Sashe 64
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsaya yana kallonta, zaune take a kan darduma, bayanta jingine da jikin gado, idonta a lumshe, kamar me jin bacci, yanda muryarta ta ke fita cikin karatun ka ai zai nuna maka cewar bacci take ji. Duk da yana cikin wani hali na azaba, amma sai da tausayinta ya kama shi, baiwar Allah yanzu haka bata samu bacci ba. Yaci gaba da takawa zuwa cikin akin, amma hannunsa ri e a kansa. Dif!, ya ji karatun nata ya tsaya, numfashinta ya yi nauyi, alamun dai bacci ta fara. A lokacin kuma wannan bajin haya in da ke cikin kwalba ya dena motsi, kwalbar ma ta dena jijjiga. Tsayawar karatun nata ya tsaya tar e da sarawar da kansa ke yi. A hankali ya zauna a kusa da ita, kuma har lokacin bata farka ba, kanta ya kama tare da orashi a kan kirjinsa, ya rungumeta a jikinsa tsam. Cikin bacci Maryam ta ji kamshinsa a hancinta, sai kuma ta ji kamar an ri eta, hakan yasa a wahalce ta bu e idonta, ai ko ta yi kyakyawan gani, dan ur suka ha a ido da shi, da wayar idonsa wadda take ja. Maryam ta razana zata fice daga jikinsa, amma ya i ya saketa. Ki yi baccin ki kawai A... abinci zanje na yi, yau ak...akwai aiki... Ki kwanta nace ko ? Maryam ta yi shiru, amma kuma baccin ya gudu da ga idonta, kuma bata jin zai dawo, dan bazata iya bacci a haka ba, a cikin hannayensa ?, cab i jam!!. UCHENNA POV. Yana dawowa gidan ya shiga neman Hanam, akinta ya fara zuwa bai ganta ba, dan haka ya shiga akin Arya, yasan cewa baza ta wuce nan ba. Tsaye ya sameta a jikin baby cradle in Arya, ta bashi baya, be san me take ba. Da alama ma bata san cewa ya dawo ba, zuciyarta ta cilla cikin kogi tunanin, ji take kamar za'a rabata da Aryaan ne. Bata ankara ba ta ji an kewaye ugunta ta baya, saida ta an ja iska a ma ogwaronta sannan ta gane cewa shi ne. Nagode Hanam, ban tab'a tunanin cewa mafarkin da nake zai zama gaskiya ba, ban tab'a tunanin cewa zan shiga studio na yi wa a ba, a koda yaushe mafarkina a nesa nake hangoshi, can nesa sosai, amma sanadiyyar ki, yau ya zo kusa, na ganshi a kusa Hanam ta yi ajiyar zuciya, Tun bayan rasuwar Abba ta yanke cewa za ta yi magana da Fala , a kan fara wa ar Haris in, yana san wa a, kuma yana da talent in wa ar. Kuma tasan cewa tun da yanzu ba Abba aikin a ashin Kamal ba ze iyu ba. A hankali ta juyo ta kalle shi, ba tare da ta ce masa komai ba. Ta shiga arin fita daga hannunsa, amma ya i ya saketa. Waye Gabriel ? Tambayar ta doka wani abu me sauti kamar ganga a kan Hanam, duk da tasan cewa zai bu aci sanin hakan, yana bu atar sanin waye Gabriel!!. *Room 330, Presbyterian hospital, New york* Hanam ce kwance a kan gadon marasa lafiya, gefen fuskarta rufe da bandage, yayinda idanuwanta suka kumbura har bata iya bu e su da kyau, a hankali siriryar walla ke zubowa ta gefen idonta. A jiya kawai rayuwarta ta yi wani irin sauyi, sauyin da ba zai tab'a gogewa ba, a jiyan kawai Gabriel ya ana mata azabar da tun da uwarta ta kawota duniya bata tab'a shan makamanciyar ta ba, a jiya Gebriel ya haike mata, ya haike mata cikin rashin imani da rashin tausayi. Ta yi zaton cewa bayan rashin uwa da ta yi shikenan wahalarta ta yanke, ashe ba haka ba ne, ashe akwai wata wahala da azaba dake jiranta a gaba. Ta tabbatar da yanzu rayuwarta ta gama wargajewa, babu na mijin da zai iya aurenta a haka, kimarta ta gama zubewa a idon kowa. ofar akince ta bu e, ma ociyarta Banedita ta shigo, wadda itace ta temaketa ta kawota a aibitin a jiya. Kuma itace ta sanar da 'yan sanda, hannuta ri e da leda ta shigo cikin akin. Cike da tausayawa take kallon Hanam, dan likitan da ya karb'eta jiya yace ba aramin azaba aka bata ba, ta wahala sosai. Sannu kinji, sunce zaki iya cin wani abu tashi na baki Hanam ta kawar da kanta gefe, alamun bata so, kuma itama Beneditan ta fa a ne kawai, dan tasan wannan abun akwai ciwo ga 'ya mace, bayan haka kuma ita harda raunika a jikinta. Haka Hanam ta yi jinya kusan sati uku a asibitin, amma bata fa awa Abba ba, kuma yansanda sunyi bincike a kan bayanan da ta basu sunce basu samo wanda ta fa a ba. Kuma itama sai ta share komai ta karb'i sauyin da rayuwa ta zo mata da shi, inde har Allah zai ci gaba da ora mata addararo kala-kala ta shirya karb'ar su, kuma tana fatan Allah yasa ta iya jurewa. Kuma bayan sati ukun ne ta koma aikinta, saide ta rage abubuwa da yawa, ta dena kwalliya, ta dena yawan fara'a da surutu, duk da dama can ba wani sosai take hakan ba, amma na yanzu ya ragu sosai. Kullum idan ka ganta kamar mara kafiya. Bayan wata biyu ta soma jinya, tana laulayi irin na masu ciki, kuma tun kafin ta je asibiti Benedita ta fa a mata cewar tana da juna biyu. Abun ba aramin aga mata hankali ya yi ba, amma haka ta je asibiti aka gwadata, sannan aka sanar mata da tabbacin shigar ciki a jikinta. A ranar ta yi kuka kamar ranta zai fita, amma koda wasa bata ji san ta cire abinda ke cikin ta ba, ta auke shi a matsayin aya da ga cikin addarorinta na duniya, kuma tasan a ranta cewar Allah zai bata Ikon cinyewa. Haka ta yi ta renon cikin dake jikinta, kuma ko da second aya, bata tab'a jin sansa cikin ragu a cikin zuciyarta ba. Ita da Benedita suke kula da cikin. Ga kuma su Camilla suma da suke tausaya mata, duk da cikin dake jikinta baya hanata zuwa aiki. Dan Hanam bata ha a aiki da komai. Haka kuma duk wannan bada alar cikin da take bata tab'a fa awa Abba komai a kan cikin ba. Ana haka har ranar haihuwarta tazo, kuma daga ita sai Benedita da Camilla ne kwai a asibitin. Sannan ko a wurin haihuwar taci ba ar azaba, dan har an afara shirin mata tiyata, Allah ya temaketa ta haifo yaron, kuma cikin oshin lafiya. Amma taci azaba sosai. Dan sai da likitan da ya karb'i haihuwar ya sanar musu da cewa ba lalle ta sake samun wani cikin ba, sbd mahaifarta da ta samu matsala. Tun da ta ora idonta a kan yaron, ta ji duk duniya bata da abun so da ya wuce Abba da shi, ta ji bayan Abba wani ya samu matsugunni a zuciyarta. A da bata da wani wanda take so sama da Abba, amma a yanzu, ta samu wani, wani wanda ta ji har ahon zuciyarta zata iya komai dominsa. Kuma wani abun mamaki sai yaron ya iyo kamarta gaba aya, abu biyu ya rabata da shi, farin fatar da ya fita da kuma shu ayen idanuwan da yake dasu. Ita da Benedita suka ci gaba da kula da jararin da ta ra awa Muhammad Aryaan, Har zuwa lokacin da aikinta ya are a The House of Sofia couture . Ta tattara komai ta koma Nigeria, babu abinda ta yi kewa a USA sai Benedita da Camilla, dan sune wa anda suka rakota har zuwa airport, Benedita har da wallarta. alubale na farko da Hanam ta fara samu bayan ta dawo gida shi ne, 'yan gidansu da suka kira Aryaan da shege. Dama can ba shiri suke da ita ba, kullum cikin fa a suke, duk da bata kula kowa a cikin su. Amma a ranar sai da akayi fito na fito ita da su, ta shafawa idonta toka ta tsigesu tas, ha i da kakkauran warning a kan kada su ara kiran anta da shege. Abba kansa abun ya aure masa kai, yana san ya san wannan wani yaro ne 'yarsa ke auke da shi tana kirarin itace uwarsa da ubansa, bayan yasan ba ta yi aure ba, kuma bata fa a masa za ta yi aure ba. Duk da yana waya sosai da ita sanda tana USA in, amma bata tab'a masa wani batu a kan wani yaro ba. Dan haka tana da sati aya da dawo nigeria ya kirata babban parlonsa. Bannute waye wannan yaron ? Hanam ta sunkuya ta kalli kyakyawan jaririn da take ganin fuskarta a kan tasa, sannan ta ago ta kalli Abba. ana ne Abba Abba ya girgiza kansa. Maman babanta ni ban miki Aure ba, kuma nasan ba ki yi aure ba, yaya aka yi ki ka samu yaro ? Cikin murmushi ta tsara masa komai, ta fa a masa duk abinda ya faru, kamar labarin baya ona mata rai, kamar ba a kanta abun ya faru ba, kuma kamar wadda ta zauce. Shi kansa Abba sai da yabyi kuka, dan shi yasan irin halin da take ciki a yanzu ma, amma kuma ga wata addarar Allah ya ara oro mata. Abba ka dena kuka, nahan ma'anna kayal, yalli sha'atulul adar huwa yalli rah yisir (Bamu da zabi Abba, YADDA ADDARA TA SO haka zata kansace An wuce lokacin da zata zauna ta yi kuka, a baya ne ta sha kulle kanta a aki ta risgi kukan rashin uwa, a baya ne ta sha zubar da hawaye a kan abinda 'yan uwanta suke mata. Amma yanzu komai ya sauya, an wuce wannan lokacin da zata zauna tana kuka kamar aramar yarinya, yanzu ta girma, ita uwace, wadda take jin zata iya kula da nauyin anta da Allah ya bata, ji take zata iya kareshi daga duk wani abun i, ji take zata iya sadaukar da komai nata domin ya samu farin ciki. Dan haka zata ta sadaukar da lokacin ta, ta sadaukar da auren da take shirin yi, ta sadaukar da duk abin da tasan zata iya duka domin Aryaan, ba zata gudu ta bar shi ba, domin ita uwa ce. Abba ya mi o mata