ofar parlon gidan, sannan aka bu e, Ilham in ce ta bu e mata ana gaisheta, itama Maryam in ta amsa mata da fara'a Ilham waye ne ? Muryar Maman Ilham in ta tambaya daga cikin parlon, Ilham in ta bu e kofar gaba aya tana fa Anti Maryam ce To ta shigo mana, sai ta tsaya a waje? Maryam ta shigo tana murmushi, Maman Ilham ince a parlon ita da sauran yaran nata biyu, aliyu da abdul, ta zauna a sanda suma suke gaishe ta, sannan suka gaisa da Maman Ilham Maman Ilham meat pie ne nayi, shine nace bari na kawo miki a bawa yara A'a to an gode Maman Ilham ta fa i tana karb'ar bowl Gobe zan fara zuwa makaranta Tanan ALARO zaki fara zuwa ? Maryam ta amsata kanta a asa kamar yanda ta saba. To Allah ya temaka, Allah ya bada sa'a Maryam Ameen, ni zan koma Take mi Har zaki koma? Eh magariba ta yi, nasan ya kusa dawowa Hakane kam, Ilham tashi ki rife mana ofar arashe tana kallon ilham in, lokacin Maryam har ta kai bakin ofa. Tun daga fitar ta daga gidan su Ilham in ta hangi motar Tafida sai kawai ta tsaya a ofar gidan har ya araso, ya bu e gate in da wayarsa sanna ya shiga da motar. Amma bai kulle gate in ba dan ya ganta shima, fitowa yayi daga motar ya dawo ofar gidan inda take, Kuma tun kafin ya arasa inda take ya fara sabbaben nasa, wato sauraren bugun zuciyarta, wani abu da ya zame masa farilla a kwanakin nan, abun na mugun bashi mamaki, dan yanxu abun ya zame maza jiki. Idan baya gidan har Allah-Allah yake ya dawo, dan yazo yaci dadda an girkinta, ga kuma dadda an sautin bugun zuciyarta, wanda yake saka masa nutsuwa a koda yaushe, a da daga asibiti sai gida sai kuma filin wasan cricket, bashi da wani abu na nishadi bayan cricket Amma yanzu an samu sauyi, zuwan Maryam rayuwarsa ya sauya abubuwa da dama, ya koma wani Tafidan da ban da na da, yanzu ya koyi yawan cin abinci, sab'anin da, da ba sosai ya cika cin abincin ba, sbd shi bai cika san cin abincin waje ba, yafi so ya girka da kansa, wani lokacin a makare yake tashi baya samun damar yin girkin. Da yamma kuma ya dawo a gajiye wataran saide yaci bread kawai ya sha ruwa, amma yanzu a kullum so yake tace masa ga abinci, dan ya samu yaci dadda an girkinta, shi yana mamakin yanda kanta yake a waye, ga yanda ta iya girki, har tunani yake ma wata ila tayi makarantar koyon girki ne. Ga kuma yawan sauraren wa a da yake a da, amma banda yanzu, sam sauraren wa arma baya gabansa, wannan bugun zuciyar tata, shine ya zame masa kamar wa ar, wani lokacin sai ya raba dare yana saurarensa, koda tana akinta yana iya jiyoshi. Saide idan tana asa ne, amma middin tana aki to zaiji yanda zuciyarta ke bugawa, kuma har yanzu idan yana tsaye a gabanta zuciyarta na bugawa cikin tsoro. Sai kuma wani abu dake faruwa da shi, rabon da ba in ruhinsa ya tashi tun yana ha ejia, kuma hakan ya bashi mamaki, duk da a wasu lokutan idonsa na sauya kala, duk da a da can ba in ruhin baya tashi sai idan
Chapter 24 · 0% Book details